← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 55

Sashe 18

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai ko zai yi shekara ɗaya bai kalli ko wacce ba, Wallahi sai dai ya auri mata biyu" Yaya Halima ta ce "Naji zaɓin Uba, wace kuma zaɓin uwa?" "Bani da zaɓi amma duk wacce Allah ya nufa data kwanta mini ko ƴar gidan wace zan saka Hakimi ya ɗaura musu aure"
girgiza kai kawai Yaya Halima tai tana faɗin "Wata drama ɗin abin dry a gidan Engineer da Barrister a bani abinci naci ni dai" Mother ta miƙe tana kiran sunan Maimoon. Fitowa tayi daga part ɗinsu jikinta sanye da duguwar riga ta rusuna ta ce "Ina yini Mama?" Yaya Halima ta ce "Lafiya lou Maimoon ya karatu? Kwana biyu Mother ta hanaki zuwa ko?" Maimoon ta juya ta kalli Mother wacce ta ɗauke kai tamkar bata jin abin da suke cewa ta ce "A'a Mama, karatu ne ya yi zafi amma muna exam zan zo"
"To Allah ya taimaka, a kawo mini abinci" murmushi Maimoon tayi ta nufi kitchen. Yaya Halima ta kalli Mother tana mamakin zafin zuciyar ƙanwar ta ta. Arabian Mandi rice wacce ta sha kayan haɗi sai ƙamshi take Maimoon ya zubu a plate tare da haɗin salad da ya sha bama da egg with some of vegetables. "Ki sakko muci abinci Maryam" Mother ta ɗauke tana faɗin "Anya? ci kawai Yaya bana jin zan iya ci" murmushi kawai Yaya Halima tai tana faɗin "Allah ya kyauta komai ya yi zafi maganinsa Allah"

Yana tsaye gaban madubi banda huci babu abin da yake maganganun father nayi masa amsa kuuwa a kunnuwansa "Bashi da amfani, bai taɓa yi mini rana ba, ya yi mini asarar contract ɗina" hannu ɗaya ya sanya ya dafe kansa dake masa ciwo sosai, ɗaya hannun kuma ya rufe kunnansa a zatonsa hakan zai taimaka wajan rage tuna maganar mahaifin nasa. Ɗago jajayen idanunsa ya yi ya tsurawa kansa ido ta cikin madubin. A wannan karan dole ya nunawa father shi ma namiji ne yana shiru ne sbd bai damu da duniya da abin da ke cikinta ba. Juyawa ya yi zuwa Library ɗinsa dake gidan Hakimi. Zama ya yi saman kujera cikin sauri ya duba dukkan mayan kadarorinsa kama daga kan filaye, gidaje, ɓangaren Library na karatun addinin dana kimiyya ya buɗe, S.A.H bank duk yana fahimtar dukiyar tasa har ya kasa shi kansa bai yi tunanin abin da ya mallaka ya kai girman hakan ba, a haka kuma bai haɗa dana wajan Mother ba wanda suke mallakinsa. Tunani ya fara tunda yana da bank a kano me zai hana ya buɗe S.A.H BANK a sauran jahohin da suke Nigeria? Da kuma kamfanin sarrafa shinkafa ƴar hausa mai kyau wacce za taiwa talakawa sauƙin siya kan fara shi mai sauƙi?. Da wannan tunanin ya yi na'am da zuciyarsa cikin nutsuwa ya fita daga Library ɗin ya koma haɗaɗɗan bedroom ɗin nasa, kai tsaye toilet ya shige tare da sakarwa kansa shower yana sauke numfashi a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar yama mance da batun aure baki ɗaya. Domin daman shi bai dame shi ba indai macace da kanta zata gudu ta ce bata son shi domin ba zata samu abin da take buƙata ba daga gare shi. Fitowa ya yi yana ƙamshin shower gel Shea body butter ya shafa jikinsa ko body spray bai fesa ba ya cilla mint bakinsa tare da kwanciya saman bed ya rufe idanunsa.

Umar-khan ne ya shigo cikin parlourn Abba Hakimi bakinsa É—auke da sallama. A hankali Abba Hakimi ya ajjiye azkar É—in hannunsa wanda yake na yamma tare da duban Umar-khan cikin kamala da kamewa ya ce.
"Umar-khan yaya dai?" Shafa kai ya yi yana tare da faɗin. "Abba Hakimi daman Mother ta ce ko Sheikh yana nan? Gaba ɗaya baya can gida" murmushi mai laushi Abba Hakimi yai yana zame idanunsa daga kan Umar-khan ɗin "Aliyu ai ba yaro bane?" Abba Hakimi ya faɗa a gajarce Umar-khan ya miƙe ba tare daya samu cikakkiyar amsa daga bakin Abban Sheikh ɗin ba ya ce "Ni ma zan je gida, sai da safe Abba Hakimi" yana buɗe azkar ɗin ya numfasa kaɗan cikin sakin fuska ya ce "A gaida Abdulrashid"

"Zaiji sosai"
Umar-khan ya amsa wa Abba Hakimi yana barin gidan baki ɗaya tare da tunanin inda Sheikh ɗin ya yi domin yana tsoro idan zuciyar ta motsa kowa sai yaji babu daɗi. Momi A'isha ce ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci zama tayi bayan ta ajjiye ta ce "Ina ta mamakin abin da ya sanya mahaifin Sheikh ke aikata haka kamar wani mara ilimi, kuma ya dace ace ka saka baki ko auren ya keso Sheikh ya yi sai ka zaɓa masa ƴar mutunci, kaga hankalin Barrister bai kwanta da zaɓin Engineer ba" gaba ɗaya Abba Hakimi ya tattara nutsuwarsa kafin ya ce "Ku dai mata yawanci tunaninku ɗaya, bani da ikon ture umarnin uwa ga ɗan shi,kada ki manta ni uban rana ne kuma mariƙi, I don't have the courage to deny the Engineer what he wants"

