Sashe 29
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Misalin 12 hall event ɗin ya cika da ƴan mata da kuma samari D.j ke tashi kamar zai fasa hall ɗin, amarya Zahrah ta sha ado cikin wata pink ɗin gwon gaba ɗaya half ɗin ƙirjinta yana waje. Yaƙe kawai sbd rashin ƙarasuwar ango Yaa Sheikh da bai ba gashi friends ɗinta sai tambaya suke kowa ya damu da yaga wanne mai tausayin ne ya auri Zahrah?.
Sautin Algaita da suka ji a can wajan hall ɗin ya sanya Surry ta shi da sauri ta nufi wajan, manyan motoci ne guda wajan huɗu sabbi dal sai ƙyalli suke. Fuskar Surry ta sauya launin lokaci guda ta gane Yaa Sheikh ne da friends ɗinsa. Ta kasa motsawa wani abu na cakar zuciyarta, tana tsaye taga wasu matasan samari ko wanne da fararen kaya har ƙasa sun rufe musu ƙasa ko takalmin su ba a iya gani, motar ƙarshe wacce ta kasance da Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu wani saurayi ya buɗe ta, cikin nutsuwa ya fito shima yana sanye da fararen kaya mai Alkyabba rigar har ƙasa tana jan ƙasa. Ya ɗago kai a nutse suka haɗa idanu da Surry tayi saurin ɗauke idanunta bata taɓa ganin ƙwayar idanu mai tarwatsa zuciya irin ta Yaa Sheikh ba. Cikin sauri ya juya zuwa hall ɗin labari tuni ya isa kunnen Zahrah farin ciki ya lullube zuciyarta. Mc ya fara sanar da zuwan ango Zahrah ta tasu tunda Yaa Sheikh ya ganta sau ɗaya bai sake ganinta ba, domin ba ita yake nema ba a yanzu. A haka suka jera har yanzu wajan zaman da aka tanadar musu, lokacin zuwa lokaci idan Zahrah ta haɗa idanu da Yaa Sheikh sai ya sakar mata murmushi abin mamaki haƙura biyu kacal take gani a cikin bakin nasa, ta dai daure. Lokacin da akace su tasu zuwa filin hall ɗin idanunta ya sauka akan ƙafar shi da rigar ta zame, wani irin zaro ido tayi gabanta ya faɗi jikinta ya hau rawa sbd ganin kofato da tayi maimakon ƙafa, ta ɗago kai da sauri suna sake haɗa idanu ya buɗe mata bakinsa mai ɗauke da haƙura biyu. Wani ihu ta fasa a wajan tare da sulalewa babu numfashi. Surry da sauran friends sukai kan Zahrah ba tare da sun lura ba ango da abokan shi suka ɓace daga wajan.
Wanda ake tunanin shi ne Yaa Sheikh suna fita daga hall É—in ya yi wani ihu tare da girgiza ya rikiÉ—e zuwa Aljani Prince Bilal. Sauran wanda akace abokan shi ne suma suka rikiÉ—e zuwa Aljanu.
Cikin wata murya mara daɗi Prince ya kalli Sandu ya ce "Na samu nasarar kashe babana, tsayin kwanaki ina neman matata Danejo amma babu ita, babana ya cuce ni ya sanya na manta kamarta yanzu ko na ganta ba zan san ita bace idan ba zoben dana bata na gani ba" Sandu ya ce "Ai zoben ya fara dacewa mu nema, tunda kace yana wajanta ko?" Prince bakinsa na fidda hayaƙi ya ce "Yana wajanta" hura iska daga cikin bakinsa sai ga wani photo ya bayyana na tambarin masarauta ya nuna musu tambarin ya ce "Duk inda kuka ga zobe mai tambarin nan a hannu wani to shi ne zoben hannun matata Danejo,da zoben da ita a kawo mini su, maza kuje" ɓat suka ɓace daga wajan, Prince ya juya ya kalli hall ɗin da ake partyn kamar zai koma ciki sai kuma ya ɓace ɓat shi ma.
Ƙarfe 2 na daren Asabar ɗin jirginsu Yaa Sheikh ya sauka a Yola International airport, kai tsaye motoci suka ɗakko su zuwa cikin wani haɗaɗɗan hotel, tawagar Abba Hakimi daban, ta Father daban, sai su Saif-wazir, Umar-khan, Ishaq-Hakim, Khalil Ahmad Sarki, El-bashir. Dashi kansa Mai martaba.
