← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 55

Sashe 32

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yaa Sheikh ya faɗi hakan kai tsaye. Abba Hakimi ya ce "To kafin nan muyi wata game mana, idan kaci ni kuma nayi al'ƙawarin raba aurenku har abada, ka zauna kai ɗaya da ita Zahrah tunda ba a son Ƴar fillo" Mother ta juya ta kalli Yaa Sheikh kafin ta ce.
"Yanzu meye laifin yarinyar? ba tafi wacce aka haɗaka da ita ba? to a karo na farko zan faɗa maka zama da wannan babu fashi a wajanka Aliyu" Uncle Haroon ya ce "A'a Barrister labarin aure baza kici haka ba, ana yin aure dan farin ciki da kwanciyar hankali,idan ba yajin yarinyar a ran shi bai kamata a takura masa wajan zama da ita ba, zai iya amincewa bisa takurar kuma ya cutar da ita, a dai bi komai a hankali" Mother ta girgiza kai ta ce "Uncle Haroon ka rabu da Aliyu, tunda ya amince dana Zahrah zai amince da wannan ɗin ma sai ya tattara su tafi can Madina su ƙarata" Yaya Halima ta kalle su baki ɗaya kafin ta ce "duk ba Wannan ba, na tambayi Zahrah a sigar wasa cewa wannan ƙanwarta ce? Sai ta ce mini wai ƴar aiki aka samu mata, That's the position of a maid in Aliyu's house" Dr A'isha tai murmushi ta ce "Matar gida ko ƴar aiki? dama a ɗauke ni aikin gidan Aliyu naga yadda zaman zai kasance" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa a hankali kamar zai kalli Dr A'isha sai kuma ya fasa ya mai da kan ƙasa.
Sai a lokacin Uncle Bashir ya ce "Ya kamata kada ita Zahrah tasan cewa itama yarinyar matar Yaa Sheikh, a barta ta tafi da ita a matsayin Æ´ar aikin kamar yadda tazo da ita da manufar hakan"
"I also agree with this decision, she took it as her worker" cewar Dr A'isha. Abba Hakimi ya sauke numfashi yana duba lokaci,bayan nazartar maganganun sauran ya ce. "Na amince baka son Æ´ar fillo, suma sun yarda da hakan, zaka tafi da ita can gidanka dake Madina matsayin matar ka kuma Æ´ar aikin matar ka, zaka iya zuba idanu matar ka ta zama baiwa a cikin gidan aurenta, ra'ayinka ne,
Ni bance kaji tausayin ta ba, kawai ina son ka riƙe mini ita a wajanka na tsayin shekara ɗaya ciff, ka sata makaranta, ni bance ko sau ɗaya kayiwa Halisa Danejo kallon matar ka ba, ita ɗin kamar ajjiya ce na baka, ka dawo mini da ita shekara guda, kada naga wani sauyi a tare da ita, ka tabbatar yadda take budurwa a haka ka dawo mini da ita, nayi maka al'ƙawarin shekara nayi zan raba auren naku rabawa ta har abada" gaba ɗaya mutanan parlourn suka zubawa Abba Hakimi idanu, su basu ga dabarar haka ba, sun san ko shekarar biyar aka bawa Yaa Sheikh there is nothing he will do, there will never be any change from him, balle ya furta da bakin shi ya ce yana son ta,That will never happen.
Abba Hakimi ya gyara zama sosai idanunsa akan Yaa Sheikh ya ce "Amma Wallahi Wallahi Allah kenan Aliyu ban taɓa rantsuwa akan ka kamar haka ba, shekara guda tayi ka dawo mini da yarinyar nan saɓanin yadda nai tunani zaka sha mamakina, kai ba yaro bane ka fahimci mai nake son faɗa maka, babu dalilin da zai sanya ka lalata budurcin yarinya kuma ba son ta kake ba, This is a deal" Uncle Bashir ya ce "Amma Abba Hakimi wannan deal ɗin bai tsauri ga Malam ba?" Abba Hakimi ya ce "Ba kaji kai ma kace Malam ba? Yaa Sheikh zai iya ɗaukan wannan game ɗin" Murmushi Uncle Haroon ya yi kai tsaye ya yarda da abin da Abba Hakimi ya zartar cikin fara'a ya ce "To idan haka ne ina tsagin uwar gidan Halisa, za muje matsayin masu aikin gida kawai" Uncle Bashir ma ya ce "Ni ma dai ina team ɗin uwar gida" yaya Halima tai murmushi ta ce "Ikon Allah, to ina team ɗin Aliyu koma mai zai faru ya faru she is his wife matar shi ce babu laifi" Dr A'isha ta ce "Ni dai ba zan zaɓi team tun yanzu ba, sai naje Madina naga yadda zaman zai kasance" Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir shi kam a rayuwa mai Abba Hakimi ya mai da shi? Ina ruwan shi da wata ƴar fillo balle har yaje gareta matsayin miji mai buƙatar hakƙin shi wajan matarsa? Zai bawa kowa mamaki. Miƙewa ya yi a hankali zai bar wajan Abba Hakimi ya ce "No tayaya ka taɓa ganin anyi deal ba saka hannu, maza saka hannu a wannan dairy ɗin" Yaa Sheikh ya kalli Abba Hakimi da kyau, shi kam Abba Hakimi ya ɗauke kan shi alamar bai gane meke nufi ba. Cikin sauri ya saka hannu tare da saka suna da date da kuma time. Yana gamawa ya juya jiri na ɗaukan shi sbd ciwon kai ya nufi Part ɗin shi.
