Sashe 4
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“What is Bachelor of Science in Conservation Biology?" Dake tana ɗaukar su course ɗin Conservation Biology Under Faculty of Sciences ne. Shiru duk sukai suka kasa bata amsa hakan yasa Zahrah sakin tsaki a file ta ce "Is an assignment, ba zan wasting time ɗina wajan yi muku explanation ba, i have so much work to do bye" wani daga cikin students ɗin ne ya miƙe yana dariya tare da ƙwaiƙwayar yadda Zahrah ke tafiya ya tsaya gaban ɗaliban ya ce "I have so much work to do bye... Big Maaaa The arrogant one I hate this woman. But i like her style" gaba ɗaya Students ɗin suka saka dry ba kuma kowa ke ƙaunar Zahrah ba, wulaƙanci da disga mutane ya mata yawa, kuma idan ta shiga hall babu wanda ya isa ya shiga ga bada Assignment da shegen text da Attendance. Zahrah na fita ta nufi Office a nutse take tafiya cikin takun isa da gadara tana sanye cikin wata atamfa Amarya collection mai tsada ɗinkin riga da skert ya kama jikinta sosai, idanunta sanye cikin farin cat eyes wanda ya ɗan haska ɓakar fatar jikinta she's classes and educated ƴar wanka ce ga tsafta da tarin ilimi. Ƙafarta dake sanye cikin Derby shoes ta tura cikin office ɗin tana ya tsona fuska ta ajjiye handbag ɗin L.v akan kujera idanunta akan Surayyerh ta ce "Lafiya dai?" Surayyerh taja tsaki ta ce "ina lafiya? Can you imagine yau Mom ce ta mareni sbd wancan banzan?" Buɗe idanu Zahrah tai kamar ba zatai Mgn ba sai kuma tace "mene abin damuwa?" "Zahrah mari fa? Wallahi ba zan ƙara ɗauka ba idan aka sake marina, Look at me am 29 going to 30 ace Mom bata bar marina ba?" Girgiza kai kawai Zahrah tai ba tare da ta ce komai ba. "Ina magana Kinyi shiru, wannan miskilancin naki na tsana fa" "uban me kike son nace maki Surayyerh? Your mother has been slapped you sbd kinyi kuskure sai nace bata kyauta ba? Babu abin da zaki iya sbd Uwa ce dole ki hqr" Zahrah ta faɗa cikin ɓacin rai. "i can't bazan iya jurewa ba" cewar Surayyerh "ok zaki rama kenan? Are you going to beat your mother?" Surayyerh ta girgiza kai cikin damuwa ta ce "A'a kawai zan faɗa mata kada ta kuskura ta sake marina, Nasan Uwa tace kuma sai tai ta dokana akan wanne dalili, ɓacin rana nake gudu" Kallon Surayyerh kawai Zahrah keyi kafin taja numfashi ta ce "Ina cikin damuwa Surayyerh na fara tsorata fa" Surayyerh ta ce "Damuwa akan me?" Hannu Zahrah ta ɗora akan cikinta ta ce "Am pregnant Surayyerh ina da ciki wata uku, kuma na gaji da zubar da ciki wallahi" zare idanu Surayyerh tai tana faɗin "Pregnant? ciki na huɗu kenan fa Zahrah? Kina da hankali kuwa? Wannan karan dole ki yafe cikin kin manta mai Dr yace miki ko?" Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke kafin ta kalli Surayyerh da kyau ta ce "I'm not ready for this, kin san ba aure gareni ba, idan na bar cikin na haihu me zance a gida? Me zan faɗawa Mimi? daman Kullum cikin faɗan naƙi aure take wai na girma da yawa, karatun boko ya buɗe min idanu yanzu kusan shekaruna 31 ne Surayyerh" Surayyerh ta numfasa ta ce "Me kike jira? Ki kira Deen mana kuyi magana ya turo iyaye kuyi aure, Mimi nada gaskiya Kinyi primary, secondary, N.c.e, degree, kinyi masters to what are you waiting for wanda ya shige kiyi aure, haba ai ta boko ai ta boko nifa idan yanzu ne wlh ba zan wata boko ba, shekara 31 ana abu ɗaya sai zallar iskanci kawai da kike kina zubar da ciki a banza, sai kin gama zubar da ƙwayayen da Ubangiji ya baki matsayin zuri'a a banza wlh" Tsaki Zahrah tai "wani lokacin wlh ke Mahaukaciya ce, ni kike tunanin zan iya auren Deen yanzu? Inda a yanzu nasan rayuwa nai boko naje ƙasashe kala-kala da ace ko secondary schl ban rufa ba shi ne zan iya auren Deen amma yanzu kam i can't, zanje hospital a cire cikin, da kike maganar haihuwa waye ya faɗa miki daman ina son raya da haihuwa da yawa ne? Abeg ta shi muje Madam am not in the mood" Surayyerh ita dai mamakin Zahrah take bata, ta rasa ita da Zahrah waye yafi laifi, ita tana ganin mahaifiyarta na takura mata domin har kusan zaginta take a zuciya, ta hanata jin daɗin rayuwa komai sai ta ce wai taji tsoran Allah, ita kuma Zahrah iyayenta sun sake mata duk abin da zatai babu me cewa dan me gidansu gidan boko ne a waye suke gaba ɗaya, hakan yasa Zahrah keta aikata alfasha hankali kwance. "Kinzo da mota ne?" Surayyerh na miƙewa tsaye ta ce "E, kefa?" Zahrah ta ce "A'a, ba zan iya driving ba wannan cikin duk ya sauyani muje kiyi dropping nawa gida" "ok let's go" Fita sukai Zahrah da Surayyerh aminai ne duk faɗan da za suyi har abada babu mai ji, su gama fushi su shirya. Mota suka shiga Surayyerh na driving Zahrah na gefe a haka suka bar cikin Abti America.
