← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 55

Sashe 41

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Uhm" kawai Umar-khan ya ce domin bashi data cewa a wanann batun, suna fitowa Zahrah na fitowa suka kalli juna da Halisa kowa ya ɗauke kai. Bayan sun sauka daga jirgin Zahrah ta kalli motar dake gabansu ta ce "Ina My Excellency?" Ya ce "Yana da meeting ne, sai zuwa 12 zai dawo" Zahrah ta ce "meeting da wannan daren?" Umar-khan ya ce "Manyan mutane daman sai dare suke meeting, muje kada mu ɓata lokaci" Zahrah ta shiga bayan mota Halisa ba haka, Umar-khan na gaba shi da driver.
Wata haɗaɗɗiyar area suka nufa gaba ɗaya mazauna wajan larabawa ne, gidan dake kusa da na Yaa Sheikh sune hausawa, faɗar kyau da tsarin gidan Yaa Sheikh ɓata baki ne, flat gida na zamani, motoci birjik a harabar gidan ga tarin flowers da ɓangaren swimming pool, ga
Wajan tsuntsayen shi kusan duk rubutun gidan da rabci ne, yana da ɓangare na Musamman da yake bawa manyan mutane darasi.
Zahrah ta dubi haɗaɗɗan parlourn mai ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru, sai ƙamshi yake, ga wasu fitito masu kyau iya haɗuwa ya haɗu. Umar-khan ya kammala shigo da kayansu ya ce. "Ɓangare uku ne a gidan, wancan ɓangaren Yaa Sheikh na tsakiyar kenan, na gefen dama babu na kowa na hango ma babu kowa, ya ce ki zaɓi wanda kike so, ɗayar ki bawa mai aikin naki" Zahrah ta kalli part ɗin hannun hango taga bayan na Yaa Sheikh yafi kyau dan haka ta ce "Na ɗauki na ɓangaren hango ka shigo mini da kayana ciki" tana faɗin haka ya miƙa mata key ɗin ɓangaren ta amsa hana shigewa ciki. Ya kalli Halisa ya ce.
"Daman girman kine shiga ɓangaren damar" murmushi kawai tayi, Umar-khan ya riga yasan da ɓangaren Yaa Sheikh da wanda Halisa zata zauna a manne suke, domin akwai ƙofa kai tsaye daga ɗakin Yaa Sheikh wacce zata kawo shi ɓangaren Halisa ɗin. Ya ja mata kayan zuwa jiki, ya yi mata bayanin komai da kitchen da banɗaki komai dai, kana ya nuna mata yadda ake amfani da kayan kallon ɓangaren ta.. "Sai da safe Matar Malam" ta jinjina masa kai. Zahrah ma ya kai mata kayan kana ya nufi nasa gidan.
Misalin 1:30 motar Yaa Sheikh tai parking driver ya buɗe masa ƙofa, a hankali ya fito ya ɗan tsaya yana duba ko wanne ɓangare yana yin addu'a sbd ya saba, ganin hadari a garin kuma yasa duk ya rufe Windows na gidan. Ya nufi ɓangaren shi, wanka ya yi ya ɗora jallabiya mai kyau a jikinsa, black tea yake son sha amma bai san yarda zai ba, gashi kuma yasa a sallami masu aikin shi. Haka dole ya zame jallabiyar ya saka kayan barci yana buƙatar hutawa sosai, sbd ya samu peace of mind kwana biyu yana stressed kansa da yawa. Kiran sallar farko a kunan Yaa Sheikh da Halisa domin zamanta wajan mother ta saba da tashin asuba, a hankali ya nufi bathroom tare da sakarwa kansa ruwa mai zafi kana ya yi alwala tare da yin brush, cikin zafin nama ya shirya cikin kyakkyawar shigar shi wacce ya saba, farar jallabiya ya ɗora hirami a kan shi, bakinsa ɗauke da aswaƙ ya nufi Masjid Malik wanda shi ke gabatar da jam'i a can, bayan idar da Sallah ya yi karatu wa jama'a kamar yadda ya saba.
7:00 ya shigo gidan da mmki yake jin parlour ƙamshi mai daɗi, yana ƙoƙarin shigewa part ɗin shi ta ce "Jamɓanduna?" Jin fillatanci yasa ya fahimci ba Zahrah bace amanar shi ce kuma ƴar riƙonsa, ya juya tare da kallon ta, tana cikin wata duguwar riga mai kyau plush pink sai baby hijab a kanta, kai ya ɗauke ta ce.
"Anti Zahrah ba ta shi ba, ni tun É—azo na tashi ina ta kallo" shi dai bai ce komai ba ya shige part É—insa tabi bayan shi da kallo kafin ta juya zuwa kollon girke-girken da ta keyi.
Yana shiga part É—in sa ya zauna saman kujera, tare da kiran number Umar-khan babu jimawa ya É—auka a nutse ya ce "Ka yi komai, kada ya shige kwana biyu a nemi gurbin karatun" yana faÉ—in hakan ya kashe wayar, tare da kiran wata number mgn É—aya ya yi ya kashe..
Halisa na zaune taji telephone line na ƙara ta miƙe sauri daman Umar-khan ya faɗa mata yadda ake amfani da ita, tana ɗagawa taji ance "Mrng maaa, the breakfast is ready Yaa Sheikh na jira" Halisa ta ce "Kika ce me?" Ta ce "Abincin Yaa Sheikh ya kammala kina magana da ɓangaren kitchen, yanzu maid zata kawo" Halisa ta taɓe baki tare da komawa ta zauna, babu jimawa wata mata mai fararen kaya ta shigo ɗauke da tray da butar shayi ta ce "Mrng Maa ga shi Yaa Sheikh na jira"
Halisa ta amsa tana miƙewa tsaye Zahrah ta fito cikin kayan barci da alama ko sallar ba tai ba, ta kalli matar ta ce "lafiya?" Tai mata bayani ta ya mutsa fuska ta ce "Ok daman ita ce mai aiki bata ta kai, ki sama mini breakfast mai kyau yanzu" matar ta juya Halisa ta riƙe tray Zahrah ta ce "Sai ki fara aikin ki tun yanzu, kije ki kai masa breakfast ɗin ki dawo ki shirya mini kayana a wardrobe" Halisa ba ta ce komai ta juyawa zuwa inda taga Yaa Sheikh ya nufa, bakinta ɗauke da sallama bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune kan kujera ta ƙarasu har inda yake ta tsuguna ta ce "Ga shi wai" ya gyara zama yana tsiyaya tea ɗin tare da kaiwa bakinsa. "To kai iya wannan kake sha ne? Ko nayi maka abinci?" Da idanu kawai yake bin gefen fuskarta da kallo ta gyara zama ta ce "Mother ta ce kai mijina ne" ya ware idanu da sauri yana binta da idanu, ta buɗe baki zata sake magana caraf ya saka hannu tare da kame bakin.....

08119237616
Paid book
Not edited
Chapter 41 · 0% Book details