← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 55

Sashe 55

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

7:00 ya shigo gidan bayan ya biya ta wajan tsuntsayensa, daman yasan ba zai samu kowa a main parlour ba. Kai tsaye part É—insa ya nufa da mmki yake dubanta tana kwance saman prayer kar sai gyangyaÉ—i take. Ya nufeta bai ce komai ba taji an É—agata sama tayi saurin buÉ—e idanu suka kalli juna sai kawai tai murmushi mai kyau tana kwantar da kanta. Bayan ya sauketa saman bed ya ce.
"Sanyi sai kama ki, a daina kwanciya ƙasa" ta ɗaga masa kai tare da faɗin "To Abba makaranta fa?" Ya tsare ta da idanu kafin yai magana wayar shi ta gida ta fara ringing ya miƙe tsaye a hankali ya manna wayar a kunnansa. Umar-khan dake kan layi ya ce.
"Barka da safiya Yaa Lee, ya mai jiki? Ummul na neman iso na shigowa sashin naka" "Uhm" ya ce yana ajjiye wayar. Babu jimawa Ummul ta shigo hannunta É—auke da babban tray.
"Barka da safiya, ya jikin nata?" Yana zama kan kujera tare da naɗe ƙafarsa ya ce.
"Mun tashi lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah, Ya jikin ƴar Abba" Halisa tana daga kwancan ta ce "Naji sauƙi Ummul, tambayi Abba kiji shi ne ya ɗaukeni yanzu kuma a jikinsa na kwana" kamar ƙasa ta tsage ta shiga haka Ummul taji kunyar Yaa Sheikh ta kamata Halisa ta ƙara cewa.
"Ummul Abbana É—an gayo ne ba kiji bakinsa ba..."
"Ya isa haka, yau naga takai ne ni Ummul" Halisa ta juya za taiwa Yaa Sheikh magana amma ko inuwarsa babu a bedroom da alama ya daɗe ta ficewa tun da yaji abin kunyar da take neman haɗa shi da ita. Ummul sam batai wani mmki ba, ita juriya da haƙurin Yaa Sheikh kawai take gani.
"Ƴar Abba ba komai ake faɗa ba, shi aure sirri ne, duk abin ya faru ki barshi a ranki, kinji?" Ta ɗaga mata ta ce "maza sha tea kinji?" Ta maƙale kafaɗa ta ce "Modibbona zai ban kije kawai Ummul, kuma me ya sa ki ka daina cewa matar malam?" Ummul ta ce.
"Because he's no longer your husband" tana faÉ—in haka ta fita. Ita kuma Halisa sam bata gane ba. Tana fita Yaa Sheikh ya fito daga bathroom suna haÉ—a ido da Halisa ya watsa mata harara ita dry ya bata ma.
Zahrah na tsaye ta kafe Ummul da idanu tana tirketa da manyan tambayoyi. "Ina Æ´ar aikina take, ya zama last question da zan miki" Ummul ta ce. "Bata jin daÉ—i, a part É—ina ta kwana" Zahrah tai shiru sai kuma ta ce "Muje akwai aikin da za tayi mini yanzu?" Ummul ta ce "Bata lafiya fa?" A fusace Zahrah ta ce "And so what? Ke rashin lafiyarta ya dama" Ummul ta É—auke ta ce.
"To Umar-khan ya tafi kai ta asibiti" yaja tsaki tare da juyawa ta ce "Bari naje wajan Yaa Sheikh É—in naji wanda ya bada lasisin yiwa Æ´ar fillo abu ba tare da izinina ba" Ummul tai bedroom É—inta da sauri ta kira Umar-khan ta ce.
"Ka kira Yaa Sheikh yanzu ga matarsa Zahrah nan zuwa, kasan Halisa na wajansa" tana faÉ—in hakan ta kashe kiran.
Kiran telephone line ya tsayar da Zahrah daga tafiya part ɗin Yaa Sheikh, ta ɗaga kiran tare da cewa "Hello" Jadda dake bisa layi ta ce "Waye ne za a fasa mini kunne kamar yaƙi?" Zahrah taja tsaki a ranta ta ce "Matar Aliyu mana?" Jadda ta zabga Salati ta ce "Yaushe Gadanga ya yi aure kuma?" Zahrah ranta ya ɓaci ta ce "matarsa Zahrah" Jadda ta ce "Uban meye kuma Zahra? A to Allah ya isa ban yafe ba maganar da nayi dake, maza maza mutum nake nema bake ba don Allah, kije kiji da Iyaye abu a kwance kamar tawul ɗin wankan mai jego" wani kyakkyawan tsaki Zahrah ta ja. Tamkar Jadda ta fasa wayar haka tayi ta ce "Uwarki ki kaiwa tsaki, ai sai yanzu na tabbatar Gadanga bai aure mace ba, mai siffa irin ta fir'auna da ƙaruna, baki kamar maliya tayi ambaliya" kashe wayar Zahrah tayi baki ɗaya tsanar mata ya ƙara zama daram a zuciyarta.