Har zuwa lokacin Yaa Sheikh ya kasa yarda wai ɗaurin auren shi aka zo, da yarinyar da ko sanin kamanninta bai ba, kuma bai damu daya sani ɗin ba. Washegari Lahadi aka ɗaura auren Zahrah Farouk da Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu akan sadaki dubu ɗari yadda Abba Hakimi ya bada. Ran Father ya ɓaci shi da ya so a bada dubu ɗari biyar ko miliyan guda.
Abba Hakimi na cikin mutane Saif-wazir ya zo kusa da shi murya ƙasa ya ce "Abba ga motar can ya kamata muje" Abba Hakimi ya miƙe tsaye hannunsa riƙe da sanda yabi bayan Saif-wazir zuwa cikin mota.
Kai tsaye Rugar Bello Saif-wazir ya nufa yana faɗin "Ina Yaa Lee zai kai wannan matar? Wallahi Abba kallon sani nake mata kuma na manta inda na taɓa ganinta" Abba Hakimi yai murmushi yanayin garin Yola na birge shi ya ce
"Saifuddeen ina rabaka da shiga sabgar da bana ka ba" Saif ya ce "da gaske Abba, tabbas na san fuskarta na manta ne kawai" ya faÉ—i haka yana parking daidai inda suka tsaya last time shi da Yaa Sheikh.
Abba Hakimi ya fito suka jera da Saif zuwa Rugar Bello, kamar yadda yasan Rugar haka É—in ya sameta suka samu ArÉ—o dasu GiÉ—aÉ—o. Bayan duk sun zauna Saif ya ce "Nasan baka gane ni ba ko?" ArÉ—o yai jim alamar nazari can ya ce "Gaskiya bai shaidaka ba" Saif ya gyara zama ya ce "mun zo kwanaki ni da É—an uwana,kuka ce wai ya yiwa wata Æ´ar fillo fyaÉ—e har kuka É—aura masa aure da ita?" ArÉ—o ya ce "tuh! tuh! Masha Allah na gane shi yana ina? Ina kuma matar tashi nake?" Zuciyar Saif ta buga, ya kalli Abba Hakimi kafin ya kalli ArÉ—o ya ce.
"Wannan shi ne babana kuma baban Sheikh ɗin, daman yarinyar baya dawo gida bane? Ai mun kaita asitibi ta gudu" Arɗo ya girgiza kai ya ce "Ayyah shai dake ba a nan Rugar take ba, muma ganinta kawai mukai amma ba ƴar Rugar Bello bace" Abba Hakimi da Saif suka kalli juna kafin Abba Hakimi ya ce "Ikon Allah, yanzu bayan wannan rugar akwai wata ne" Arɗo ya kalli Labo, Labo ya girgiza masa kai, tunaninsu wani taimako za a bawa Fulani a fili Arɗo ya ce "Ai kaf Yola nan ce kawai Rugar Fulani, ba lallai idan ƴar garin bace" Abba Hakimi ya dinga kallon Arɗo yana mamakin wannan bankaura, daga kallon sarkin fawa sai miya tayi zaƙi? Kawai daga ganin Sheikh sai sukai masa bahaguwar fassara a tirɓayar tunaninsu mara kan gado.
Jiki a saɓule Abba Hakimi da Saif-wazir suka miƙe zuciyoyinsu babu daɗi. Bayan sun shiga mota Abba Hakimi ya sauke numfashi ya ce "Abin mamaki,ban taɓa jin wannan kwaɗon ba sai yau" Saif yai murmushi ya ce "Fulanin kenan Abba, yanzu ina zamu nemuwa Yaa Sheikh uwar gidan shi?" Abba Hakimi yana yin murmushi saboda wani tunani daya faɗo masa ya ce "Uwar gidan da baya so? Bari mu buga wasa waye zai nasara? Mai gidan? Ko Amaryar? Ko kuma Uwar gidan da ba a san inda take ba?" Saif ya ƙara sakin murmushi ya ce "Wannan shi ake kira da bikin zuwa ya samu babu zanin ɗaurawa, zan so naga yadda wasan ya zai fara ni ina team ƴar fillo"
A haka suka koma masaukinsu ƙarfe 2 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa kano.