Abba Hakimi yabi bayan shi da kallo a zuciyarsa ya ce "let's see ko Aliyuna waliyyi ne"
Wajan ya yi shiru kowa da abin da yake tunani a ran shi, Mother na tunaninsu yadda zata cusa Halisa a zuciyar Yaa Sheikh, kallo ɗaya ta yi wa yarinyar hankalinta ya kwanta da ita, kawai dai ta fahimci bakin yarinyar babu control kamar ba a gasa mata shi ba. Yaya Halima kam gani take kamar Yaa Sheikh ba zai iya tsallake wannan gasar ba, lura da yanayin Halisa da komai sai tafi Zahrah jan hankalin ɗa namiji kowa zaman zai kaya ohhu! "Kada a bari Jadda da Engineer su san maganar auren wannan yarinyar Halisa da Yaa Sheikh, mu bari muga abin da hali zai aga yanayin zaman maybe a samu sauyin ra'ayi game da Yaa Sheikh akan yarinyar" cewar Uncle Haroon. Abba Hakimi ya miƙe tsaye haka Uncle Haroon da Uncle Bashir sukai wa Mother sallama.
Bayan tafiyar su yaya Halima ta kalli Mother ta ce "Yanzu me zaki Barrister?" Mother ta girgiza kanta idanunta akan wayarta tana neman contact É—in wata mata ta ce "me zan yi kowa yaya? ga Abban Sheikh nan ya gama magana" ta faÉ—i hakan tana danna call.
"Tun É—azo da nace ki kawo mini bottle water ina kika tsaya?" Zahrah ta tambayi Halisa tana zare mata idanu. Ta turo baki gaba ita tsakani ga Allah take son faÉ—awa Zahrah abin da ta fahimta wajansu Abba Hakimi. Zahrah ta ce "ba dake nake ba dan ubanki?" Da sauri Halisa ta kalli Zahrah bakinta na rawa ta ce "Baffana kika zaga? Ya mutu fa?" Wani tsaki Zahrah taja ta ce "Idan ya mutu ni na mutu? Waye shi da ba za a zage shi ba" Halisa ta jima tana kallon Zahrah idanunta ya yi jajir ga abin masifa babu halin yi sbd ka shaidin Dada a gareta.
"Matsa ki bani waje ai dama har uwar suka haɗu suka mutu Kinga baki da sauran wani gata kiyi mini aiki hankali kwance" Halisa ta juya da gudu tare da fashewa da kuka hannunta a fuskarta tana karewa. karo suka ci da Maimoon data ɗakko warmers ɗin lunch wanda akace ta kaiwa Zahrah, Maimoon ta ja baya da sauri tana faɗin "Subuhanallah ya akai kike kuka haka ke dawa?" Halisa ta kasa kuka sai shassheƙa da zata iya ita gida kawai zata gudu wallahi. Maimoon ta ce "Ok ya isa daina kukan jirani a nan wajan kinji?" Ta ɗaga kai a nutse alamar "to". Zahrah na kwance waya a hannunta suna vedio call da Deen wanda gaba ɗaya ba vedion Allah da Annabi bane, ita dai Maimoon taji wani sauti kamar gurnani da sauri Zahrah taja duguwar rigarta zuwa ƙasa tana rufe wajan data buɗe. She pretended not to notice what she had done. Tana ajjiye warmers zata juya Zahrah ta ce "Hey you" Maimoon tai banza kamar ba taji ba. "Ina magana" Maimoon ta juya kaɗan suka haɗa idanu ta ce "dani kike?" Ta ce "to waye a ɗaki?" Maimoon ta ce "Huh na ɗauka kina magana da wayar hannun ki ce" Zahrah ta sakko daga kan gadon ta ce "what the do you mean by that?" Maimoon tai shiru can Zahrah ta ce "What's your name?" "Maimoon" ta bata amsa Zahrah ta ce "Ok At least you have to respect me ni matar yayanki ce, kin shigo bedroom without my permission da muna tare Yaa Sheikh fa?" Maimoon ta ware idanu sosai ta ce "Yaa Lee a bedrooms ɗinki? Shhhh" tana faɗin hakan tai waje da sauri.
"Kan uba wannan yarinyar sai na saita mata zama kalli Yadda take mayar mini da matar tani?" Waya ta É—auka ta shiga kiran Surry.
Chapter 32 · 0% Book details