← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 55

Sashe 15

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba Hakimi da Mother suka nufi state c.i.d hankali a tashe Maimoon da Zeefa da Fattoumah sai kuka suke a rayuwa suna ƙaunar yayan nasu duk da babu wata jituwa a tsakaninsu. Ko abinci suka kasa ci sai sallah kawai da suke suna addu'ar Allah ya kuɓutar da Sheikh ɗin. Hankali kwance Father yake zaune yana waya da babban amininsa ko da wasa bai masa magana akan matsalar da suke ciki ba, duk da cewa al'amarin ya gama zaga ko'ina a faɗin Nigeria.
A kiɗime Mother take bin su Saif-Wazir da kallo ganin yadda idanunshi ya yi jajur alamar kuka suka sha. "Ina Babana ina Aliyu mai ya faru da shi?" Shiru Saif-Wazir ya yi mata, ta juya kan Umar-khan ta riƙe wuyansa sosai cikin faɗa ta ce "Where's my son Umar-khan? Ina Aliyuna?" Umar-khan ya yi ƙasa da idanun shi ba tare da ya ce komai ba. Sakin Umar-khan tayi ta nufi wajan Ishaq-hakim ta ce "Ishaq-hakim faɗa mini gsky ina Aliyu me akace yana da gsky ko? Ba aikata abin da ake zarginsa ba?" Hannunsa ya ɗaga tare da nuna mata wani waje da sauri ta juya Idanunta ya sauka akan Sheikh Aliyu Haydar Aliyu wanda aka cire masa Jallabiyar jikinsa aka ɗauresa da Sarƙa tun daga wuyansa hannunsa zuwa ƙafarsa farar fatar jikinsa tayi jajir bakin Ishaq-hakim na rawa ya ce "Mother Sheikh ya amsa laifin da ake zarginsa ya tabbatar shi ne ya lalata ƴan matan hadda ciki.....

_*IDAN BA KE...* labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irinsa ba, ƙaddarar labarin akan soyayya ne mai tsayawa a zuciya da saka shauƙi a zuƙatan masu karatu..... Tsammaci abin da baka tsammani salo na musamman🫣💋 08119237616._

*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

10....
Kasa magana Mother tayi sai Ishaq-hakim da tabi da kallo tana son gasgata abin da yake faɗa. "Ta ya ya Sheikh zai amsa laifi fyaɗe? Laifin da duk duniya ta san ba zai iya aikatawa ba?" Ta faɗa a fili tana sakin wani raunataccen kuka mai tsayawa a zuciya ba zata iya kallon Sheikh cikin sarƙa a ɗaure ba, kamar wani ɗan fashi ko Kidnapper. Umar-khan ne ya kama Mother wacce take ƙoƙarin zubewa a wajan sbd kukan da take idanunsu ya yi jajur ya ce "Ki daina kuka Mother, wata kila Sheikh ya amsa laifin ne sbd rashin mafita, mu duka abin ya zo mana cikin wani sabon yanayi wanda bamu taɓa riskar kanmu ciki ba, Ubangiji ka ɗai ya san gaskiya kuma shi muke roƙa ya fidda Sheikh Aliyu daga cikin wannan jarrabawar" gaba ɗaya zuciyar Mother ta karaya tunaninta ya tsaya cak duk inda take neman wata hujja ta kare ɗan nata babu.
Da hannu bibbiyu ta riƙe Umar-khan ta ce "Kai ne kake tare da Babana Umar-khan, ka taimaka mini nasan kasan Aliyu ba zai iya aikata hakan ba, yana tsare imaninsa yana amsar rayuwa a duk yadda ta zo masa" Umar-khan ya mayar da hawayen dake cika idanunsa kafin ya zaunar da Mother ya ce "Be patient Mother, muyi addu'a kawai amma da ace zan iya bada shaida, da iya abin da zan faɗa ya isa ya wanke Sheikh daga cikin zargi"

