← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 55

Sashe 34

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin san shi ne da kike son shi?" Mother tayi tambayar idanunta akan Halisa wacce hawaye ya gama cika mata idanu. Ta kasa cewa komai amma bakinta bai bar rawa ba, ganin yanayin ta ya sanya Mother sassauta murya ta ce "Kina da ƴan uwa a garin nan?" Ta girgiza ta ce "Aradu babu" "Ok to ki Saurare ni da kyau, listening to me..." Tsayawa tai da maganar idan ma tayi ta san a banza, Halisa does not speak English, let alone understand what is being said. Ganin bata da wani option wanda ya shige tayi magana da harshen da Halisa zata gane ya sanya Mother tattara nutsuwarta ta ce "Ki ɗauke ni matsayin uwa kafin ki koma gida, zan riƙe ƙo kamar ƴar dana tsuguna na haifa, da farko ki yarda cewa ke matar Yaa Sheikh ce Balarabenki kamar yadda kika ce ɗin, Kinga zoben hannunki shi ne sadakinki, abu na biyu kada ki kuskura koda wasa ki faɗawa Zahra kema matar Yaa Sheikh ce, duk aikin data saki kiyi zaki samu lada albarkacin igiyar auren dake kanki, duk abin da Yaa Sheikh zai ce kiyi just do it ina nufin kiyi kai tsaye, ba zai cutar dake ba, infact ai kin riga da kin san shi ko?" Halisa ta ɗaga kai da sauri kuma ta ce "Kuma ina son shi ai, ina ganin shi idanuna idan ina barci" Mouth ta ce "Good, a kullum yana tashi tun ƙarfe 4 na dare baya komawa barci sai ƙarfe 12 sbd ƙarfe 8 yake zuwa wajan ɗaliban shi, duk inda 12 tayi ya dawo gida, bai damu da abinci ba sosai ba zai taɓa cewa yana jin yunwa ba, tsakanin azahar da asr yana barci idan bai ba, ciwon kai yake sosai, sannan baya rabo da black tea da zuma a ciki, duk ranar Alhamis da Litinin azumi yake, yana son ƙosai sosai" Halisa ta saki murmushi tare da riƙe hannun Mother ta ce "Innalillahi ƙoshai aradu daɗi akwai burudi to? Wayyo Allah zanci ƙoshai na mure" dariya Mother zatai ko takaici bata son duk wannan shirman a wajan Halisa.. "Zaki samu abin da yafi ƙosai ba, amma can idan kina shirme gidan yankan kai suke kai mutum, ki zama a nutse, bayan haka yana son abincin gargajiya tuwo, dambu da sauran su dai, ki tabbata kina wanka sau biyu zuwa uku a rana, idan ba haka ba Yaa Sheikh kurarki zai yi daga gidan shi, kuma kishiyarki ta rabaki da mijinki har abada" Idanun Halisa ya sauya kala jin abin da Mother ta ce. Bayani Mother taci gaba dayi mata cike da ƙwarewa ta ɗora da faɗin. "Kina jin alamun ya dawo, ko babu abin da zai miki kije wajan shi kice kanki ke ciwo ko ya koya miki karatu, zan zuba miki kayan amfani masu kyau ki tabbatar kina using dasu amfani kinji?" "Zan yi ai, amma dai ba zata ƙwace mijina ba ko?" Mother ta haɗiye dryar data zo mata ta ce "Akan me? Idan kina yin abin da nace bata isa ta ƙwace miji ba, amma idan bakya yi uhm ko ganin shi kin dai na yi, yawwa sai gaisuwa kullum da safe kije ki gaishe sa, da yamma haka da kuma daddare, akwai lokacin da yake ciwon kai bai azabar zafi ganin shi har ɗauke yake ya zama kamar makaho, zan faɗa miki abin da za ki yi idan ciwon ya tashi, yanzu maza