Ko sallama ba tayi ba a haka ta shiga part ɗin Yaa Sheikh, a tsaye ta gansa ya baza Alkyabba sai ƙamshi yake zabgawa wani irin kyau ya yi mata wanda bata taɓa ganinsa ba, ya ƙara girma da faɗi.
Ta sauya tafiya tana kaÉ—a jiki cike da kissa ta nufesa tana zuwa ta ce.
"My Excellency, you look good kayi kyau sosai" ta rungumesa ta ce "I love you husband" ya buɗe ido yasan daman babu gaisuwa a tsarinta. "Yaushe zaka bani damar zuwa sashinka na tayaka barci? Na fara gajiya kawaici na ya ƙare ina buƙatar mijina" sai a lokacin ya kalleta sosai a hankali ya ce "Sanda ki ka shirya" zata sumbaci bakinsa taji kamar wani abu yana yi mata yawo a jiki ta ɗan motsa ta ce "Uhm daman nace a daina fita da ƴar aikina ba tare dana sani ba, kuma idan da hali ta kwashe kayan zuwa sashen masu aikin gidan nan" ta zabura sbd abin da yake ƙara bin jikinta gudun kada ta bata kanta a gaban Yaa Sheikh tayi saurin cewa "I'll be back" ya lumshe idanun tare da buɗewa tai saurin ficewa.
Wani irin fisgar numfashi ya yi jin yadda ta riƙesa sosai ta baya, gaba ɗaya ta jiƙa masa bayan riga ta bakinta. Ya saka tattausan hannunsa tare da fito da ita waje daga cikin Alkyabbar jikinsa.
Ya dubeta ya kalli hannunta brush ne wanda ta wanke baki ta tura baki ta ce.
"Ji nayi tana cewa zata kwana dakai fa Abba shi ya sa" wato ita ta kuri Zahrah?.
Ya juya zuwa bedroom har lokacin jikinta baƙwari sosai suna zuwa taga ya jawo Injection yana zuƙar ruwa gabanta ya faɗi sosai. "Allah sarki Abbana waye babu lafiya kuma?" Da ace dry halinsa ne babu abin da zai hana shi yi ya juya ya ce. "Ƴar fillo" ta haɗiye yawo ta ce "A'a wallahi lafiya nake,don girman Allah Abba kada kayi mini don soyayyarka da Annabi wlh banso" ganin ta gaske yi mata zai ta kwasa zata gudu ya damƙota tare da zama da ita akan cinyarsa ya ce.
"Shhhhh, ina gaisuwata?" Ya faɗa yana ajjiye allurar gefe ɗaya. Ta sauke numfashi ta ce "Naji tsoro ashe bani za aiwa ba" ya dai bita da idanu a hankali ta saƙalo wuyansa tare da ɗora bakinsa a kumatunsa, ta sakar masa kiss ya saka hannunsa a bayanta tare da yin ƙasa da trousers ɗin jikinta, idanunsa cikin nata a haka ya ɗauki Injection. Halisa tai murmushi tana ƙara yi masa kiss a kumatu shi kuma ya saita Injection ɗin a jikinta. A hankali ta dawo bakinsa sai kuma ta fasa ta ɗaga idanu tare da kallon Yaa Sheikh ta ce "Abbana ina son ka" a karo na farko ya sakar mata murmushi wanda yasa ta zuba masa idanu kamar bata taɓa ganinsa ba, ya sumbaci goshinta ya ce.
"I na... Ina.." tai dry ta ce "Yawwa Modibbona ni ma kace kana so na" ya ɗora tsinin allurar sosai a jikinta ya ce "Ina.. ina son" bai ƙarasa ba ta ce "Ina son k....," wani ihu ta fasa daidai lokacin daya tsira mata tana ƙoƙarin sakin kuka ya kame bakin kukan da nasa bakin ya rungometa sosai a jikinsa...

Paid book
500
08119237616
Allah ya nuna mana Monday ai weekend lfy🥱
Chapter 55 · 0% Book details