← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 55

Sashe 46

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki Ahmad Nuran Kingdom.
Da sauri yake tafiya hannunsa zube cikin aljihu cikin yanayin kaɗuwa da kuma tashi hankali, saukarsa kenan ƙasar kullum cikin tafiye-tafiye yake, kana kallon fuskarsa kasan baya cikin nutsuwa da walwala. Ko'ina ya gilma acikin gidan sarautar bayi da kuyangi ke zubewa suna gaida shi, amma kallon arziƙi basa samu daga gare shi. Kai tsaye sashin Fulani Atine ya nufa, wata kuyanga ta sanar da Fulani Atine zuwan yarima cikin jin daɗi ta bashi izinin shigowa bayan ta sallami hadiman nata. Tsaye ya yi yana kallonta kafin ta ce. "Meke faruwa da kai El-bashir? Yaushe ka tafi da har zaka dawo?" Yaƙi magana sai huce yake tamkar zakin dake neman abinci bai samu ba. "Wannan ɓacin ran na mene What is the reason for bringing you back to this country now?" Ya ɗauke idanunsa cikin ɗaga murya ya ce "Idan ina raye sai naga bayan Yaa Sheikh hankalina zai kwanta, sai na tabbatar ya wahala a rayuwa kamar yadda ya wahalar dani, zan tirkesa na musguna masa kamar yadda ya sanya ni cikin damuwa da ƙonar zuciya na tsayin shekaru, sanyi amfani da uniform ɗin dake jikina na police na jasa zuciya hanyar da zata ɓata suna da martabar da yake iko da su, ba zan taɓa farin ciki ba muddin ina ganin gilmar Yaa Sheikh a duniya" Fulani Atine tayi murmushi tana mmkin zafin zuciyar da El-bashir yake da ita, a hankali ta ce "El-bashir duk bai kai wannan extent ɗin ba, pls i want u to calm down" cikin zafin zuciya El-bashir ya ce "Ya kai har ya shige extent ɗin da da kike faɗa, a wannan karan dole nayi gaba da gaba da Yaa Sheikh dole nai amfani da mutum mafi kusanci da shi wajan ruguza rayuwarsa data ahhalinsa" Fulani Atine ta ce "Kana da hujja kenan? kana da shaidar da zaka iya kurfanar da Yaa Sheikh a court? Kada ka manta lokacin da al'amarin nan ya faru Yaa Sheikh baya ƙasar bare ka zurfafa cewa shi ya aikata, kada ka tirke kanka maimakon Aliyu, nice shaidarka akan idanuna komai ya faru" El-bashir ya riƙe hannun Fulani Atine ya ce "Ki taimaka mini na ɗauki revenge akan Yaa Sheikh, ba zan iya ba, na kasa haƙura na kasa jurewa Fulani, ya rabani da jin daɗina" Fulani Atine ta ce "Kafin ɗaukan fansa, dole ka nemi kusanci da Yaa Sheikh, dole ka nemi gurbi a zuciyar ƴar fillon da ake magana, kasan yadda kayi ta fifitaka akan shi" El-bashir yai shiru for some minutes kafin ya ce "Mene amfanin saka ƴar fillo cikin al'amarin nan?" Fulani tai murmushi yaro yaro ne, daman ance daka na gaba ake gane zurfin ruwa, ta ce "Idan ka taɓa ƴar fillo kamar ka taɓa zuciyar dake sarrafa tunani Yaa Sheikh ne, nasan abin da kai baka sani ba, kayi hakan" ya shiga safa da marwa He was completely at a loss, unable to understand what she was saying to him. "Nayi masa da baibayi ta ko'ina ina da investigator a cikin ma'aikatan dake aiki a can gidansa na Madina" yana faɗin hakan ya fice rai ɓace.
"Well-done El-bashir Ahmad Nuran Sarki, kana yin komai bisa tsari kamar yadda aka shirya" Fulani Atine ta faɗa tana bin bayansa da kallo. Ma martaba Ahmad Sarki ne ke tafiya shi da Khalil yana yi masa bayanin sauyawar da El-bashir ya yi cikin kwana biyu. Mai martaba na ƙoƙarin yin magana El-bashir yazo ya shige ta gabansu tamkar zai ta shi sama, meke damun El? Kamar wanda ya zauce ko wani abu ya taɓa tunaninsa? "That's what am going to tell you, El ya sauya ko dai akwai abin da yake faruwa ne?" Mai martaba ya numfasa bai ce komai ba ya shige babban sashinsa, Khalil kuma ya nufi wajan Oum Juwairah.

