← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 55

Sashe 36

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

_IDAN BA KE it's paid book... ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616. If you read for free😂🤷🏾‍♀️_

Umar-khan ya katse mata tunani da faɗin "Ki shiga muje" Zahrah ta ɗan basar tare da faɗin "Dake ban kula da kyau bane, amma ita me za ta je yi?" Ta tambaya idanunta akan Halisa wacce wayar Umar-khan ke hannunta sai latsa ko'ina take ba tare data san ta kanta ba. Umar-khan ya ce "Ayya ko kin manta Glasses ɗin naki ne, ita za ai mata visa ne" baƙin cikin maganar da umar-khan ya yarfa mata ya sanya ta kasa cewa komai ta shiga cikin motar tana sauke numfashi sbd ƙamshin Roja data shaƙa ga daddaɗan freshener dake tashi a motar.
Tana shiga Umar-khan shi ma ya shiga a hankali ya yi wa motar key sbd Yaa Sheikh baya son gudu da yawa, gatekeeper ya buɗe gate suka nufi wajan da za ai photo a haɗa musu visa. Bayan sun yi nisa akan titi Umar-khan ya juya ya kalli Halisa ya ce "Madam idan kika latata mini waya mijinki zai biya" Zahrah ta ɗago kai tare da duban saitin Umar-khan, bata fahimcin zancen ba domin ita ta ɗauka waya yake. Halisa ta buɗe fararen daidaiton haƙoranta masu kyau ta ce "To ai baya da kuɗi"
"Injiwa?" Umar-khan ya tambaya idanunsa akan titi, ta ɗan turo baki tare da watsa hannu alamar bata sani ba, ya girgiza kai ya ce "Shi ke da kuɗi, hakan ne ma ya sa ban ƙwace wayata ba, albarkacin ki sai a siya mini iphone 13max pro Matar Malam na makka da madina" taja lulu eye's ɗinta lumshe wanda hakan ya zama jiki a gareta, magana zarar bunu cikin rashin sani da kuma sabo da surutu yasa Halisa faɗin.
"Kai ma kasan ayi mini aure ne? Ko na faÉ—a maka yanzu" Umar-khan ya tuntsire da dariya sosai yana faÉ—in "Ina zan sani Æ´ar fillo? Kuma......,"

