Sashe 9
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda ya kwantar da ita a gaɓar ruwan har gari ya waye ta kwana a wajan, wani daren ya yi ta sake kwana, kwana biyu kenan amma bata motsa ba. Bata kuma da ranar tashi sai lokacin da Ubangiji ya nufa ko kuma ya tsara. A can cikin barci ta fara mafarki gata da namiji suna kasancewa waje guda, wani abu mai kama dana auratayya na gilmawa a tsakaninsu. Numfashi ta sauke tana motsa ƙafafuwanta zuwa cinyoyinta da suke mata zafi, tana jin kamar an daddaneta a firgice ta farka tana kurma ihu tare da kiran sunan Dada, ba addu'a babu komai. Cikin tsoro ta fara bin jikinta da kallo babu komai lafiyarta ƙalau domin ba wani sauyi da taji. Ajjiyar zuciya ta sauke a bayyane tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka, kenan haka rayuwarta zata ƙare cikin dokar dajin ko yaya ne? ya akai ta tsinci kanta a dajin gaba ɗaya ta rasa amsar tambayoyin zuciyarta. A hankali ta fara jin dariya na karaɗe wajan, tare da surutu ƙasa ƙasa. Miƙewa ta yi da sauri ta shiga duba inda take jiyo sautin dryar a haka ta ƙaraso jikin wata ƙatuwar bishiya, cike da tsoro da kuma tarin zullumi ta ɗaga kansa zuwa saman bishiyar idanunta ya sauka akan wani ganyen bishiya dake lilo shi ɗaya, sai ka ɗauka iska ke kaɗa shi amma abin mamaki shi kaɗai ne yake lilo daga cikin sauran ganyen bishiyar. Prince Bill wanda a yanzu ya rikiɗe zuwa suffarsa ta asalin aljani yana kwance saman ganyen yana karkaɗa ƙafarsa wacce ita ce take sanya ganyen bishiyar motsawa, Danejo dai kallon ganyen take cike da mamaki tana tsaye taci mangoro ya faɗo kanta abinka da mai jin yunwa da sauri ta ɗauki mangoron babu Bisimillah ta shiga sha idanunta na lumshewa sbd daɗi. Daga bayanta taci ance. "Kisha a hankali da wasu da yawa idan kina buƙata" juyawa tai da sauri baki buɗe take kallon mai maganar, iya tsoro da razani ta shiga domin bata taɓa ganin halitta irin wannan ba, mangoron ta saka tare fasa wani Ihu ta ɗaga ƙafa zata gudu yai saurin riƙe hannunta.
Share🥰🥰🥰
*🌈IDAN BA KE 🌈*
6....
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
"Na shiga uku Aljani Balarabe" Danejo ta faɗa a ruɗe tana ƙoƙarin kwace Hannunta daya riƙe cikin nasa. A nutse Prince ya ware idanunsa sosai a kanta yana Mmkin Yadda duk ta ruɗe kamar taga mugun abu. "Me ya baki tsoro" murguɗa masa baki tai tana suɗe hannunta dake ɗauke da ruwan mangoron ba tare data ce komai ba. Prince ya saki tattausan murmushi mai kyau da tsari yana binta da kallo musamman idan ya tuna abubuwa da suke faruwa a tsakaninsu, sai yaji nutsuwa ta kamasa. Hannunsu ta make ta ce "Sakeni haka kurum kai mini ciki, bayan Dada ta ce ba kyau namiji ya taɓa mace" ta ƙare Maganar tana binsa da kallo, sai a lokacin da a shiga ƙarewa tsarin hallitar jikinsa da kallo, fari ne tas kamar ka taɓa shi jine ya fito, yana da faɗin ƙirji fuskarsa mai cike da ilhama, ga wani gudun saje wanda ya kewaye fuskarsa zuwa ƙasa wajan gemunsa, fuskarsa mai faɗi ce babu wani abu da zai bamban tasa da jinsin larabawa. Prince ya saketa yana mai faɗin "Ciki na nawa kuma?" Zuciyarta na bugawa sosai ta ce "Me kace?" Ya girgiza mata kai yana ware hannun shi ya ce "Babu komai Danejo" zare ido tai tana dafe ƙirji sosai a tsorace ta ce "Kasan sunana? don Allah kasan rugarmu wallahi ɓata nayi ka taimaka kaji ɗan Balarabe" idanunsa ya ɗaga sama tare da daidaita juyawar launin idanunsa ganin yana neman rikiɗe masa, jikinta duk rawa yake tai saurin cakumarsa tare da rirriƙesa wanda yai sanadiyar fitowar wata jela a bayansa, sbd ko yaya ya samu kusanci da ita, baya iya zama a zallar mutum, dole sai wani sashi na jikinsa ya juye zuwa na aljani. "Ukkkkk heee" ya faɗa cikin kumburarriyar wacce ta amsa kuuwa cikin kunan Danejo. Gaba ɗaya rikicewa tai ganin yadda take neman maƙalesa baki ɗaya saboda tsoro da fargaba har take shirin bayyanar da kofatonsa yasa yai saurin riƙo Fuskarta tare da hura mata iska a fuska. Ƙuri tai masa da idanu a rarrabe ta shiga faɗin "Ka kaini wajan Dadata kaji, bana son zama a nan tsoro na keji Da...da...ta.." ta kasa ƙarasa maganar sbd idanunta da suka ruf wani barci mai nauyi ya ɗauketa.
