← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 55

Sashe 40

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da fararen idanunsa masu tsari yake bin ta da idanu da mamaki, ganin da gaske bata mutsi tsoran da ya yi mata yawa ya sanya numfashinta ya ɗauke, hannunsa basu taushi ya sanya akan fuskarta kamar mai jin tsoran gently ya shiga bubbuga kumatunta amma ko motsi ba tayi ba, ya ɓata fuska ganin tun ba a je ko'ina ba, yarinyar zata fara bashi wahala.
Yatsun hannunta biyu ya kama yaja da ƙarfi yana buga tsakiyar kanta ajjiyar zuciya ta sauke da ƙarfi tana jan numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana riƙe wanda taji kusa da ita sosai cikin fillatanci take faɗin.
"Don Allah ku sakko dani ƙasa zan mutu wayyo Dada wajanki zan dawo" saukar numfashin da yaji yana sauka a fuskarta da ƙamshin da ba zata manta da shi ba ya sanya ta buɗe idanunta wanda ta rufe su saboda tsoro, wanda ta gani take jikinsa ya bata mamaki numfashinta ya kusan ɗaukewa, sbd yadda ya yi mata kwarjini a idanu ga Alkyabbar jikinsa duk ta rufe mata jiki, a jikinsa yaji shi take kallo bai kalleta ba, ya sanya hannu tare da riƙo kafaɗunta da kyau yana zaunar da ita akan kujerar sosai.
Yana daga inda yake ya ranƙwafa sosai tare da miƙa hannu zuwa inda blet ɗin take, kwantaccen sajansa ya shafi fuskarta ta sauke numfashi mai zafi wanda ya sanya Yaa Sheikh daka tawa da kama blet ya jima kafin ya zaro blet ɗin da sauri ya maƙala mata, yana ƙoƙarin janye jikinsa ta ɗora hannunta a tsakiyar tafin hannun shi..
"Uhmmm" ya ce a ransa yana ɗaga idanunsa zuwa gareta ya kalli cikin idanunta ba tare da ya ce komai ba, Halisa ta sake damƙe hannunsa da kyau cikin rawar murya ta ce. "Usako miyetti masin" idanu kawai ya lumshe mata tare da matsawa waje guda.
A fusace Zahrah ta kunce blet É—in jikinta tare da tashi tayi kan Halisa tana kumfar baki ta ce.
"Ke dan uwarki mijina sa'anki ne da har zaki faɗa kansa da ƙazamin jikinki? Shegiya mara ƴan ci" Halisa ta kalli Zahrah ta ce "To Anti godiya nayi masa fa, kuma dana faɗa ƙasa naji ciwi ba ƙwara na faɗa kan shi ba, kuma ai ban masa nauyi ba ko kaji ciwo?" Ta faɗa tana juyawa tare da kallon Yaa Sheikh, shi gaba ɗaya hankalinsa baya kansu hannunsa riƙe da darija yana dubawa, tuni ya mayar da hiramin kansa baya buƙatar kowa yaga wani sashe na jikinsa.
"Kauuu!!" Zahrah ta ɗauke Halisa da mari tare da nuna ta hannu ta ce "zanci uwar data haifi babarki" ƙarfi da girman zagin yasa Yaa Sheikh kallon Zahrah a zuciyarsa yana Istigifari bai ɗauka wani zai iya zagin ba, ba a taɓa zagi a gaban shi ba, hakan ya zama abu sabo a gare shi. Bai ce komai ya ɗauke kai tare daci gaba da duba jaridar hannunsa, zafin marin yasa Halisa fashewa da kuka sosai tana kifa kanta a cinyarta, kuka take sosai wanda rabin kukan baƙin cikin zagin da Zahrah tayi mata ne. Yaa Sheikh kukan yake ji har tsakiyar kansa jin kukan na neman tarwatsa masa kai yasa ya miƙe tsaye tare da buɗe wata ƙofa ya shiga.
Zahrah ta kasa haÉ—iye mamakin yadda Yaa Sheikh ya nuna kulawa ga Halisa, haushin abin da ya yi yasa ta huce akan Halisa É—in.
Sun yi nisa da tafiya sosai wata maid ta shigo cikin wajan tana tambayar Zahrah me za a kawo musu, Zahrah ta karɓi abin hannun matar ta duba, kana ta zaɓi abin da take so. "Nace ko zaki iya sauyawa wannan yarinyar waje?"Flight attendant ta ce.

