← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 55

Sashe 45

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Baki son Malam?" Ya tambaya kai tsaye domin shawo kan rigimar tata, ta riƙe hannunsa ta ce "Ina so bana, to ba naga Anti Zahrah ta rungomeka ba, shi ne naji kawai kuka yazo mini kaga gwanda na tafi gida" ya miƙe da sauri tare da shigewa bedroom ɗinsa not too long ya dawo fuska a kame, a tsaye ya sameta kallon da yake masa yasa ta saka hijab ɗin. Kana tabi bayansa babu kowa a main parlour dan haka ya nufi compound direct.
Yana zuwa Umar-khan na fitowa daga mota tare da faÉ—in. "Good Mrng Yaa Lee" kai ya É—aga masa ya shiga bayan mota, itama Halisa ta shiga bayan motar gatekeeper ya buÉ—e musu fita.
Sun jima da tafiya amma abin mamaki Halisa bata ce komai ba, ko Umar-khan bata gaisar ba, a haka suka ƙarasa Al Aqeeq International School. Umar-khan ya yi parking a harabar makarantar tare da fita yabar musu motar, ƙoƙarin buɗe motar take ta fita taji ya kamo hannunta taƙi yarda ta kallesa alamar dai She's still angry with him. Wani sirrin baƙin zare ya ɗaura mata a hannunta, ya riƙo hannun da kyau ta yadda dole ne ta matso kusa dashi idan taji an jawota, sukai kusa da juna.
"Ƴar fillo" ya ce a hankali da sauri ta kallesa sai taga ba ita yake kallo ba, ta ce "gidan zaka bayar dani?" Sai a lokacin ya juya gaba ɗaya zuwa gareta a hankali numfashinsa ke sauka cikin murya ta yanayin gajiya da kasala ya ce.
"Anti ba zata sake ba,
Amma idan Anti bata rungome Malam ba waye zai rungome shi?" Bakinta na rawa ta ce "Ni matar malam zanyi" ya buɗe ido sosai da sosai yana mmkin ƙarfin halinta. "Da gaske ni kullum sai na rungome ka nace maka mijina" bashi da wani option wanda ya shige bin bakin mganar da kallo ya daɗe yana kallonta kafin ya ce.
"Uhm" da sauri bakinta na rawa ta ce "Ai na iya bari ka gani" kafin ya yi magana ko wani yunƙuri yaji gaba ɗaya ta zagaye hannuwanta tare da rungome shi, ta ɗora kanta a ƙirjinsa, ya buɗe idanu da sauri cikin In-inar data zo masa ya ce. "Su...su... Subuhanallah Ya Allah....

Ta saki dry sosai ta ce "Abba Allah na iya kaji ai?" He was completely lost for words and just shook his head. Bayan wasu giftawar seconds ya nuna mata ƙofa da hannu ta buɗe ƙofa tare da fita, a hankali shima ya buɗe ƙofa ya fita tare da fitowa yana ƙara covering jikinsa da kyakkyawar shigar dake jikinsa. Umar-khan na ganin fitowar Yaa Sheikh ya ƙarasu wajan yana mai sakin murmushi,kai tsaye office ɗin headmaster school ɗin Yaa Sheikh ya nufa, gaba ɗaya teachers na school mmkin ganin Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu a cikin makarantarsu ya kama su, kowa sai durƙusawa yake yana miƙa gaisuwa a nutse cike da kamala nutsuwa yake ɗaga musu hannu yana ƙara kame kansa wanda yake fidda kwarjinin shi.
Cikin mutunci Headmaster ɗin mai suna Ayyan ya miƙe yana gaida Yaa Sheikh. Umar-khan ya ce "you did the interview for her, then you look at the one class that is suitable for her" Headmaster ɗin ya kalli Halisa cike da birgewa ya ce. "What's your name?" Tai ƙasa da kanta sam bata ji me yace ba, balle ta fahimci me yake cewa. Ya ɗauka bata gane english sai ya juya zuwa cewa.
"ma asmuk?
kam eumarka?" Nan ma tai shiru Ayyan ya kalli Yaa Sheikh cike da martabawa ya ce