Fuskarta yabi da ido yana hango lokacin da yake tare da mahaifiyarta, duk yadda ya nunawa Dada so da ƙauna amma haka wani mugun babban Malami ya raba shi da ita, ba shi da niyyar cutar da Dada kawai ƙauna ce tasa yake tare da ita, yai ihun tare da magiya amma haka Malamin ya fatatakesa daga cikin Dada bayan ya ƙona shi. Wannan dalilin ya sa yai jinya sosai har bai san inda Dada tai ba sai kwatsam ya ganta lokacin tana ɗauke da cikin Danejo, tun daga wannan lokacin ya ɗauki son duniya ya ɗora akan Danejo, ya manta da batun Dada ɗan tayin dake cikinta kawai yake muradin yaga ya zo duniya.
Sauke numfashi yai yana binta da idanunsa daya gama rikiɗewa har wani hayaƙi yake fiddawa, hannunta ya riƙo ya kama yatsan dake ɗauke da zoben daya saka mata ya jima yana kallonta kafin ya saketa zuwa ƙasa ya kwantar. Tsakiyar dajin ya koma yana Girgiza da surutai cikin ƙaramin lokacin ya koma asalin suffarsa ta aljani yana wani ihu da gurnani kafin kace wani abu ya gama haukata dajin can kuma ya ɓace ɓat.
Yamma Yabi ne da Shatu tare da Sarkin ruga da kuma Giɗaɗo kwance a gaban Dada wacce take cikin halin rayuwa ko mutuwa, bata san inda kanta yake ba, sunan Halisa Dajeno Rome ne kawai a bakinta. Giɗaɗo ya ce "A jiƙa wannan maganin a bata" da sauri Hamma Yabi ya amsa tare da jiƙawa da taimakon Shatu ya ɗaga Dada suka ɗora mata maganin, wani shaƙuwa tai jikinta ya shiga jijjiga can kuma ta kwanta shakaf barci ya ɗauketa. "Na shiga uku na lalashe Hamma Dada ta mutu wayyo yanzu yaya za mu yi Dada ki tashi" idanun Hamma Yabi na taruwa da ruwan hawaye ya kama Shatu tare da riƙeta ya ce "Assha Assha Shatu Dada nada rai, daina kuka yaro barci Dada tai" kuka kawai Shatu take, duk da ƙarancin shekarunta amma ta fahimci cewa Dada ita ce cikon farin cikin su, tare da jin daɗinsu. Sarkin ruga ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Allah shi bata lafiya, Aradu tana gab da mutuwa" jin kalmar Sarkin ruga yasa Shatu ƙara sakin kuka tana jijjiga Dada tare da faɗin ta tashi kada ta mutu ta barsu cikin ƙuncin rayuwa. Cike da takaicin kalamar Sarkin ruga Hamma Yabi ya bisa da kallo yana addu'ar Ubangiji shi ya ɗauki rayuwarsa yabar Dada a duniya ko dan farin cikin Shatu da Halisa. "Ba a samu labarin Danejo ba har yanzu?" Girgiza kai Hamma Yabi yai yace "Aradu ta ɓace babu ita kaf cikin ruga da kuma daji" cikin tausayawa Giɗaɗo ya ce "Wayyo Allah shi baiyyanata" "Kawai iskanci ta tafi, amma ina ne Danejo bata sani ba cikin ruga da dajin ba har kiwo take zuwa ba?" Da sauri Hamma Yabi ya ce "Danejo ba zatai iskanci ba, domin bata san shi ba" fita duk sukai daga cikin bukkar. Hamma Yabi ya dubi Shatu da barci ya ɗauketa a jikinsa a hankali ya kwantar da ita, tare da fita daga cikin bukkar. Yana fita ya shiga irga Nagge wanda ya zama al'adarsa kullum tunaninsa za a iya sace musu Nagge shi ya sa a rana sai ya irgasu sau biyar. Kai tsaye asibiti ya nufa lokacin ana zubawa Dr Iliya magani a cikin mota.
Saukar ruwan ruwan sama ne ya haddasa farkawar ta daga barci, da sauri ta miƙe tsaye jirkinta na rawar ɗari sbd gaba ruwan ya gama yi mata doka, ganin bata da wata mafita ya sa ta fara ƙoƙarin ɗaga ƙafarta Innalillahi sai a lokacin ta lura ashe a kan wani ƙaton dutse mai tsayin gaske take, ita kanta bata iya hango ƙasan dutsen, a hankali ta koma tare da zama saman dutsen "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wacce kalar rayuwa ce take ciki haka? kenan akan dutsen ta kwana? ina ne nan kuma kwananta nawa? ta haukace ne ko mene? Anya ita ce ba wata Danejon bace daman?" Wani raunataccen kuka ta saka kuka take da dukkan ƙarfinta kenan ita da Rugarsu har abada ina za taga Dadarta? Kuka take sosai na rashin mafita ga rayuwarta ga ruwan sama na dukanta, yunwa take ji sosai, hannunta ta tara ruwa ya shiga sauka a hannun cikin sauri ta shiga shan ruwa sai daya isheta sosai sannan ta koma ta kwanta barci ya ƙara ɗauketa saman dutsen.