← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 55

Sashe 10

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ke! Ke! Baiwar Allah" aka shiga kiran sunanta wanda yasa ta buɗe idanunta da sauri tare da fatan Allah ya sanya a cikin Rugar Rome take, wasu fatake ta gani su wajan biyar tsaye a kanta ko wanne hannunsa riƙe da abu. Sai a lokacin ta lura ashe a kwance take saman wani ya shi saɓanin ɗazo da take kan dutse. Idanunta take rattabawa tare da binsu da ido ganin ba wanda ta sani yasa ta mayar da kanta ƙasa "Baiwar Allah wace ke daga ina kike? Kin san ina ne nan a Maiduguri kike fa?" Da sauri ta kalli mai maganar sai bata ce komai ba. Wani daga ciki ya ce "Ko bata magana ne? Kamar bafulatana" "Akwai abin da ke damunta Allah kaɗai ya sani" cewar wani, yin duniya sukai tai magana ko ta faɗi garin da take amma tai shiru kamar an kulle mata baki dole suka barta bayan sun yi mata fatan alkairi.
"Danejo" aka kira sunan a taushashe sautin Muryarsa da taji yasa tai saurin Miƙewa yana tsaye kamar kullum sanye da fararen kaya ga tarin nutsuwa da ilhama a tattare da shi. da sauri ta nufesa kamar zata riƙesa sai kuma ya tsaya dab dashi tana sakin kuka tare da faɗin "Ɗan Balarabe ka kaiki gida kaji, tsoro na keji ina son nasan halin da Dadata ke ciki" Prince ya sake mata murmushi yana faɗin "Waya kawoki nan?" Hannu ta watsa alamar bata sani ba da sauri ta ce "Amma ka sanni ko? naji ka iya kiran sunana do Allah ka kaini wajan Dadata" yana kama hannunta ya ce "Ban san inda kike ba, Danejo kuma sunan matata ne ina iya kiran sunan kowa da ita" da fararen idanunta ta kallesa ba tace komai ba, sai hawayen dake suntiri a cikin idanun nata. Hannunta ya riƙe yana janta da Shira tun tana kuka harta daina, tana zaune taga ya kawo mata naman kaji da yawa da kuma kayan marmari ƙin cin komai tai sai da ya fara mata wasa yana bata labarin abin dry sannan ta saki jiki taci kayan marmarin. "Zan kaiki gida" da sauri ta ce "Da gaske kake Balarabe?" Kai ya ɗaga mata yana faɗin "E, Matata" turo baki tai ta ce "Ni ba matarka ce ba" ya ce "Daman ba dake nake ba" kamar ba zatai Magana ba sai ta ce "Yaushe zaka kaini wajan Dada" yana riƙo hannunta ya ce "Ko yaushe, amma kiyi mini Al'ƙawarin na dinga zuwa ina koya miki karatu, kuma kiyi al'ƙawarin zamu zama ƙawaye a duk sanda na buƙace ki, kizo gareni ba zan cutar dake ba na rantse da Ubangiji al'arshi, ba zan bari kuma kowa ya cutar dake ba" tunda ya fara magana take kallonsa cikin rashin sani ya ce "Kuma Dadata zata samu lafiya?" Shiru yai mata an riga anyi masa iyaka da mahaifiyarta, babu abin da zai iya a gareta, sai dai ya sanya Safwan yai wani abu akai. "Uhm ni kayi magana mana" ta faɗa tana jijjiga hannunsa kai ya ɗaga mata ya ce "E, kina zuwa ya kiga ta samu lafiya" Murmushi tai Wanda ya bayyanar da kyanta a hankali ya dinga ɗauke mata tunani harta manta da batun gida sulalewa tai ta kwanta saman ƙafarsa barci ya ɗauketa.

ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA.
_Jami'ar Musulunci ta Madinah_ masarautar Saudi Arabiya ta kafa jami'ar bisa umarnin sarauta a shekarar 1961 a tsattsarkan birnin Musulunci na Madina. Koda yake wasu sun danganta akidar Salafiyya da bude jami'ar, ana ganinta a matsayin rashin fahimta sakamakon halayyar da cibiyar ta ke da ita ga kowane akida. Jami'ar ta sami takardar shaidar digiri na jami'a ba tare da banbanta ta ba daga Hukumar Kula da Ilimin Kimiya da Nazari a watan Afrilun 2017.

Jami'a ce mai tsarin gaske musamman Ɓangaren Addini. Ga nagartattun Malamai, da yawan ɗaliban na son karatu a jami'o'in Saudi Arabia sbd dalilai masu yawa. Manyan jami'o'in Saudi Arabia an basu shaidar yabo a bangaren ilimin kimiyya. Wasu daga cikin jami'o'in Saudi Arabia suna cikin manyan jami'o'i a duniya dangane da cibiyoyin bincike. Jami'o'in Saudiyya suna ba da kyakkyawan yanayin binciken ilimin, ta hanyar ingantattun cibiyoyin bincike. Yankunan ilimi da al'adu iri daban daban a jami'oin Saudiyya. Akwai daliban duniya daga sama da kasashe 165 da ke karatu yanzu haka a jami’o’in Saudiyya. Baya ga manyan masana ilimi da ma’aikata da ke aiki a waɗannan jami’o’in. Jami'o'in Saudiyya suna ba da cikakkiyar kulawa mai kyau ga ɗalibanta da kuma malamanta. ire-iren wannan manyan dalilai yasa akeso da burin karatu a jami'o'in Saudi Arabia.

Da sauri ya fito daga ɓangaren hall ɗin da aka ɗauki darasin Islamic Studies and History. Kansa a ƙasa ya tatatare hannayensa cikin milk ɗin Arabian jallabiya daya saka sai wani ƙaramin baƙin hirami da yai rawani dashi, ɗaya hiramin kuma ya ɗora saman kafaɗarsa. Wasu matasa ne manyan suke take masa baya hadda wasu securities. Yanayin yadda yake tafiyar kaɗai zai tabbatar maka babu sassauci a zuciyarsa, idanunsa yai jajur bai taɓa shiga ta shin hankali na yau ba, yana zuwa bakin wata farar mota jikin Umar-khan na rawa ya buɗe masa murfin bayan motar ya shiga, Malamin na shiga mota, Umar-khan ya shiga gaban motar bayan driver ya shiga. Da sauri Driver yai wa motar key ganin haka yasa Saif-Wazir ya shiga wata motar kai tsaye daga cikin University ɗin Prince muhammad bin abdul'aziz international airport suka nufa.

Ta cikin madubin motar Umar-khan yabi Sheikh Aliyu Haydar wanda ke bayan motar da kallo, ya jingina da jikin Kujera sai huci yake fitarwa, ya rirriƙe Jallabiyar jikinsa da hannu bibbiyu, gumi na tsastsafo masa ta tsakiyar goshinsa sbd yadda zuciyarsa ke masa zafi da ta fasa. Girgiza kai Umar-khan yai cike da tausayin yanayin yadda Sheikh Aliyu Haydar ke gabatar da rayuwarsa. Juyawa yai yaci gaba da kallon yadda driver ke sharara gudu, har suka ƙaraso filin tashi da saukar jirgin, The plane is ready to take off. Tun daga bakin wajan securities ɗin suka firfito tare da mamaye motar Sheikh, Umar-khan ya buɗe murfin motar ciki. Sauri Sheikh Aliyu Haydar ya fito a wannan lokacin ma kansa a ƙasa, yana hawa strains ɗin jirgin Saif-Wazir na biye dashi, sai Umar-khan wanda ya ɗan tsaya yana amsa kiran Father. Cikin damuwa Umar-khan ya ce "Kayi haƙuri Father, Sheikh ba zai taɓa aikata hakan ba, zargi ne kawai ake masa, yanzu jirginmu zai tashi be patient Father" tsaki Father yai ta cikin wayar kafin ya kashe. Yana shiga jirgin aka bawa Pilot daman keta hazo, a hankali jirgin ke zagayawa a ƙasan kwalta ya jima a haka kafin ya kete zuwa sararin samaniya.