"Her name please?" Zahrah ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Something Halisa.." ta ɗan danna wani abu a jikinta tare da yin magana bayan ta gama ta ce. "I think ita ce Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu right Maah?" Zahrah ta ce "No, bana tunanin ita ce her name is Halisa Danejo Rome" Flight attendant ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Sorry Maah babu da wani suna a jerin wanda za su yi tafiya yau, Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu shi ne" A fili Zahrah ta ce "Kan uba" sai yanzu ta tuna sunan Yaa Sheikh kenan, da sunansa akai mata visa kenan?.
"Oh maybe she's the one, zaki iya sauya mata wajan zama?" Matar ta ce "Yes Maa, daman yanzu na duba ta samu sauyin wajan zama tuni" Zahrah tai murmushin jin daÉ—i matar ta kalli Halisa wacce ko inda suke bata kalla ba sai Ajjiyar zuciya take saukewa.
"Can you follow me please?" Zahrah ta ce "ki mata hausa maybe she understand you" matar tai murmushi ganin yadda Zahrah take kwaɓe fuska ta ce "But she's your daughter?" Wata uwar harara Zahrah taiwa matar ta ce "Kinga alamar ina da ƴar ne?" Ita ma tai murmushi ta ce "Ai babu mmki idan nace miki a tunani zaki haifi yara biyar ma" Zahrah ta kalli jikinta da kyau ta kasa cewa komai, sbd baƙin cikin Flight attendant.
"Halisa biyo ni kinji" a sanyaye duk da tsoran jirgin da take tabi bayan matar har zuwa champer 2 na jirgin. Nan ma dai kujeru biyu ce kawai a wajan ba kowa, ta nemi waje ta zauna cike da tsoro.
Not too long da zamanta ya shigo tare da zama kan kujera da sauri ta sunkuyar da kanta domin a tunaninta faɗa zai mata, sai taga mai kulata ba ƙafarsa kawai ya miƙe. Tana zaune aka turo basket na abinci, zallar fruits ne sai gorar ruwa, aka ajjiye a gaban Yaa Sheikh ita kuma aka ajjiye mata chips da egg sai haɗin salad da ruwa. A hankali ya ɗauki orange ya saka bakinsa ya shiga taunawa cikin nutsuwa, Halisa ta kalle shi bakinta na rawa ta ce.
"Amma wannan abin yabann sha'awa ɗan sammani" ya jita sarai amma yai mata banza sai da orange ya ɗin ya rage guda uku ya ɗauki guda ɗaya zai ƙara sakawa a bakinsa tayi saurin riƙe hannun shi, bai zaici haka ba ya kalli hannunta tare da kallon gefen fuskarta ta langwaɓar da kanta gefe ta ce "Ayya ka sammin bana, ni ma idan kaga abuna zan maka naga kana ta haka da idanu" yabi idanunta da kallo yadda ta lumshe su tare da buɗewa tana gwada masa yadda yake, ta kwance na hannunsa tare da kawai bakinta, ta ɗauka wani daɗi ne a orange ɗin.
Ya sauke numfashi ganin hannunta na neman taɓa dugun gemun shi cikin ƙasa da murya mai sanyi ya ce. "Ci kani" ta yi saurin saƙona tana komawa wajanta, bai ƙara taɓa komai ba a kayan sai ruwa daya sha sosai.
Misalin 10 na dare jirginsu ya sauka a Prince Muhammad bin Abdul'aziz International airport, sai nasarwa ake kowa ya saka blet jirgi zai sauka, ganin bata fahimci me ake cewa ba ya kalleta da kyau, ya riƙa ya saka blet a jikinsa ba damar cirewa kuma sun ɗan bada tazara, a hankali jirgi ya fara girgiza yana rawa Halisa ta rikice daga tai nan sai tayi nan, shuuuuu jirgin ya yo ƙasa tai gaba luuu zata kifa shiru tayi jin an riƙo kafaɗar ta, ya haɗa da gefen ƙirjinsa tare da riƙeta.
Ƙuri tayi masa da idanu ganin nasa idon a rufe ta kasa motsawa shima kuma bai saketa ba, tunda har lokacin jirgin bai gama daidaita ba, balle ya samu damar sauka a titinsa. Ɓangaren Zahrah sosai taji daɗin ganin an ɗauke Halisa yanzu zata samu damar kasancewa da mijinta hankali kwance, sai dai tun tana jiran dawowar shi amma shiru gashi bata da ikon tambayar wani, bisa dole tai shiru. Bata tsammaci abin haka ba, sai ji tayi ana faɗin sun ƙarasu Madina tuni ai. A hankali ta saka blet tasan dai dole tare zasu tafi gida. Jirgi na yin parking ya saketa da sauri kafin ta buɗe ido ya fice daga cikin wajan, ta shiga zare idanu yanzu idan guduwa sukai yaya zatai?. Tana wannan tunanin Umar-khan ya shigo yana murmushi ya ce "Matar Malam tasu muje" ta miƙe tana kallon Umar-khan ta ce "To kai gida kaje ka dawo ne?" Yai dare ya ce "Hhhhhh ai kam na koma Nigeria na dawo" tabi bayansa da sauri ta ce "Kasan me" ya ce "sai kin faɗa" ta lumshe idanun ta buɗe ta ce "A ciki da abin ya tashi sama kawai na faɗa kan Malam na ɗauka zai dukeni kamar yadda anti da dake ni, sai naga kawai ya lumshe idanu ni kam nace masa na gode"
Chapter 40 · 0% Book details