← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 55

Sashe 31

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Misalin 4:45 manyan motocin da suka ɗakko dangin amarya daga airport suka shiga parking a harabar gidan Mother. Wasu ƴan uwan Zahrah da yayar mahaifiyarta da ƙanwar mahaifiyarta sune suka kamo Zahrah da aka rufe mata fuska zuwa cikin gidan sauran friends suka bi bayansu. A parlour akai musu masauƙi su gaisa da dangin miji kafin a basu masauki. Jadda dake zaune ta ce "Wai ina matar Gadangar ne sai wasu yamutsastsun fuskoki nake gani?" Ladidi ta ce "Gata nan Zahrah buɗe fuskarki ai miki bayanin dangin miji" Mother dai na zaune hankalinta na can waje guda sai kaɗa ƙafa take.
Dr A'isha ma na zaune taci uban kwalliya kana ganinta kasan ba talauci inda take, Yaya Halima ma haka, sai Momi tare da Æ´an uwan father, da matar Uncle Haroon.
"A meye haka? Alsulhu khair buÉ—e fuskar uban kowa ya gani"
"Ai Hajiya kin san amare da kunya" Jadda ta ce "kaji masifa ko? Waye sa dake wace ke? daga gidan wa zuwa ina?" Ladidi tai shiru amma Jadda ta fara ƙular da ita.
"Muhammadur Rasulullah s.a.w wannan ai uwa aka aura Aliyu ba mata ba? Gidan ubawa Aliyu zai kai É—irkekiyyar matar nan ni kai na ta kusa haifata yau na shiga uku da gaske wannan ce matar Malam É—in?" Jadda ta faÉ—a bayan ta saka hannu ta buÉ—e fuskar Zahrah. Surry na gefe tana danne dariyar dake ranta.
"Maryam zo kiga abin al'ajabi yoo Allah na tuba ko ke ai kinfi matar malam kyan gani? Allah sarki Gadanga an haÉ—aka da uwar mata" sai kuma ta fashe da kuka sosai ta ce "Innalillahi ashe har gashin doki take saka zunubi babba" ta saka hannu ta kama hannun Zahrah ta ce "Wanne tsinannen abu ne wannan kuma?" Ta faÉ—a tana duba farcen hannun Zahrah.
"Haba Hajiya wannan abun duk na mene? Ya daga kawo yarinyar sai cin mutunci?" Jadda ta miƙe ta nufi kan me maganar ta dungure mata kai ta ce "Algunguma ai duk duniya an gama cutar Malam an haɗa shi da arniyya" "Arniyya wacce ira kuma Hajiya?" Ladidi ta faɗa rai ɓace. Jadda ta kunce ɗan kwalin kanta tare dacin ɗamara ta ce "Arniyya ƙatuwa ma, mene bambancin su? ga tafkeken zunubi ba tausayi ba komai aka cirewa doki gashin shi aka saka mata, gata narkekiyya mai idanu a tsakar kai, gashi ta wani ɗashe kamar mace mai shigar sabon ciki Innalillahi masifa ta saukarwa Malam" gaban Zahrah ya faɗi tai saurin rufe fuskarta.
Dr A'isha ta fashe da dry wacce tun ɗazo take danne ta. Yaya Halima girgiza kai kawai take kafin ta ce "Kuyi haƙuri don Allah muke ga masauƙi can" Mother hankalinta na kan Danejo wacce take ɗan ɗaga liƙab ɗin fuskarta tana leƙewa da sun haɗa idanu da mother sai ta mayar ta rufe.
Babu wanda Jadda bata ciwa mutumcin ba kafin su bar wajan. Mamaki ya kama Ladidi ganin uwar mijin ta Zahrah ci kanku ba ta ce ba. Kwanan su biyu suka koma Yola aka bar Zahrah tare da Halisa.
Yaa Sheikh ne durƙushe a gaban Abba Hakimi da Uncle Haroon sai Uncle Bashir ga Mother da Yaya Halima da kuma Momi matar Abba Hakimi. "Ina magana kayi shiru Aliyu?" Abba Hakimi ya faɗa cikin sassauta murya. Yaa Sheikh ya ɗago kan idanunsa ya sauka akan yarinyar da ake nuna masa, ya ƙara duban Halisa da kyau sai yanzu yai mata cikakken kalo ya mai da idanunsa kan Abba Hakimi ya ce.
"Wace? kamar ban waye ta ba?" Uncle Haroon yai murmushi yana jinjina halin Yaa Sheikh. Abba Hakimi ya ce "Amma kasan Rugar Bello? Ka kuma san Arɗon rugar ka gane abin ya faru,ka kuma shaida zoben hannunta?" Yaa Sheikh ya ɗan kallin kyakkyawan hannun Danejo wanda yake maƙale da zoben da yake so har ransa nan take ransa ya ɓaci, a lokacin ya tuna everything ya shanye mmkin kamannin da yake gani a fuskar yarinyar, shi kam a rayuwa ko zai so mace ai banda ƴar cikinsa wannan gwaliliyyar yarinyar bata shige raino ba, ita za a kalla ace wai matarsa? Shi kam ya zai yi da mata biyu ba?. Yai shiru yaƙi bada damar da za a karanci halin da zuciyarsa ke ciki. Uncle Bashir ya ce "Da alama ya fahimta" Abba Hakimi ya ce "Halisa maza je aikyan yayar taki kada taga kin daɗe" ta miƙe da sauri domin daman a takure take Yaa Sheikh duk ya firgitar da ita. Abba Hakimi ya ce.
"Ba wasa muka zauna yi ba, jibi zaka shige Madina kafin nan kana son yarinyar nan ko baka son ta?" Yaa Sheikh yai shiru ya kasa fahimtar abin da suke nufi dashi, shi kam duk ranar da ya ce yana son mace ai sai ya yi azumin kaffara shi ya sa har abada ba zai taɓa cewa yana son wata ba.
Ya girgiza kai a hankali "Baka son ta?" Cewar Uncle Haroon. Bai kalli Uncle Haroon ba ya kalli Abba Hakimi. Abba Hakimi ya gyara zama yana sakin murmushi ya ce "Ka shirya sakinta? baka san me gobe zata haifar ba?" Yaa Sheikh ya riƙe hannunsa da kyau yana girgiza kansa harshen shi na harɗewa ya ɗan motsa ƙafarsa ɗaya cikin In-ina ya ce "Ha...hhh...har... Har abada ba ba ba zan zan so ta ba"

_IDAN BA KE it's paid book ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616..... Isn't free if you read for free🤷🏾‍♀️_
Chapter 31 · 0% Book details