← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 55

Sashe 42

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shiru" ya ce yana sakin bakin tare da mai da Idanunsa kan glass cup ɗin da ya tsiyaya tea aciki. Ta tura baki gaba ba tace komai ba duk da irin ƙaiƙayin da bakin yake mata, haka nan taji kamar ana mintsininta akan Halisa yi magana cikin sauri ta ce.
"Nima ina jin yunwa na sha shayin naka?" Cak ya ajjiye tea ɗin daga hannunsa yana ɗaukan tissue tare da goge bakinsa, ta ɗauki shayin daya rage zata kai bakinta ta ji ance "A'a" ta ajjiye cup tana miƙewa tare da bin bayansa, sahun tafiya da yaji a bayansa yasa ya tsaya, tayi saurin dawowa gabansa suna haɗa ido ya ware mata manyan idanunsa masu kaifi ta tura baki ta ce "Na sake magana banga ka riƙe bakin ba ai" Yaa Sheikh ya girgiza kai kawai tare da shigewa bedroom ɗinsa yana ɓoye yanayin fuskar shi. Ta kalli inda ya shiga sai kuma ta juya tana kwashe tray ɗin. A main parlour ta samu Zahrah zaune tana breakfast ga wata maid nayi mata tausa a ƙafa. "Ke zonan" cewar Zahrah Halisa ta dawo ta zauna tana ɗauke kai gefe guda, saboda har yanzu bata mance mari da zagin da Zahran tai mata ba, Zahrah ta ajjiye spoon ɗin hannunta wanda take shan tea da shi ta ce.
"Kai breakfast ɗin sai yanzu? Ko bai ta shi bane" Halisa ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai tana faɗin. "Shi ya ce na tsaya" Zahrah ta ce "Shi Yaa Sheikh ɗin?" Tai shiru ba tare da ta ce komai, tasan indai zatai magana to zata saki layi ne, Maid ɗin ta kalli Halisa da sauri, ai ko ita da tayi shekara da shekaru tana aiki a gidan Yaa Sheikh magana bata taɓa haɗa su ba, infact ko parlourn shi bata san ya yake ba, Ummul ce kawai take kai masa breakfast ita ma iya dining room, sai ya gama yabar wajan take zuwa ta kwashe, idan kuma yini gida zai yi a ranar basa taɓa zuwa part ɗin, Umar-khan ne ke kai masa dinner, bai fiya cin lunch ba sai dinner, anytime yana tare da butar shayi kamar buzu. Mamaki ya cika Maid ɗin jin abin da Halisa ta faɗa wai shi ya ce ta jira? Who is she to him?.... "Whatever, Ke yama kika ce sunanki?" Maid ɗin ta ce "Bara'at" Zahrah ta ce "Ok, duk wani aiki na part ɗin nan, zuwa part ɗin Yaa Sheikh ya dawo hannun wannan yarinyar, idan kun kammala abinci na Yaa Sheikh ita zata dinga kai masa, bana son na dinga ganin wani abu na ba daidai ba, bana son surutu da hayaniya yana saka mini ciwon kai, ko a gidan ubana ban taɓa sanin hanyar kitchen ba, to a nan ba zan fara saninsa ba, kuna gama girki ki bata ta kawo mini nawa" daga Halisa har Bara'at kallon Zahrah suke, suna mamakin ƙarfin ikon nata, duk da cewa Bara'at bata san matsayin Zahrah ba, amma tasan dole da akwai abin da ta taka a gidan... Zahrah ta kaɗa ƙafa tana faɗin "Ku ɗauke idanunku daga kan mijina, daga nesa kuka ganshi ku sauya hanya, duk abin da kuke nema ni zaku faɗawa, koda abin cin gidan ne ya ƙare" Bara'at ta ce "Ok, amma kula da abincin gidan yana wajan Ummul" It's your problem, I just finished planning what I want" ta juya kan Halisa tana faɗin.. "Jeki breakfast ki saman a bedroom" tana faɗin hakan ta shige part ɗinta, Halisa ta bita da kallo a zuciyarta tana mmkin halin Zahrah. Miƙewa Bara'at tayi Halisa ma haka, tabi bayanta har zuwa sashen kitchen, ma'aikata ta gani mata da yawa ko wanne da abin da suke a kitchen ɗin. Da sauri Bara'at ta nufi wajan Ummul tana ce wa "Yau naga abin mamaki Ummul" kyakkyawar matashiyar matar wacce zata iya shekaru 50 zuwa sama ta kalli Bara'at ta ce. "Da akai me Ukkuti Bara'at?" Bara'at ta sauke numfashi ta ce "Wata mata na gani, mai iko da isa, wallahi na tsorata da yanayinta" Ummul tai murmushi tana ajjiye abin hannunta ta ce "Faɗimatul-zahrah bin Umar Farouk, matar Yaa Sheikh" a tare duk suka ce "Matar Yaa Sheikh?" Ummul ta kallesu ta ce "Na manta ban shaida muku bane, sai a haƙuri da juna ko?" Idanunta ya sauka akan Halisa wacce take dube dube duk abin da suke faɗa tana ji amma hirar bata gabanta, Ummul ta girgiza kai kawai, tana mai jin wani abu a ranta, yarinyar tana nan dai babu sauyi a tare da ita kamar yadda yake nuna mata ita a waya. Hawaye ya sakkowa Ummul ko yanzu ta mutu ta yi farin ciki, Aliyu ya samu gefen rayuwar shi kamar yadda yake faɗa mata a koda yaushe.
