Sashe 20
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sheikh Aliyu haydar na kwance saman makaken gadonsa idanunsa akan screen ɗin laptop ɗinsa yana sauraran abin da ake faɗa ta cikin laptop ɗin. Can dai ya ja tsaki ya girgiza kai, speaking calmly ya ce "Ni ni niii da dddddd dama zaka zaka zaka sauya labarin nan naka Khalil, in anyway banga amm am am amfaninsa ba..." Dry sosai wanda aka kira da Khalil ya yi ganin yadda Sheikh ke runtse idanunsa yana buga kai duk dan ya kare kansa "To ai ni yana da amfani a wajena tun da abin da ya shafi Sheikh Aliyu haydar Aliyu ai shafi Khalil Ahmad Sarki, look Sheikh don Allah cire son zuciya ka faɗa mini mai mata sukai maka? Let me know" Sheikh ya shafa lallausan gashin kansa wanda yake kwance gwanin sha'awa, cikin son cire damuwar father a ransa ya dage yake hira da Khalil duk da yana shan wahalar magana ya jima bai magana mai tsayin haka ba, idanunsa lumshe ya ce "kakaka....ka kasan me?" Sheikh ya faɗa yana buga kansa jikin pillow yana riƙe ɗaya hannunsa sbd In-ina. Kallonsa kawai Khalil yake yana jiran jin abin da Sheikh ɗin zai faɗa, a wahale cikin In-ina wacce yake son ya saba magana da ita ya mirgina kaɗan yana riƙe kansa da hannu bibbiyu ya ce "man ta ta manta kawai, ya ya yaushe za za kazo?" Murmushi Khalil ya yi cike da ƙaunar Sheikh Aliyu haydar ya ce "Zamu zo da mai martaba wajan Hakimi, I think I will spend my two weeks vacation with you in Kano" jinjina kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba. "You are just afraid of women because you see yourself as a Sheikh, women are the happiness of a man, try and see" Girgiza kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kashe vedio call ɗin.
Umar-khan ne ke driving a hankali idanunsa akan titi amma hankalinsu na kan Sheikh dake manyan mota cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya É—ora golden É—in Alkyabba sai rawanin daya Æ™arawa fuskarsa kyau da haiba ya yi wani irin kyau kamar Balarabe Æ™amshin Roja ya cika motar sosai. Yana ki shingiÉ—e a bayan motar tunani yadda zai sauya ya koma kamar yadda father yake buÆ™ata, a haka suka Æ™arasa Wani Restaurant mai kyau da tsari mara hayaniya, Umar-khan ya yi parking kasancewar fitar sirri ce yasa babu wasu masu take masa baya, cikin sauri ya buÉ—e Sheikh mota a nutse ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da goya hannunsa a baya cikin kamala ya yi gaba Umar-khan na biye da shi zuwa cikin Restaurant É—in. Zama Sheikh ya yi tare da kallon mutanan da zasu tattauna dasu, bayan sun gaida Sheikh ya É—aga musu kai suka shiga nuna masa zanan bank É—in daya buÆ™ata na reshe uku, kaduna, Abuja, da Lagos. Baya cewa komai sai da Umar-khan suke tattaunawa gani ya yi zanan bai masa ba, domin babban bank yake so wanda ba a taÉ“a yin mai girman sa ba. Hakan ya sa ya amshi carbon paper da pen a nutse ya zana yadda yake so, zanan ya bawa ma'aikatan mamaki abin da basu sani ba, kaÉ—an kenan daga cikin baiwar Sheikh duk abin da ya sanya ransa yana gwadawa yake yi daidai. Sallama sukai bayan anyi musu transfer miliyoyin kuÉ—i domin fara aiki gadan-gadan. Æangaren Kamfanin sarrafa shinkafa ma tuni aiki ya yi nisa, ya yi ordern injina masu kyau daga Chaina. A gajiye ya dawo gida idanunsa na rufewa kansa ya sakarwa shower lokacin 1:30 ya saba barci tsakanin azahar zuwa sallar asr, fresh milk ya tsiyaya a cup tare da zuba honey ya sha kaÉ—an ya wanke baki, yana kwanciya barci ya É—auke shi daman ya riga daya saba.