Jeniyar motocine suka tabbatar da Father Sheikh Aliyu Haydar ya ƙaraso gida Nigeria, da sauri ya miƙe daga zaunan da yake yana zaga haɗaɗɗan parlon gidan, tare da jiran shigowar Sheikh ɗin. Da mamaki Umar-khan ke bin ƴan jaridu da kallo, daga na gidan Redio, T.v, media. Abin har yai tsamari haka yana da tabbaci Sheikh ba zai taɓa aikata abin da ake tuhumarsa ba, zargi ne kawai. A nutse ya sakko da ƙafarsa daga cikin motar kai tsaye ƙofar shiga cikin gidan nasu ya nufa, Umarninka da Saif-Wazir na karesa daga ɗaukan da ƴan Jaridu suke masa. Sako ƙafar da Sheikh Aliyu Haydar yai cikin parlon yai daidai da lokacin da Father yake sauke masa wani lafiyayyan mari wanda yasa Umar-khan saurin juyawa ya fita, domin ba zai iya jure ganin ana cin zarafin babban mutum akan idanunsa ba kamar Sheikh Aliyu Haydar, Saif-Wazir Hawayen da yake maƙalewa ne suka sakko masa, da sauri ya karawaw Umar-khan baya. Cikin faɗa da tsawa Father ya ce "Ka kyauta Aliyu Haydar, ashe wannan dalilin ya hanaka auren tsayin shekaru talatin da huɗu? Ka yaudareni kaci amanar Musulmai kana fakewa da karatun addininka kana lalata yaran mutane a makarantar Jami'ar Madina?" Har wannan lokacin kan Sheikh a sunkuye yake banda cukurkuɗe Jallabiyar jikinsa da yake da hannu babu abin da yake. Father ya girgiza idanunsa cike da hawaye ya ce "Ba shakka biri yai kama da mutum, tunda nake baka taɓa zuwa wajena kace Father na zaɓi yarinya ina son aurenta ba,You betrayed me Aliyu, you deceived me as your father" Ya faɗa yana saukewa Sheikh wani marin cikin tsawa ya ce "Talk Aliyu, kayi magana ka amsa mini Sheikh..!!!" Father ya faɗa yana Girgiza kafaɗar Sheikh. Ɗago kai Sheikh yai bakinsa na rawa laɓɓansa na karkarwa alamar yana son cewa wani abu, amma sam ya gagara sbd rashin iya magana da bai ba. "Ban damu da duk yadda zakai magana ba Aliyu, a yanzu ba zanwa ƙinƙinarka uzuri ba ka bani amsa da gaske wata kaiwa ciki?" Shaaa hawaye ya sauka fuskarsa Sheikh sbd yadda yake son furta wani abu ya kasa. Matsawa ya yi kusa da Father yana buga hannunsa a cinya a hankali hannu na rawa ya miƙa tare da kama kwalar rigar Father, idan ya ɓalle bottle ɗin gaban rigar Father sai ya mayar rufe, da ƙarfi ya buga ƙafarsa yana riƙe wuyan Father hawaye ba zubu masa cikin ƙinƙina ya ce. "Ya....ya.... ya Allah..." Ya ƙare mgnar cikin ƙinƙina yana mai buga ƙafarsa a ƙasa.

Share as so much as you can💋... Not Edited👏🏻

#Sarautar marubuta
#True life story

*🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Arewabooks@Nimcyluv*_
Follow my account👇🏾
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Chapter 10 · 0% Book details