Amarya Zahrah na bedroom ɗinta Feedy ta shigo ta ce "Wow Zahrah kinga Yaa Sheikh wlh sai da zuciyata ta buga, na jima banga mutum mai kwarjinin shi ba" Zahrah ta miƙe ta ce "Da gaske Yaa Sheikh ya shigo?" Surry dake shigowa ta ce "Ya shige wai ai, Mimi ta ce ki sakko yanzu Kinga your husband and groom's friends" jiki na rawa Zahrah ta miƙe ta saka babban mayafi kamar ta Allah tana mai rufe jikinta sosai sbd cikin jikinta daya fara tasawa. Yana zaune saman wata haɗaɗɗiyar kujera, yaci dakakkiyar shadda gezner fara tas sai ɗaukan idanu take, ya ɗora Ash ɗin Alkyabba mai adon ruwan zuma, yaci rawani kamar kullum fuskarsa mai ɗauke da saje da tarin ƙasumma wacce tai tsayi sosai ta sauka har ƙasan haɓarsa sai ɗaukan ido take.
Khalil cikin sarki, Umar-khan, Ishaq-Hakim. Sai Oga El-bashir dake can gefe sbd faÉ—an Your highness gaba É—aya sun saka kaya iri É—aya,familyn kowa na ji da kansa wajan kyau.
Zahrah ana karairaya sbd ganin miji ɗaya tamkar da dubu acikin ƙawaye ta kere kowa aka ƙarasa kujerar da Yaa Sheikh yake, cikin ƙasa da murya ta ce.
"Your wlcm My Excellency" idan kujerar da yake kai ta motsa to Yaa Sheikh ya motsa gaba É—aya hankalinsa baya kanta, barcin dake addabar shi yake son yaje ya rage wanda ya saba yinsa kullum.
Kamar wanda aka tsikara haka ya miƙe tare da barin parlourn, Surry tai Shu'umin murmushi, Zahrah kuma tabi bayan Yaa Sheikh kamar wata jela.
Halisa ce ke kuka kamar ranta zai fita itama Dada idanunta ya cika da hawaye amma bata son tai kuka sbd kada ta karya Jaririyar zuciyar da ƴarta Halisa. "Dada dan Allah kada ki barsu su tafi dani, bana son barinki" Surry dake riƙe da kayan Halisa a wata babbar jaka data zuba mata tai murmushi ta ce "Haba Halisa, ai za a iya kawo ki wajan Dadar duk sanda kike so, kuma za a bawa Dada waya ku dinga hira" ita dai kuka kawai take farar fuskarta tai jajir. Surry ta ƙara cewa "Ba lokaci mu ake jira" sai lokacin Dada ta sauke numfashi ta ce "Halisa ki kama kanki, ki rage surutu da tsiwa, idan kika zaluncin yarinyar data taimaki rayuwata sam ban yafe miki ba, duk abin da tace kiyi mata kiyi ba musu ki ɗauke ta tamkar uwa, kuje Allah ya yi miki Albarka Insha Allah zaki Albarka zaki zama abar kwatance burukanki zasu cika, zamu zauna zaman jiran dawowarki nida Shatu" Halisa ta ƙanƙame Data sai Ajjiyar zuciya take saukewa ji take kamar ta rabu da ita kenan rabuwa ta har abada. Da ƙyar Surry ta zame Halisa daga jikin Dada suka shiga mota kai tsaye suka nufi gidan su Zahrah lokacin ana ta zuba shirin tafiya airport. Surry ta rasa yadda zata shiga ta Halisa sai kawai ta ɗakko wani liƙab ta kalleta ta ce "Maza saka wannan a fuskar ki kada wasu su gani" tana shassheƙar kuka ta ce "Ban iya ba" Surry ta ja tsaki tare da kama fuskar Halisa ta ɗaura mata Liƙab ɗin. Surry na tafe tana binta a baya tamkar munafuka ita duk liƙab ɗin ya dameta. Karon da taci da mutum ya sa cikin masifa ta ɗago ta ce "Aradu ba zan yarda ba sai na rama....," Yawun bakinta ya ƙafe lokacin da idanunta ya sauka akan fuskar Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu, jikinta na rawa haka ma laɓɓanta ta ce "Balarabe kai ne..." Ta faɗa tana ƙoƙarin cire liƙab ɗin fuskar daidai lokacin Saif-wazir ya ƙarasu wajan tare da Abba Hakimi...