Washegari ya kama weekend Sheikh bai san meke faruwa ba, sai daya farka yaji labarin tun 7 su Uncle Haroon da Abba Hakimi tare da Baffansa suka nufi garin Yola nema masa aure. Ko ajikinsa bai ɗauki auren matsayin wani abu, shi dai ya san ko farcen mace bai taɓa sha'awa ba balle ya birgensa. Da yamma su Abba Hakimi suka dawo cikin jin daɗin an basu auren Zahrah nan da sati mai kamawa za a ɗaura aure. Kasancewar yau Friday ne ya sanya Sheikh ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda fara tas da ita mai ɗinki jamper da babbar riga, bai sanya hula ba sai hirami daya saka a saman sumar kansa ya ɗauki zagayayyen abun nan na larabawa Black colour ya ɗora saman hiramin, shekarunsa suka bayyana a jikinsa, domin kowa ya kalli Sheikh Aliyu haydar ya san ba yaro bane, girma ya fara hawa jikinsa babu mamaki ya yi aure a same shi da yara biyar haka, shekaru 34 ba wasa bane ba. Kai tsaye babban masallacin juma'a ya nufa sai da ya yi huɗu ba sosai mai ratsa jiki akan tsaida sallah a lokacin ta, tunda duk In-inar Sheikh inda karatu zai yi yana farawa ake nemanta a rasa. Bayan idar da Sallah ya nufi zaga gidan marayu kamar yadda ya saɓa idan yana ƙasa, a hankali yake tafiya hannunsa goye a bayansa kansa a ƙasa fitowar su kenan daga gidan marayu zasu shiga mota yaje gida wajan Mother, kamar daga sama wata budurwa kyakkyawa ajin farko ta tsaya a gabansu da sauri Umar-khan da Saif-wazir suka sha gabanta tun kafin securities su ƙarasu bakinta na rawa ta ce "Don Allah ku barni nayi magana da shi, na jima ina son haɗuwa da shi" Umar-khan ya daka mata tsawa ya ce "Baya buƙatar ganin kowa, kuma a mu'amalar shi baya yi da mata ki nemi wani wajan" A nutse Sheikh ya dakata tare da juyawa idanunsa zuwa inda budurwar take, waro fararen idanunsa waje ya yi yana mamakin abin da ya haɗa shi da bayin Allan nan da suke bibiyar shi. Murmushi mai laushi ya yi ba tare daya bari kowa ya gansa ba, yana mai ƙarewar budurwar kallo musamman ƙafarta. "Ka taimaka mini daga yanzu ba zan sake zuwa inda yake ba" Umar-khan ya yi mata wani ban zan kallo ya ce "Ke ko mayya ce ke baki isa kije inda Sheikh yake ba, kunne masu ƙullawa mutane sharri ko?" Sosai taji zafin maganar Umar-khan sai kawai ta juya kamar zata kifa sbd sauri. Tana barin wajan Umar-khan ya dafe kansa Saif-wazir ya ce "Are you okay?" Ya ce "Kai na ke ciwo, zazzaɓi nake ji" Umar-khan ya faɗa bakinsa na rawa kafin kace wani abu wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Umar-khan. Girgiza kai kawai Sheikh ya yi domin ya san za a rina waya aiki Khan musayar yawo da aljani?.
Da sauri Hamma Yabi ya shigo bukkarsu hannunsu ɗauke da kuɗi ya kalli Danejo wacce take sumar kanta ya ce "shai Alhmd kuɗi shun samu gobe zan kai Dada asibitin burni" murmushi Danejo tayi wanda ya ƙara fidda kyanta na fili ta ce "Kai Allah abin gdy Dadata zata samu lafiya yau ba zan barci ba sbd farin ciki aradu" Hamma Yabi ya kalli Dada dake kwance kamar haka cikin farin ciki ya ce "Insha Allah, da sassafe sai burni" fita ya yi farin ciki ya cika zuciyar Danejo Dada zata tashi su koma yadda suke rayuwa a baya. Hamma yabi bai dawo ba sai dare riƙe da ƙullin buduri da ƙosai mai zafi wanda ake a can wajan gari. Sai dai ko zama bai ba suka fara jiyo harbi ta ko wanne waje alamar ƴan fashi ne suka shigo cikin Rugar Rome. "Bone Hamma harbi harbi....," Bata ƙarasa faɗa ba suka ji an shigo bukkarsu wani mutum mai riƙe da bindiga ya kalli Hamma Yabi yana faɗin "Kuɗi,kawo kuɗi bamu da lokaci" jikin Hamma Yabi na rawa ya ce "Ba kuɗi bamu da shi" mutumin ya yi wata dry sosai ya ce "Babu? idan na bincika na samu duk hukuncin dana ɗauka akan kai ka sani" yana faɗin hakan ya fara bincike bukkar daga can waje harbi ake ta ko wanne sashe, cikin rashin sa a mutumin yaga kuɗin da Hamma Yabi zai kai Dada asibiti "Aradun Allah kuɗin asibiti ne, kayi mini ka taimaka Dada zamu bawa lafiya.....," Harbin da akaiwa Hamma Yabi a ciki ya sanya ya fasa ƙara tare da faɗuwa ƙasa ihu Danejo ta fasa ganin yadda jini ke zuba a jikin Hamma Yabi tana ƙoƙarin zuwa inda yake mutumin ya ƙara sakarwa Hamma harbi a tsakiyar kansa......
Wannan littafin na kuɗi zaka samu book 1, 2 akan ₦500 daga farkon labarin har ƙarshe ka tura ta wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.
*🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Arewabooks@Nimcyluv_*