Yaa Sheikh da tun ɗazo idanunsa yake a rufe ya buɗe su a hankali kai tsaye ganinsa ya sauka akan ƙaramin bakinta wanda yake motsawa a hankali ta cikin madubin motar. Yaa Sheikh ya ɗauke idanunsa da sauri yana mai ɗan dafe kai cikin nutsuwa da kamewa wacce ta zauna a jikinsa ya buɗe baki da ƙyar ya ce.
"Ka kula, Umar-khan"
"Ok Yaa Lee" cewar Umar-khan with so much respect. Zahrah ta matsa kaɗan kusa da Yaa Sheikh tare da ɗora hannunta a saman na shi. "Asstagafirullah, Allah na tuba" ya furta cikin ranshi a zahiri bai motsa ba, sai ma rufe idanunsa da ya yi kamar mai barci. Zahrah taja gemunsa wanda yake matuƙar ɗaukan hankalinta ta ce "I love you My Excellency" baki ta miƙa zata sumbaci gefen fuskar shi, tari ya turnuƙe Halisa a kiɗime Umar-khan ya ƙara slow da driving ɗin ya ce.
"Sannu mene ya sameki, are you sick? Baki da lafiya ne?" Ganin tarin ya kasa tsayawa yasa Umar-khan faÉ—in "Yaa Sheikh ko zaka taimaka mata da ruwan wajanka, babu raguwar a motar" bai É—ago ba, ba kuma zakai tunanin da shi ake maganar ba..
"Sannu, sannu" ya ƙara jerawa Halisa cike da tausayi. Yana driving ya kalli Yaa Sheikh ta madubi da kuma Zahrah wacce takaicin Halisa ya cika ta duk ta hana su sakat tasu a lokaci na farko ta bawa Yaa Sheikh ɗin kyakkyawar sumbata wacce zata ruguza shi tun yanzu, tasan ba lallai ya iya riƙe kansa ba, dole ya zo gareta.
Umar ya É—auke idanunsa yana faÉ—in "Yaa Sheikh Please ta wahala da yawa" ya ajjiye carbin hannunsa tare da É—ago kansa kamar mai nazari ya shiga kallon Umar-khan, not looking at her place ya kame kansa murya kamar anyi forcing nasa na magana ya ce..
"Stop the car" Yasan idan har Yaa Sheikh ya buɗe baki ya yi magana to yana nufin abin da ya faɗa ne har cikin ran shi a hankali ya yi parking motar zuwa gefen titi. Zahrah ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Daman bai kamata mu shiga mota ɗaya dasu ba, ga wannan shegiyar yarinyar ƴar fillo, kawai su nemi abin hawa i can drive us kaji My Excellency" ya ɗan kalleta kaɗan ta wani kashe masa idanu tana shirin kama hannun shi ya fita daga cikin motar, yana fitowa ya shiga takawa a gefen titin hannunsa goye a bayansa, ganin yadda ya tsaya waje guda kansa a ƙasa yada Umar-khan fita yana tunanin ko lafiya? Ya nufi wajan shi tare da faɗin "Yaa Lee lafiya?" Ya ɗago kai ya kalli Umar-khan, mamaki ya kama Umar ganin yadda goshin Yaa Sheikh yake fitar da zufa ya jiƙe sosai da gumi.
Bai magana ba ya miƙa hannunsa tare da amsar key car ɗin hannun Umar-khan, da hannu ya nunawa Umar-khan bayan motar alamar ya shiga ciki ya zauna, mamaki ya kashe Umar a tsaye yau Yaa Sheikh zai yi driving ɗin mutane a mota bana shi ɗaya ba? Me hakan yake nufi.
Zahrah dake bayan mota tana jiran ace Halisa ta fita ita kuma ta dawo gaba ita da mijinta su tafi iya su biyu sai gani tayi Umar-khan ya buɗe bayan motar ya shigo, mamakin sauyin al'amarin cikin ƙaramin lokaci ya hanata magana.
Yaa Sheikh ya sanya tattausan farin hannunsa mai ɗauke da suma lub ya buɗe murfin gaban motar, ƙafarsa ta hannun dama ya fara shigarwa kana ya shiga ya zauna baki ɗaya.
"Ban gane wani ƙaton namijin ya zauna dani ba, bayan ina matarka?" Babu wanda ya bata amsa sai ji tayi ya yi wa motar key. Murmushi kawai Umar ya yi yana ayyana wani abu a ran shi..
Yaa Sheikh ya yi tunanin zata cika shi da surutu kamar yadda ta cika Umar-khan da hayaniya mara tushe, amma sai yaga saɓanin haka bawai kallonta ya yi ba, ya fahimci hakanne ta madubin motar.
Kanta a ƙasa idanunta ya yi masifar jaaa jikinta na ɗan rawa a hankali, saukar sautin ƙira'ar daya cika motar har ya kawo zuwa kunnenta yasa ta sauke numfashi mai ƙarfi jikinta ya saki kafin su ƙarasa barci ya ɗauke ta sai ajjiyar zuciya take saukewa.
Bayan magrib Mother na zaune a parlour ita da Jadda. Jadda ta kaɗa ƙafa ta ce "Amma dai Allah ya isa, an munafurce ni ko waye kuma yaje shi da Allah, shi yasa yadda zai yi dashi danni ba zan iya komai ba" "lafiya dai Jadda?" A fusace Jadda ta ce "Ina batun lafiya Maryam? Ashe haka aka haɗawa Uwar matar can lefe hadda na Allah ya isa fa? Ni dai babu ruwana na kusa zare hannuna daga al'amarin Aliyu ko na ɗaga masa nonon kawai tun da nayi niyya" Mother tai murmushi kawai tana jiran zuwan Maimoon.