Da idanu Dada take bin kuɗin da Danejo take bata, a sanyaye ta ce "Duk wannan?" "E, Dadana ɗan Almajirin mai yagaggun kaya ne yace mini aradu duk kindirmo ake siya dasu, kuɗin da yawa" Dada ta jinjina kai ba tare da tace komai domin magana bai dameta ba, tun bayan rasuwar Baffansu Danejo ta zama shiru-shiru sanadin hakan ciwonta ya sake yin tsamari. "Dadana nawa ce wannan?" Danejo ta tambaya tana nunawa Dada gudar dubu ɗaya, girgiza kai Dada tai bayan ta tsurawa dubu ɗayar idanu ta ce "Ban san sunanta ba, ki bari Hamma Yabi ya zo sai ki tambayeshi ko?" Miƙewa Danejo tai ta ce "Bari naje wajan Shatu na tayata irga Naggenmu" fita tai a hanya taci karo da Hamma Yabi, da sauri Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya shiga duba Funa, Fobbina, Wayla, Hirna. Ma'ana Gabas, Kudu, Arewa, da Yamma, ganin ba kowa yasa Hamma Yabi faɗin "Mun shigesu Danejo, gobe ake bikin gasar wasa da maciji, wanda Sarkin ruga yake sawa, kuma yau za'a zaɓi wanda za'ai wasan dashi" fararen idanunta ta juya sosai cikin rashin damuwa ta ce "Hamma mene abin damuwa, ni Dadana kawai nakeso ta samu lafiya ina ta mafarki wani kala" girgiza kai Hamma Yabi yai kaifn ya kama Danejo sosai ya ce "Baka iya wasa da Mashiji ba Danejo, kuma Sarkin ruga zai iya zaɓarki matsayin wacce zatai wasan, idan baki iya ba Mashijin zai iya saranki ki mutu murus, ko baki mutu ba idan baki iya ba Sarkin ruga zai iya korar mutum daga cikin Rugar Rome" cike da tsoro Danejo ta zaro idanu waje ta ce "Mi boni Hamma Yabi yaya zanyi?" "Yanzu shai mu jira muga wa za'a zaɓa, kije ki ɗauki kindirmo mai man shanu ki bawa Dada gobe zamu koma ashibiti" kai ta ɗaga alamar to Hamma Yabi ya nufi cikin jejin nemo wani sassaƙen magani ita kuma ta nufi wajan garke a nan ta samu Shatu ta kama bakinta a nonon Nagge tana ta sha hankali ƙwance. Zama tai kan wani Leggal (Icce amma kututture) samun kanta tayi da tunani wanne kalar Mashiji za'ai wasan dashi? Meyasa idan taje Birni take ganin wasu mutanan ba irinsu ba komai nasu daban ne, meyesa birni ta banbanta da Rugar Rome?. Ajjiyar zuciya ta sauke tana murza yatsun hannunta da sauri takai dubanta zuwa ga ƙadamin yatsarta idanunta ya sauka akan zoben dake maƙale da yatsar da tsananin mamaki take kallon hannu yaushe wannan abun ya zo hannunta? Mene sunansa ita bata taɓa ganin abu mai kama da zobe ba sai yanzu, ga wani zane a tsakiyar zoben kamar tambarin abu amma bata san ko mene ba, ƙoƙarin zare zoben take amma ta kasa hakan yasa dole ta hqr. Suna zaune a garken suka ji ana shelar Sarkin ruga yana neman jama'ar Rugar Rome baki ɗaya. Da Shatu da Halisa suka kalli juna zuciyarsu cike da zullumi amma Danejo tai ta maza ta kama hannun Shatu suka nufi wajan. A tsaye suka samu mutane wasu na sanye da fararen kaya na Fulani wasu kuma Kuraye yawancin su gaba ɗaya farare ne, amma sam babu cikakken addini ga rashin tsafta. Sarkin ruga ya gyara tsaiwa yana faɗin "Kamar yadda kowa ya sani, a gobe ne zamu gabatar da gasar wasan Mashiji, za'a zaɓi mutum ɗaya ya buga wasa da ƙaton Mashiji kamar yadda muka saba, idan mutum ya kashe Mashiji akwai kyautar Nagge da kuma ƙwayar nono guda hamsin, idan Mashiji ya kashe mutum Shi kenan wasa ya zo ƙarhe, idan mutum bai mutu kuma za'a kuresa daga Rugar Rome baki ɗaya, don haka yanzu zamu fito da alƙalin wasa ya zo ya zamu wanda za'ai wasan da shi" Shatu ta ƙankame hannun Danejo ita ko kalmar Mashijin bata so taji an faɗa balle ta gansa a gabanta. Dajeno kam shiru tai kanta a ƙasa tunani fal ranta domin gaba ɗaya ma hankalinta baya wajan. Alƙalin wasa ya fara zagaye mutane har ya shige kan Danejo gama dubawa yai sannan ya gyara murya ya ce "Mun zaɓi Halisa Dajeno Rome a matsayin wacce zata fafata da ƙaton Mashijin mu a gobe....
#Sarautar marubuta
#True life story
*🌈 IDAN BA KE 🌈*
Nimcyluv sarauta
*_Arewabooks@Nimcyluv_*