← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 55

Sashe 19

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

13.....
Mimi ta ce "baki son kishiya kuma? Ina ruwanki da wata kishiya?" Dady ya ɗaga hannu yana murmushi ya ce "Ni ma bana fatan Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya yi wa Zahrah kishiya,domin za a rage mini abin da nake tunani" cikin rashin fahimta Mimi ta ce "kamarya Alhaji?" "Ba sai kinji ba, ki shirya aurar da yarinyar ki cikin satin nan" ya faɗa yana miƙewa tsaye cikin jin daɗin amincewar da Zahrah ta yi.
Jikinta na rawa ta haura upstairs tana zuwa ɗakinta ta samu Surayyerh ciki daman bata tsaya a parlour ba sama ya shige ɗakin Zahran. "Wayyo daɗi kashe ni, na samu mijin da nake fata da burin samu cikin sauƙi" ta faɗa gado tana sakin ƙarar farin ciki. Surayyerh ta ce "Pardon? Ban fahimta?" Miƙewa Zahrah ta yi ta ce "C'mon yanzu Dady yake sanar mini za a haɗa aurena da Sheikh Aliyu" mamaki ya hana Surayyerh rufe baki sai da Zahrah ta saka hannu ta rufe mata baki, Surayyerh ta samu damar faɗin "Are you serious Zahrah? Gaskiya am happy for you daman kina son Sheikh?" Tayi fari da idanu irin na gogaggun matan nan ta ce "Fiye da yadda bakya zato, soyayyar Sheikh ta hanani aure, abin mamaki ban taɓa ganin shi a zahiri ba sai dai photo a wajan Dady ko idan yana tafsir, nasan shi ma bai sanni ba"

"Yanzu duk ba Wannan ba, ya ya zaki da cikin jikin ki tunda likita ya tabbatar ba zai zube ba? Gashi kuma aure ya zo babu shiri?" Zahrah ta ce "Kada ki damu da cikin zanyi auren, ko da haihuwa nayi sai nace bakwaini ne ai anayi" Surayyerh ta jinjina makircin Zahrah amma ta share ta ce "Idan kin ɓoye cikin ya zaki idan ya san ke ba budurwa ce ba?" "Oh! My God what exactly wrong with you Surayyerh ki ke neman yi mini baki? Ai ba zai sani bama ɗinki zanje ayi mini" Surayyerh ta ce "Uhm shi fa babban Malami ne You never lie to him Malamai sun san komai infact sun fi kowa iya soyayya kiyi tunani ki nemi mafita" share zan can Surayyerh Zahrah tayi a yanzu yadda za taga Sheikh Aliyu haydar Aliyu a zahiri shi ne burinta. Da magrib Surayyerh ta tafi gida akan gobe zata dawo domin fara shirye-shiryen haɗa events.
Tun a bakin parlour Surayyerh ta san akwai matsala tana shiga Umma ta kalleta sosai ta ce "Daga ina kike?" Turo baki tayi tana musmus da bakinta kamar mai zagi ta ce "Wai ke Umma zargina kike ne? Haba don Allah na fara gajiya ciki kike tsoro ko mene?" Umma mamaki ya kasheta a tsaye ta ce "Surayyerh ni mahaifiyar ki kike faɗawa haka sbd ina kare kiwon da Ubangiji ya bani?" "Wani irin kiwo kamar wata dabba Umma? Kawai takurawar taki ce ta yi yawa, ki barni da abin da yake damuna gashi duk iskanci Zahrah rana tsaka ta samu miji na kece raini wanda ba zan taɓa samun irinsa ba" jirin dake neman yadda Umma yasa ta nemi saman kujera ta zauna. Ubangiji ya gani kuma shi ne shaida tayi iya yinta ta fara gajiya tana ganin gaba gaba Surayyerh dokanta zatai ita kam wannan karatun bokon bai mata rana ba. Hawayen daya cika idanunta ta mayar sbd babu dacewar yiwa Surayyerh kuka sai ta sake lalacewa. Surayyerh ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗinta tunani ya yi mata yawa abin da bata tsammata ba a yanzu ya kawo mata farmaki.
A firgice Halisa Danejo Rome ya farka daga nauyayyen barcin daya ɗauke ta mai cike da mafarkai wanda bata taɓa yin kamarsa ba, me ya sa Balaraban nan ke zuwar mata cikin barci ne? Amma gaba ɗaya yadda ta gansa a daji ya bambanta a farki, na cikin mafarkinta yafi kyau da kamala nutsuwarsa da kamewar shi tafi bayyana, kwarjinin dana mafarkinta yake dashi na zahiri baya da shi, duk mutum ɗaya ne? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta shiru tayi cike da damuwa domin ta fara gajiya da mafarkinsa. Motsin da taji kusa da ita ya sanya ta juya idanuna ya sauka akan Dada wacce take sanƙame numfashi na fita da ƙurar ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa. "Na lalashe na shiga uku Dada jikin ne? Sannu Dadata zaki samu lafiya" ta faɗa hawaye na wanke mata fuska gaba ɗaya ta ƙara zama wata kala damuwar ciwon Dada ya sata gaba, gashi yanzu Hamma Yabi baya yini gida sbd neman kuɗin zuwa asibitin burni. Jigum tayi tana kallon yadda kumfa ke fita ta bakin Dadar amma bata san me zatai mata ba, bata da wanda zata kira a cikin bukkar. Shatu dake rakuɓe ta kalli Danejo ta ce "Dada mutuwa zatai ko?" Girgiza kai Danejo tayi ta ce "Waya faɗa miki? Babu inda Dada zata yafi ta barmu aradu muna tare da ita" wata ƙara da Dada tayi tana sanƙamewa ya sanya Shatu fashewa da kuka, da gudu kuma Halisa Danejo Rome tayi waje. Karo sukai da Hamma Yabi wando ya shigo hannunsa riƙe da ƙwayar magani daya amsu, ya riƙe Danejo da kyau wacce take ƙoƙarin fita daga hayyacinta. "Hande en boni, Danejo lalashewa ya sameka me ya samu Dada?" Gaba ɗaya ta rikice sai ƙanƙame hannun Hamma Yabi take ganin bata hayyacinta ya jata ciki yana zuwa ya kwantar da ita yana rufe mata fuska shiru tayi har lokacin cikinta bai bar rawa ba, domin gani take kamar Dada tabarta kenan ta mutu ta tafi. Ya girgiza yana komawa wajan Dada tare da ɗagata ya bata maganinsu ya shafa mata zuwa fuska da wuya Ajjiyar zuciya ta sauke tana buɗe idanunta, hannun Hamma Yabi ta kama da kyau tana son tambayar shi mene ya samu Halisarta amma ta kasa, a haka barci ya ɗauke ta cikin mayuyacin hali. Washegari kamar kullum Danejo ta tatsi nono a ƙwayar, tun kafin gari ya yi haske ta fita kiwo da shanunsu, sai da ta ɗauki awa uku ta dawo cikin sauri tana tafe tana kaɗa naggen bayan ta ɗaure su ko abinci bata ci ba ta nufi cikin burni kawai tsaye zuwa Abti America. Yadda taje haka ta dawo babu wanda ya sanya kuɗi ya sai nonon balle su samu na abinci, a wahale ta shiga Rugar idanunta na rufewa ta kafa baki a nonon wata nagge ta shiga sha sai da cikinta ya ɗago taja Ajjiyar zuciya tare da nufar bukkarsu.
Chapter 19 · 0% Book details