Zahrah ta ƙarasu parlourn sanye da ƙaton hijabi irin ta Allah ɗin nan nace, ta zauna tana faɗin "Sannu da hutawa Mother" a taƙaice ta ce "Yawwa" ta juya kan Jadda wacce ta haɗe rai sosai ta ce "Barka da gida" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce "Allah ya isa, Allah ya isa wallahi ban yafe ba" Jadda ta faɗa tana kallon Mother tare da fashewa da kuka ta ce "To me nayi mata da zata gaishe ni? Sbd Allah ina ruwanta dani ko nace ina buƙatar gaisuwarta" Zahrah bata ƙara bi takan Jadda ba ta kalli Mother tana sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Daman zan mayar da Yarinyar nan ne gida" Mother ta kalli Maimoon dake shigowa tana faɗin "Wacce yarinya?" Zahrah cike da nuna cewa tafi kowa iya ladabi ta ce "Ƴar fillo, zan tura ta gida" Jadda ta miƙe ta ce "Wannan farar yarinyar kyakkyawa mai zubin labarawa kamar ita tai kanta? Idan kin isa Allah ya tsine" Mother tai murmushi ta ce "Me ya sa?" Zahrah tai ƙasa da kai ta ce "Daman Mimi tace na dawo da ita gida, da ƙyar aka yarda aka bani ita kuma tana karatu" Mother ta karkaɗa ƙafa ba tare da ta ce komai ba ta danna wayarta babu jimawa aka ɗaga wayar ta ce "Umar-khan, kayi waya da mutananku na can Madina, a fara nemawa Halisa gurbin karatu a matakin ajin farko na secondary" gaban Zahrah ya faɗi, ganin how smart she had. Bayan gama wayar Mother ta ce "kada ki damu Zahrah, I'll talk to your mom, ki fara shirye-shiryen tafiya" ta miƙe tana faɗin "Na gode Mother" da sauri ta shige part ɗinta.
Tana zuwa ta rufe ƙofa tare da cire hijabin jikinta inners ne kawai a jikinta cikin faɗa ta ɗaga wayarta ta ce "haba Deen wai kai wanne irin maye ne?" Deen dake cikin wayar ya ce "Muna vedio call kika tafi kin barni cikin wani hali Beb" cikin ɗaga murya ta ce "Jarbabbe duk kai ka koya mini jaraba kwana nake bana barci, nifa batun tafiya da yarinyar nan ne na fasa,ina hangowa kai na matsala gaba ɗaya ji nake kamar wani abu zai faru idan na tafi da ita" Deen ya numfasa ta wayar yana faɗin.
"Ya kukai kuma me kike so ayi?" Ta faÉ—a masa duk yadda sukai da Mother ya ce "Uhm Sirikarki Educated ce kuma Barrister, ta fiki tunani da hankali idan kina wannan haukan da wuri za a gano shirinmu, dole ki yafe É—an cikin ki a gidan Yaa Sheikh, shi ne zai bamu damar cimma burinmu ya zama dole ki samu kusanci dashi ina nufin ki samu mu'amalar aure da shi, hakan shi ne hanyar farko, ai ana haihuwa bakwaini ki san duk yadda kikai kina zuwa Madina ku samu daidaito Zahrah, kece madafin cimma burina na faÉ—a miki irin cin amana da zaluntar da akai mini" ta sauke numfashi tare da ta ce.
"It's ok Deen, na maka al'ƙawarin ƙwato maka hakƙin ka, ina son ka, burina ka tsaya dani banda wata macen" ya yi murmushi ta wayar ya ce.
"Zahrah kenan, kina so na kullum kike cewa, amma son da kikewa Yaa Sheikh yafi son da ki ke mini, duk da hakan me ya sa kika amince zaki cutar da shi bayan kina son shi?".
Zahrah ta ce "kada ka damu wannan sirri na ne, sunna or later zaka sani, Yaa Sheikh manufa ne, kai kuma makami ko wanne nada amfani, amma dole muyi wani abu akan Halisa" ya ja tsaki a ran shi sam bai ga abin damuwa akan wata Halisa ba.
"A kashe ta? Ko kuma a haukata ta?". Zahrah ta ce "Hauka kuma, zan yi tunani akan haka, muje vedio call na nuna maka wani abu mai yaji" dry ya yi ya ce "Zahrah bana son ganin wannan shafaffen ƙirjin naki, wanda yake kwance har ciki serious tun kafin Yaa Sheikh yasan wace ke ya kamata ki nemi magani" maganar Deen ta daki zuciyar Zahrah ta kashe wayar rai ɓace.
Khalil ya ce "Mother daman zuwa nayi nai miki sallama, yanzu zamu tafi airport" ta ce "To sai yaushe kuma" ya shafa kai ya ce "Ina tunanin sai bikin Maimoon ko idan matar Yaa Sheikh ta haihu".
Chapter 36 · 0% Book details