Bara'at ta ce "Ummul wace ita kuma wannan?" Ummul ta ce "Masu gidan ce" "Masu gidan kuma?" Cewar Suhaima Ummul ta ce "Ina nufin mai aikin Zahrah ce" ta kalli Halisa da kyau tana mai sakin murmushi ta ce "Sunanta Halisa, ƴar uwar Zahrah ce an bawa Yaa Sheikh riƙon ta amana ne, zatai amfani da sunan Halisa bin Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Halisa ta ƙarasu wajan Ummul da sauri fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi ta kama hannun Ummul ta ce "Laa kema kin sanni ashe, kuma kin san anyi...." Ummul tayi saurin rufe bakin nata tana cewa "Ba'a yin surutu a ɗakin girki, Bara'at akwai tray tana shirya breakfast ki bawa halisa" Bara'at ta ɗakko tray ta bawa Halisa ita kuma ta ce a kitchen ɗin zata zauna ta ci.
Bayan ta gama cin abincin Ummul ta miƙa mata farar madara mai ɗauke da zuma a ciki, batai musu ba ta amsa "Nima ina son na iya girki sosai, ina son yi wa Yaa Sheikh girki mai daɗi" Ummul tayi kamar bata ji zancen na Halisa ba, taci gaba dayin aikin gabanta tana son a akai gidan ciyarwa Yaa Sheikh abincin akan lokaci.
Zahrah na tsaye a gaban mirrow anci uwar kwalliya sai ƙarinin mai take, wayarta dake ringing ta ɗauka ganin sunan Deen ta ce "Uhm maye daman nasan babu mai kirana sai kai" daga cikin wayar ya ce "Ba wannan zaki tambaya ba, fara duba number" da sauri Zahrah ta duba number da mmkin take kallon number ta Saudiya ce,what does that means? Ya katse mata tunani da faɗin "Ki daina mamaki na riga ki sauka a Madina, ke kawai nake jira, don't make any mistakes nazo da maganin da ki ke buƙata, ina son ganinki" The surprise of his behavior prevented Zahrah from speaking. "Wallahi ki san yadda akai ki ka zo, ko ki ganni a gidanki" yana faɗin haka ya kashe wayar babu jimawa ya tura mata address ɗin inda yake, Zahrah ta dafa kai da sauri kuma ta juyawa zuwa ɗaya bedroom ɗin nata a nan ta samu Halisa tana shirya mata kaya a wardrobe, zama tayi ta ce "Ke kin fara menstrual?" Halisa ta ɗauka gyaran kayan take nufi kai tsaye ta ɗaga mata kai alamar eh. Juyawa tayi ta nufi part ɗin Yaa Sheikh.
Fitowar shi kenan daga Library room ɗinsa, ya zauna sanye da wata tattausar Jallabiya a jikinsa hannunsa cikin sumar kansa, cikin nutsuwa ya gyara zama akan duguwar kujerar da yake kai hannunsa riƙe da Cup yana shan green tea wanda Ummul ta kawo masa da kanta, speaking calmly ya ce da Khalil.
"Uhm surutu dai" Ta cikin waya Khalil ya saki dariya ya ce "Ya muke da matarka? Allah ya nuna mini ranar da zata barbabaÉ—a tana É—auke da cikin Yaa Sheikh, koda yake kace baka son ta ai, auren dole akai maka" Yaa Sheikh yaja idanu ya rufe yana jinsa fresh sbd barcin da ya yi, cikin son dakatar da Khalil ya ce.
"Wallahi ba auren dole bane, ni na zaɓi matata It was completely my plan..." Katse wayar ya yi jin yana faɗin abin da mai shirya ba, tare da rufe kansa. Tsaye ya ganta a kansa babu sallama ya ɗauke kai kawai yana ci-gaba da danna waya tare da duba abubuwan da Umar-khan ya tura masa.
Ta zauna kusa da shi tana cewa "My Excellency baka fito ba har yanzu hope lafiya?" Kai kawai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, ta haɗe jikinta da nashi tana cewa "Daman nace ina neman permission zamu shopping da ƴar fillo" har lokacin idanunsa yana kan waya bai ce komai ba. Ta shafi fuskar shi tare da cewa "Ba jimawa za mu yi ba kaji My Excellency" Jotter ya ɗauka da pen ya yi rubutu kana ya ajjiye mata a gefenta haka kurum yaji harshensa ya harɗe baya jin yin maganar. Ganin ƙoƙarin rungome shi take son yi ya ɗan miƙe tsaye, yasan cewa hakƙinta take nema, kuma yasan girma da ƙarfin hakƙi amma ya zai? He's not interested at all, baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin.
Tabi bayan shi da kallo, tana ji a ranta dole ne ma tayi gaggawar aiwatar da burin dake ranta, Yaa Sheikh ya dawo hannunta sai yadda tai da shi tayi imani da Allah idan ya zo hannunta shi da wata Æ´ar mace kuma har abada, ba zai iya kallon kowa a matsayin mace ba dole sai ita, What is the solution? where will she start and what will she do now.
Chapter 42 · 0% Book details