Halisa na zaune tana duba Assignment ɗin da aka bata juya littafin kawai take amma ta rasa ta ina zata fara. Tunda ta dawo gida bata ji motsin Yaa Sheikh ba, ko taji Ummul ta ce akai masa abinci. Ta miƙe tsaye jikinta sanye da wata riga mai kyau wacce tazo mata iya gwiwa wandon jikinta 3gauter ne. Zahrah data fito daga ɗakinta zuwa parlour hannunta riƙe da plate ɗin da aka soya masa ƙwai ta kalli Halisa ta ce. "Ke ubanwa ya ce kina saka wannan kayan a cikin gidan nan?" Halisa ta kalleta ta ɗauke kai ita bata ita take ba "Kan uba? Ke dan ƙaniyarki ni sa'ar ta ruga ce ina magana kina jina?" Halisa ta murguɗa baki cikin tsiwa ta ce "Ban ɗauka magana ki ke ba" hannu ta ɗaga zata wanka mata mari taji an riƙe hannu, ƙamshin Roja daya cika parlourn ya gama shaida mata wanda ya riƙe ta. Ta juya da sauri har lokacin yana riƙe da hannunta ta ce.
"My Excellency yarinyar ta fara raina ni ne, ka barni naci.." wata kyakkyawar tsawa ya daka mata wacce bata taɓa jin irinta ba, Halisa ta firgita da tsawar ga Yaa Sheikh ta kwasa da gudu zuwa part ɗin Ummul tana haki.
Zahrah ta ce "Tsawa kai mini akan wannan mara gata da Æ´ancin Æ´ar aiki na ce ita ga Yaa Sheikh?" Ya saki hannunta fuska kame yana gyara yanayinsa ya ce.
"Ba a kanta ba,
Akan zagin da ki ke mana, idan zaki ki bari kije waje" ya faɗa a taƙaice kwarjininsa yasa Zahrah kasa tanka masa a ranta kuma ta ɗauki niyyar cin uban Halisa. Cike da kissa da buƙatar mijinta kusa da ita, cikin dake jikinta ya ƙara sanya mata son kasancewa da namiji ƙwarai da gaske. Ta rungome Yaa Sheikh tana shassheƙar kuka ta ce "Amma kasan ni ba sa'ar ta bace, kawai zan mayar da ita, tunda akwai masu aiki a gidan" ya yi mata shiru shi dai bai kuma hanata rungome shi ba, kallo ɗayan da ya yi mata ya karanci yanayinta. Ganin abin da take ƙoƙarin yin yasa Yaa Sheikh faɗin. "Asstagafirullah Allah" Zahrah ta tsaya tana kallon shi kafin ta ce "what do you mean by that? Am your wife exit?" Ya zameta daga jikinsa tare da juyawa zuwa part ɗinsa sai da ya kusa shigewa ya ce
"Lokacin Sallah, akwai alwala tare dani" tai murmushin jin daÉ—in ganin ya juya da alama alwalar da yake riritawa ta lalace dalilin rungumar shi da tayi. "Shikenan, anjima zan zo" ta juya zuwa nata part É—in.
Ummul ta kalli Halisa dana cewa "Wannan hakin fa? yana da kyau ki nutsu sosai matar malam" Halisa ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na tsorata sosai Ummul, Allah yasa ba dokan Anti Zahrah ba" Ummul ta dubeta ta ce "Doka wanne iri, ni wannan Assignment ɗin naki ba Abin da na gane, kije wajan Abban naki" ta kwanta cinyar Ummul tunanin Dadarta ya faɗo mata a rai. Tai shiru can kuma ta ce "Ummul Abba mijina ne ko?"
"Me ya sa kike tambaya matar malam?" Cewar Ummul. Halisa ta miƙe zaune zance na cinta ta ce "Ummul naji baya ce mini matar shi, kuma ni bana son naga Anti Zahrah..." Wayar Ummul tai ƙara hakan ya hana Halisa ƙarasa maganar. Bayan kammala wayar Ummul ta ce "kije ya duba littafin naki,ko a buge ki a makaranta" Halisa ta ɓata fuska ta ce "haka kurum ya dakeni, zaro ido naga ya yi fa?"

"Ko zai daki kowa,
Ai banda matar malam, kawai baya son taurin kai ne, kuma na lura kina da shi tun ba yau ba" Halisa zata sake magana Ummul ta ce "Tashi kije, sai ki dawo kici dinner muyi karatu" ta miƙe tana ɗora hula akanta tana tafe tana waƙa da fillatanci. A hanya taci karo da Bara'at tai mata murmushi.
A hankali ta shiga parlourn dake part ɗinsa, gaba ɗaya baya cikin parlourn sai kyakkyawan ƙamshin daya bari wanda yake tashi a hankali, tabi ƙofofin dake parlourn da kallo ta rasa wanne Kofar bedroom ɗinsa, a hankali take tafiya kamar mara gasky tana raɓewa jikin bango ta shiga leƙa wani ɗaki tsarin bedroom kaɗai ya tabbatar mata shi ne. Ji tayi an tsaya a bayanta ta juya da sauri taci karo dashi tsaye towel a hannunsa yana tsane gashin kansa daya kwanto, ganin ruwa na zuba a jikinsa tasan wanka yayi, maimakon taji kunya a matsayinta cikakkiyar bafullatana sai ta zubawa wani waje a jikinsa ido. Ya tsare ta da idanu.
"Abba" ta faɗa dimple ɗinta na lomawa ya ɗauke kai ya ce. "Me kike leƙe? Kin yi ajjiya ne?" Ya tambaya yana bata hanya ta tura baki fuska a narke sai juya bakinta take ta ce "Ummul ta ce ka koyan karatu, ni ba kai nake nema ba" ya dubi bakin maganar da kyau, ya ɗauke kai wato fushi take har yanzu.
Ganin yaƙi bata amsa ta saki kuka tana juyawa zata bar wajan, ya damƙi hannunta ya dawo da ita gabansa. Cikin kula da tausasa harshe ƙamshin shower gel yana fita daga cikinsa ya saka hannu tare da tallafo haɓarta ɗaya hannun ya dafa kanta dashi, tayi saurin riƙe ƙugunsa da duk hannunta biyu.
"Abba" ta ƙara faɗa idanun na cika da hawaye wanda suka ƙarawa idanunta sheƙi. "Rigima dai matar malam, nayi busy banje makaranta ba" ta tsora masa idanu masa idanu tana ƙara riƙe ƙugunsa ta ce "To darasi zaka duba mini, Abba kuma me ya sa Anti Zahrah take riƙe ka" ya saki fuskar yana dafe kai ta saki kuka zata juya ta fita ya saka hannu ya ɗaga ta cak tare da yin bedroom ɗinsa da ita...

If you read for free🤷🏾‍♀️ it's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.
Chapter 46 · 0% Book details