"That's enough, this is not a place to make noise" Wani daga cikin jami'an tsaron ya faÉ—a yana daka musu tsawa.
Sai a lokacin Abba Hakimi ya yi ajjiyar zuciya domin shi ma Al'amarin ya girgiza shi fiye da tunanin kowa, zuciyarsa shi zafi take masa sosai. A nutse ya juya ya kalli Ishaq-hakim ya ce "Ka mayar da Barrister Maryam gida yanzu, ka ce ina buƙatar ganin Aliyu immediately" da girmamawa Ishaq-hakim ya amsawa mahaifin nasa, idanunshi akan Mother yana jiran ta miƙe.
Cikin kuka ta kalli Abba Hakimi ta ce "Ina son nayi magana da Aliyu Please Hakimi" Kafin Abba Hakimi ya bata amsa wani daga cikin Jami'an tsaron ya ce.
"No way Madam" tana share hawaye ta ce "Don girman ka bani 2 minutes nayi magana da ɗa na, ina son tambayarsa, tare da kwantar da hankalin shi" cutting nata out ya yi da faɗin. "Isn't necessary Maaah..." A ƙagauce Abba Hakimi ya ce "take her out Ishaq-hakim" Mother na kuka sosai tana kiran sunan Sheikh Aliyu aka fitar da ita waje, Aliyu shi ne rauninta ka kaf cikin yaranta tafi ƙaunarsa duk abin da Mother ta mallaka daga cikin dukiyar iyayenta Aliyu ta bawa, She owned all her property for him, Lands, houses, companies, all signed in the name of Aliyu's property.
Su Mother na fita Abba Hakimi ya kalli jami'an tsaron cikin murya mai taushi ya ce "Kun samu hujja mai ƙarfi da kuka kama mini ɗa na?" Ɗaya ya sunkuyar da kai cikin girmamawa ya ce "Har yanzu bamu da hujja, amma a duk bin ciken da mukai Sheikh ƙara shiga ciki yake, yaƙi buɗe baki ya yi magana, gwamnatin Madina da universityn ƙasar sun matsa akan kwana biyu suka bayar idan ƙasa Nigeria bata ɗauki mataki ba, zasu ɗauka da kansu domin su irin wannan cases ɗin kai tsaye suke bincike kuma hukuncin kisa ne" runtse idanu Abba Hakimi hukuncin kisan ya daki zuciyarsa ainun. Umar-khan da bakinsa ke rawa tun ɗazo sbd masifa ya ce "Ita kanta gwamnatin Madinan idan bata da hujja dole ta haƙura, ina masu kawo ƙarar? Daga ina wannan zan can ya fito? Ina ƴan matan da akaiwa fyaɗen suke?"
"Stop raising your voice, we are working on our system, nan ba Court bace" Umar-khan zai sake magana Abba Hakimi ya yi gyara murya kafin ya ce "Ka bari abu komai a nutse, shi ya sa na mai da Barrister Maryam gida" Saif-Wazir dai na tsaye duk yadda suka so a basu Sheikh su yi magana hanawa akai. Kuma a gobe za a kaisa court domin fara gabatar da Shari'a tun da case É—in ya zo da hargitsi. Haka suka komai gida zuciyoyin kowa babu daÉ—i.
Sheikh na zaune daga shi sai single da wani farin trousers mai laushi tunda yake a duniya babu wanda ya taɓa ganin tsari da zubin halittarsa sai yanzu, an tuzarta shi tuzarcim daya har zuƙa kuturwar zuciyarsa, shi kaɗai sai tsuma yake shi da ko sauro baya so baya ƙaunar yaga baiwar halittar da tsaraicin jikinsa, yana tsarkake jikinsa domin sirrinsa ne, amma yau da wanda ya dace da wanda bai dace ko wanne tom and jerry gani yake abin ya yi masa zafi ainun. Dalilin daya sanya ya amsa laifin kenan ba tare daya shirya hakan ba.

Mother na komawa gida ta samu Fattoumah na zaune ita ɗaya a Parlour da sauri Fattoumah ta ce "Mother ina Yaa Lee? Ba zai dawo ba?" Murmushi mother ta yi tana ɓoye damuwar ranta ta ce "Ya dawo mana Manana, yan gidan Abba Hakimi where's your sisters?" Da hannu ta nuna mata part ɗinsu, Mother ya kama hannunta suka shiga ciki. Yaran duk suna zaune sanye da hijabi sunyi shiru bayan sunci kuka sun ƙoshi, cikin faɗa ta ce "Maimoon, Zeefa what's this? Kuna da hankali zaku shigo ɗaki kuyita kuka kamar anyi mutuwa, Depression kuke son ya kamaku ko mene?" Gaba ɗaya suka miƙe tsaye jikinsu na rawa za su yi magana ta ɗaga musu hannu ta ce "Ku fita a nan wajan, maza aje a kunna kallo ayi" fita gaba ɗaya sukai jiki babu ƙwari mother ta bisu da kallo tausayin su na kamata tasan duk sanadin Aliyu Haydar suka shiga wannan damuwar. Kuma ita idan har ƴar halak ce ba zata sake zuwa wajan Father ba akan maganar Sheikh Aliyu ɗin ba.
Tana fitowa daga cikin bedroom ɗin upstairs ta haura zuwa nata bedroom ɗin wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Barrister Zainab akan gobe zasu shiga Court sun daɗe suna waya kafin ta kira Yaya Halima anan ta kwantar mata da hankali ta ce ita ma ta nan zuwa dan sunyi nisa ne. Har Mother ta miƙe da sauri kuma ta koma ta zauna domin gaba ɗaya ta manta da batun Jadda cikin sauri ta danna numberta wayar ta jima tana ringing kafin a ɗaga a fusace akace "Allah dai yai gutsi gutsi da duk wanda yake addabata wannan masifar har ina, ba lallai mutum yaga Annabi ba" A hankali Mother ta ce "Jadda ni ce Maryam" Jadda ta ce "Wata abace Maryam kuma? daga wacce duniya mena haɗa dake?" Shiru Mother can kuma ta ce "Mahaifiyar Sheikh Aliyu" Jadda ta zabga salati da duk ƙarfinta ta ce "Yanzu Maryam cewa nayi ban gane ki ba? Masifar gaisuwa ce bana so, Ina shi Aliyu yana can Madina ɗin ne?" Mother ta ce "Baki san meke faruwa da shi ba?" Jadda dake kishin giɗe tayi saurin Miƙewa zaune tana faɗin "Allah ya isa, dake Maryam da shi Aliyu Allah dai ya isa wani abu ne ya samu Sheikh bani da labari?" Kafin Mother tai mgn father ya ƙwace wayar tare da kashewa baki ɗaya ya kalli Mother ya ce. "Yanzu Barrister akan wannan maganar zaki haɗani da Mahaifiyata? Su kike ta tsine mini tunda kin san bakinta ba shi da tsarki wajan sakin magana da kwasa ta" banza tai masa ba tare da ta ce komai ba, yana ƙoƙarin sake magana ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan ka gama ka ajjiye mini wayata, I have something to do with my phone" tana faɗa ta shige toilet domin zuciyarta a kusa dake da shi. da idanu ya bita kana ya ajjiye wayar yana mmkin halin mata a wasu lokutan.
Chapter 15 · 0% Book details