jeki gama aikin ki za kuje a gyara miki wannan gashin kan" Halisa ta miƙe tsaye kanta a ƙasa ta ce. "Na gode" "is nothing jeki daughter" sai da taje bakin ƙofa ta juya a hankali ta kalli Mother idanunta ya yi raurau da hawaye ta ce. "To yaushe zan faɗawa ina da miji? kuma yaushe zan fara dama masa fura" a ranta Mother ta ce "na shiga uku, wannan za ayi sirri da ita kam?" A file ta ce "zan faɗa miki ranar jeki" ta juya ta fita tana ayyana cewa da gaske dai Balarabe mijinta ne. Kai tsaye ɗakin Zahrah ta koma taci gaba da shirya mata kayan da zata tafi Madina dasu, zuciyarta cike da tunanin maganganun da Mother ta faɗa mata. Ta sauke ajjiyar zuciya a fili ta ce "Wallahi kyakkyawa da shi, Allah ya sa na zama kamar shi" ta faɗa tana taɓa fuskarta sai kuma ta miƙe da sauri tana nufar inda mirror yake, a hankali ta shiga ƙarewa kanta kallo, bata hango nata kyan zallar kyan da Rabbil izzati ya yi wa Yaa Sheikh idanunta ke hangowa. Tsaye tayi a bakin ƙofar da zata kaita parlourn Yaa Sheikh tun a nan kuma ta gane Yaa Sheikh daban yake a gidan, tsarin shi da yadda yake tafiyar da rayuwar shi, bata taɓa shakkar tsayawa gaban namiji ba, amma a yanzu tsoro da fargabar tsayawa gaban Yaa Sheikh da yadda kaifin idanun shi ke tasiri a zuciyarta sun gama cika Zahrah. "No Zahrah Aliyu mijinki ne, ki koyi zama da shi kafin ki fara juya rayuwar shi tamkar waina a tanda, dole ragamar rayuwar shi ta dawo tafin hannunki" wata zuciyar ta shiga gargaɗin haka, jikinta ta kalla tsaf duk da kasancewar ciki ne jikinta amma ƙirjinta yana kwance ya manne da fata, ita kalar halittar ce ko kuma garin yawan ta zubar aka gama lalata halittar da Ubangiji ya yi mata wacce kuma iskancin kawai ta sani sam bata san tsaunin da zata hau tabi ba, zuwa tubalin da zai gyara mata garkuwar jikinta. Ta tura ƙofar a hankali ƙamshin air-con da wani air freshener sune suka daki hancinta, shigar ta parlourn ya yi daidai da sautin karatun Yaa Sheikh dake ratsa cikin wajan har ya kawowa kunnenta farmaki. Yana zaune saman kujera ya ɗora farar ƙafarsa akan table idanunsa rufe a haka yake motsa bakinsa yana karatun cikin baiwar da Ubangiji ya bashi ya sahale masa yin karatun ba tare da harɗewar harshe ba.. Zahrah ta bi farar Jallabiyar dake jikinsa da kyau da kyau, zuwa kansa dake rufe hirami hannunsa guda ɗaya riƙe da carbi yana ja. Ta nemi wajan a kujerar dake kusa da shi ta zauna tana fari da idanu tare da juya jiki amma ta kasa yi masa magana balle gaisuwa. A jikinsa yaji ana kallon shi bambancin ƙamshin turaren da bai taɓa ji a gidan yasa ya fahimci ko waye ba ɗan gidan bane. Zahrah ta gyara murya ta ce. "My Excellency" "Shhhh" Yaa Sheikh ya furta a ran shi gaba ɗaya murya ko a maza bai taɓa jin mai amonta ba. Ganin ya yi shiru ta ɗauka ko bai ji mai tace bane?. "Daman nace bari nazo muga juna muyi hirar ku mintuna biyar ne kafin mu tafi gidanmu" still shiru ya yi mata, ta miƙe tsaye cike da kwarkwasa ta ƙarasa har zuwa inda yake tare da zama kan armchair ta saka hannu ta shafi fuskar shi kaɗan zuwa dugun