Sashe 37
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"Ikon Allah daga aure sai haihuwa, Maimoon kam ai da sauran ta" ya ƙara shafa kai idanunsa akan Maimoon dake tura masa baki.
"To Allah ya tsare, a gaida Oum Juwairah" ya miƙe yana faɗin "za taji ai tana gidan Abba Hakimi" kafin Mother tai magana idanun Khalil ya sauka akan yatsun Halisa da mmkin yake kallon Zoben dake maƙale a yatsar zai magana El ya ce "Zan tafi ni dai" ya ce "kafi jirgin sama tashi" Halisa ta kalli El suka haɗa idanu sun jima suna kallon juna kafin tai ƙasa da kanta, tun jiya da suka je visa ta daina walwala taƙi kula kowa surutun ya rago sosai.
El-bashir ya fita Khalil ya ce "Ƴar tsuhuwa Maimunatu zo ki kaiwa Matar Yaa Sheikh gift ɗinta" ta miƙe kafin ta ƙarasa yayi waje, tana zuwa corridor taji an jawota zuwa jikin mutum, a tsorace ta buɗe baki zatai ihu Khalil ya yi saurin rufe bakin ya ce "Haba Amaryata yaushe za mu yi auren ne?" Ta ce "Allah ya sauwaƙe na auri me mata ni ban so" ya ce "Ni kuma na miki al'ƙawarin wallahi sai kin aureni na haɗa mata biyu a cikin masarauta" tai masa shiru, tun Maimoon na ƙarama yake mutuwar son yarinyar. Ya ɗan ƙara matseta a jikinsa daidai kunnanta ya ce "I love you" yana faɗin hakan ya saketa yana damƙa wani box ya ce "For our In-law, and this na ki ne" ya ƙara damƙa mata wani box ɗin ya juya da sauri tare da ficewa.
Washegari gari da safe Yaa Sheikh ne yake fitowa a hankali daga part ɗin sa, yana sanye da jallabiya fara tas ƙafarsa sanye cikin slippers, hannunsa goye a bayansa ya ɗan tsaya a parlourn sbd shiru da yaji juyawa ya yi idanunsa ya sauka akanta tana ƙawance akan duguwar kujera ta kifa kanta a hannunta kamar mai barci, jar rigar dake jikinta ta ƙara fidda tsarin jikinta, madaidaitan hips ɗinta sun bayyana a fili ya ɗauke idanu yana ya mutsa fuska, remote ya ɗauka tare da kunna karatun Alkur'ani ya danna ƙara ya cika gidan. A firgice Halisa ta miƙe tsaye jikinta duk rawa yake, jajayen idanun da kusan kwana biyu suka ƙi dawowa dade ta buɗe su akan Yaa Sheikh dake zaune akan kujera yana ɗan jan gemunsa. Ba tare da ta ce komai ba sbd kanta dake juyawa da sauri ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga cikin parlourn wacce kai tsaye kuma zata kaita har waje bakin hanya, Allah Allah take ta fita sbd karatun dake gigita mata lissafi kamar zai fasa kanta.
Tana zuwa daidai inda yake zata gilma ta shige ya sanya farin hannunsa mai laushi ya damƙota tare da dawo da ita baya...
Paid book
It's 500
Via 08119237616