"Gaskiya dai, ni ina tunanin ko sbd Sheikh bashi da lafiyar yin magana cikin jama'a ya sanya Engineer ke yi masa haka? Kuma yana ganin He is the only male among his children, shi ne ya kamata ya tsaya kan harkokinsa na yau da gobe ya É—auki buri ya saka akan Sheikh É—in?" Abba Hakimi ya amshi fruits É—in data gama yanka masa kafin ya kalleta da kyau ya ce
"Baki ke aiki ko ƙwaƙwalwa? Babu wani abu da Sheikh ba zai iya ba, In-ina kuma Ubangiji ya ɗora masa muna fata a koda yaushe ta zama sauƙi a gare shi" "haka ne Allah ya bashi lafiya, anjima zani gidan Barrister ɗin" Abba Hakimi ya ce "Ki yi zamanki" ta kalle shi ta ce "Amma me ya sa?" Shiru ya yi mata tasan ba zai bada amsa ba, kuma tunda ya ce haka yana nufin hakan har ransa.

A can commission Quarter's dake cikin garin Yola/ jimeta a hankali take driving saman makeken kwaltar da zai sadata har zuwa gida, numfashi ta sauke a karo na ba adadin tana kallon titi kunnanta kuma ma sauraran abin da Surayyerh ke faɗa tsaki ta ja ta ce "You bother me with noise wlh Surayyerh koda yaushe problems ɗinki da mahaifiyarki baya ƙare wa?" Surayyerh ke ta ce "A sbd ba ke bace ko? Gaba ɗaya ta takura ni wani lokacin gani nake kamar ba ita ta haifan ba" da sauri Zahrah ta juya ta kalli Surayyerh ta ce "Ashe daƙiƙiyya ce ke? Whatever is your problems ki barni da tawa matsalar" dry sosai Surayyerh tayi tana tafa hannu ta ce "Oh! Sorry ashe fa ciki yaƙi zubewa yanzu dole ki amincewa Deen kuyi aure" Zahrah stopped Surayyerh from what she was saying ta ce "And who told you cikin Deen ne? Ni kai na ban zan cikin waye ba, ban damu kuma dana sani ba kawai na zubar da shi ba aure a tsarina a yanzu dai" Surayyerh ta gyara zama sosai ta ce "Kin san Allah a yanzu babu abin da nake so sama da aure, sai yanzu na fahimci karatun bokon nan is nothing wani abu ne wanda kana cikin gidan mijinka ma zaka iya yinsa" Zahrah bata ce komai ba tunaninta yana can yana da tabi cikin jikinta ya zube ba tare da Mimi ta lura da shi ba. A haka suka ƙarasa gida gatekeeper ya buɗe musu. Sosai tai mamakin ganin motocin Dady yaushe ya dawo bata da labari? Dawowar gaggawa?. Fitowa tayi hannunta riƙe da L.G bag daman babu mayafi jikinta kayan sun kama jikinta sosai, jerawa sukai ita da Surayyerh zuwa cikin gidan. Dady da Mimi ta bi da kallo ganin suna magana a hankali, Dady yai murmushi ya ce "Finally She's back zo nan Zonan Zahrah" ya miƙa mata hannunsa ƙara sawa tayi ta zauna kusa dashi tana rungume shi ta ce "Wlcm Dady" kallonta ya yi da kyau ya ce "Zahrah magana za mu yi mai Muhimmanci" ta gyara zama ta ce "All ears Dad" ya ce "Kin san aminina Engineer Aliyu?" Ta ɗaga ta ce "I think I knw him Dad mene ya faru?" Ya ce "Kin san wancan dake jikin photon?" Juyawa tayi ta tsurawa photon Sheikh Aliyu haydar Aliyu dake maƙale jikin bangon parlournsu zuciyarta ta ɗan buga ta girgiza kai ta ce "Ban shi ba Dad, amma na san yana da muhimmanci tunda aka photon sa a gidanmu" ya jinjina kai ya ce "Yana da muhimmanci a gareni da rayuwata baki ɗaya, Zahrah wannan da kike gani akansa duka wasu burukana suke, ina son na haɗaku aure da Sheikh Aliyu haydar Aliyu cikin satin nan" zabura tayi ta miƙe tana zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa sosai ta kasa magana baki ɗaya. Mimi ta ce "Daman nasan Zahrah ba zata amince ba, domin ko Tafsir ɗin ta tsana" Dady ya ce "Ya zama dole ta amince sbd karayar arziƙin dake shirin tunkaro mu ba tare da mun shirya ba, Zahrah ki yarda ki auri Sheikh zaki farin ciki namiji ko a maza samun irinsa zai wahala kiyi mini wannan alfarmar" Ajjiyar zuciya ta sauke ta ce "Dady na amince da buƙatar, amma idan har daga ni ba zai sake auren ko wacce mace ba ina nufin babu kishiya...

Na kusa gama free pages. IDAN BA KE it's 500 gaba ɗaya book 1,2 har ƙarshe. Via 6850917335 Na'ima Shuraihu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616 ƴan niger suyi mini magana na faɗa musu yadda zasu biya.

DESTINY
TRUE LOVE
ROMANCE
TRUST
SARAUTAR MARUBUTA

*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Nimcyluv sarauta_*
Chapter 18 · 0% Book details