gemun shi ta ce. "You're just quiet, but I know you hear what I'm saying" a wannan lokacin Yaa Sheikh ya ɗauka gangar jikinsa zata ƙaryata zuciyarsa, amma sai yaga abin ya zama diro, ya ƙara tabbatarwa lallai to da gaske bashi da cikakkiyar lafiya irin ta cikakkun maza, mace ƴar 32 tazo har inda take suyi very close da juna amma ko tsigar jikin shi bai ji ta motsa ba, balle ya yi zaton zai ji abin da Khalil ke masa surutu akai. Zahrah ta kai hannu zata ƙara jan gemun shi ya buɗe narkakkun idanunsa na mai kama da mai jin barci. He didn't give her a full look, because looking at people is not his style. Bai sake kallonta ba ya miƙe tsaye yana goya hannunsa a baya, ya nufi bedroom ɗinsa, Zahrah ta ce "Amma dai ni matarka ce ka sani?" Ya tsaya cak ba tare daya juya zuwa gare ta ba, kamar zai magana sai kuma ya fasa ya shige cikin bedroom ɗin, Zahrah tabi bayan shi da kallo me hakan yake nufi? Ta ɗauka zuwanta gare shi zai nuna wata buƙuwa ta miji ga matar shi sai kuma taga saɓanin haka. Ta juya ta sauri Dr A'isha dake Main parlour tabi Zahrah da kallo wato halitta kala-kala ce, ita bayan shekaru da zubin halittar jikinta har wani tumbi take dashi kamar namiji?. A fili Dr A'isha ta ce "Allah ya kyauta" tana faɗin hakan ta miƙe zuwa bedroom ɗin Mother itama a yau take son shigewa gidan mijinta. Zahrah na shiga bedroom ɗinta ta saka ƙafa ta murje yatsun Halisa cikin faɗa ta ce "ke kam wacce jakar yarinya ce? kina ganin mutum ba zaki matsa daga hanya ba?" Halisa da idanunta yayi jaa sbd zafin da yatsun suke mata, ta kalli Zahrah ta ce "Kiyi haƙuri" ta saka hannu ta ɗauke Halisa da mari ta ce "haƙurin uwarki? Ni dai na shiga ban ɗauka fulani mahaukatan gaske bane sai yanzu" gigicewar da Halisa tayi yasa ko gabanta bata iya gani, ba a taɓa yi mata mari da tafkeken hannu kamar na maza irin wannan ba. Ruɗewar da tayi yasa ta nufi wata ƙofa a tunaninta part ɗin su Maimoon ne, tana fita taci karo da mutum a hanyar zuwa swimming pool. El-bashir yaja baya da sauri yana kallon farar kyakkyawar yarinyar data fito hannunta a fuska tana shassheƙar kuka, ya taɓe baki yana ƙoƙarin shigewa Halisa tayi saurin kama hannunsa cikin matsanancin kuka ta ce. "Hamma fuskata zata cire wayyo Dadata fuskata ka taimaka mini" sai murza fuskar take da hannunta guda ɗaya, ɗaya kuma ta riƙe hannun El-bashir da shi. Hannunsa ya sanya zuwa hannunta dake fuskarta cikin ƙasa da murya ya ce "Sorry" ya faɗi hakan yana ɗauke hannunta. Cikin daƙiƙo ya nemi ji da ganinsa ya rasa, tunaninsa ya tsaya cak, ya zama kamar wani stateu yana ganin tarin kamanni amma bai taɓa cin karo da zallar kama irin ta yau ba. Hannunsa na rawa ya kama fuskar Halisa da kyau yana ƙare wa hukuncin Rabbil izzati ido, ita dai kuka take sosai ba ƙaramin gigita marin ya yi ba. El-bashir ya sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da haɗiye mamakinsa, ko ita ce yarinyar da Khalil ke bashi labari?. Ya shiga goge mata hawayen fuska tare da faɗin "ke dawa? Wace ke? Mene sunanki?" Ya jera mata
Chapter 34 · 0% Book details