"سنضعها في الصف الأول حتى تتمكن من أخذ الدروس"
_“Zamu sakata a matakin farko domin ta fara darasin”_ cewar Ayyan Yaa Sheikh ya numfasa ba dai ce komai ba. Ayyan ɗin ya ce. "Zata samu gogewa cikin ƙaramin lokaci Insha Allah, kuma a nemata mai darasi a gida,that will help her study more" Umar-khan ya yi murmushi ya ce "How long do you think she can take the time before she can learn everything, and get experience" Ayyan ya ɗan kalli Halisa yana karantar how smart she's kafin ya ce "I can't say how long it will take,But she will get good academic training" Umar-khan ya ce "that's good, amma matar...." Gyaran Muryar da Yaa Sheikh ya yi ya hana Umar-khan faɗin abin da ya ke shirin faɗa ɗin. Yaa Sheikh ne ya fara miƙewa yana kallon lokaci a nutse ya ce.
"A kula, banda wasa" ta miƙe tsaye tana shirin yin magana ya yi waje abinsa domin yasan zata iya faɗin abin da ba shikenan ba, bai shirya ɗaukan abin kunyarta cikin mutane Yanzu ba. Idanunta ya cika da hawaye sosai tana neman yin kuka a haka Headmaster ɗin ya kaita Jss 1. Akan idanunta kuma motar Abban nata da Umar-khan ta fita waje. Ita ɗaya ce a table nata, gaba ɗaya class ɗin basu da yawa dukkansu farare dasu gwanin sha'awa, itama ta saje dasu sbd farin da take dashi mai tsari.
Shiru tayi tana kallon kowa da idanu kowa na ajin harkar gabansa yake a haka Headmaster ya gabatar da ita ya fita. Babu jimawa wani kyakkyawan balarabe ya shigo cikin jallabiya ash ya É—ora half É—in hula a kansa, bai tsaya jiran gaisuwarsu ba. Ya nufi blackboard inda suke duba kamar computer haka ya shiga latsa abubuwa sai ga sunan subject ya fito

_Social studies_
A ƙasa kuma aka rubuta _MEANING, SCOPE AND NATURE OF SOCIAL STUDIES_
Matashin ya kalli students É—in dake gabansa, har lokacin idanunsa bai kai inda Halisa take ba, cikin kamala ya ce.
"Alhmd, yau zamu fara da meaning na social studies, please who can tell me the full meaning of Social studies?" Duk sukai shiru ya ce.
"It's okay" ya É—an duba abu kaÉ—an kana ya mai da attention nasa ga É—aliban ya ce.
_“Social studies can be defined as the study of man and his environment. Social studies can also be defined as the totality of man’s physical and social environment”_ daga nan ya yi musu explanation yadda zasu fahimta ya saka english ya saka Larabci maybe they can understand very well. Yana ƙoƙarin yin magana yaji ance.

"To aradu nidai tunda ka fara magana ban san me kace ba, idan zaka faɗa da hausa kawai ka faɗa ko kayi shiru" ya juya gaba ɗaya zuwa direction ɗin da daddaɗar muryar dake tashi, yana juya a ƙaramin bakinta idanunsa ya sauka, magana take sosai ko haɗiyar yawo ba tayi. AZAAN ya ware fararen idanunsa akanta da kyau, da alama ita ɗin new student ce, yasan magana take amma baya gane me take cewa sosai, ya dai san hausa take.
Ya É—auke bai tankata ba ya ce.
_“SCOPE OF SOCIAL STUDIES”_
_The word “man” in the definition given above connotes human beings while man’s environment has a huge influence on mankind in all spheres of life. Man’s environment affect their language, dressing, food and every other thing one can think of in the society,_ _Man also interacts with two environments which are:_
Physical environment (Natural)
Social environment (Artificial)".

"Tab ni dai dama ba wannan makarantar aka sani ba, malamin ba babu abin da ya iya" Azaan ya dubi Halisa ya ce "What's your name" ta tura ƙaramin bakinta ta ce "Me kace?" Wata wacce ba zata shige age mate ɗin Halisa ba mai suna ABIR ta ce "Ya ce ya ya sunanki?" Halisa ta ƙaramin murmushi kawai cikin siririyar murya ta ce "Halisa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Azaan ya buɗe idanu da kyau cike da mamakin jin sunan data alaƙanta kanta dashi, Yaa Sheikh take nufi ko wanne? Dama yana da yarinya yaushe ma ya yi aure har ya samu yarinya kamarta?. Azaan ya ce.
"Abir make her understand, explain to her" Abir ta ce "Okey Sir" mai Hali baya fasawa domin Azaan na shirin fita ta ce "Kuma na manta na faɗa maka ina da aure" Azaan ya kalleta sai kawai ya fice dan ya lura bama tasan shi kansa auren ba har take cewa haka. Ya tafi cike da sha'awar surutunta wanda ya birgesa lokaci guda. Abir taiwa Halisa bayanin komai na topic ɗin cikin harshen hausa, ta ce amma ta rage surutu da yawa a haka ta ƙare zaman makarantar wani karatun ta gane wani a'a, Umar-khan da kansa yazo ɗaukanta sbd Yaa Sheikh yana can wajan lecture ba zai samu dama ba.
Chapter 45 · 0% Book details