← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 55

Sashe 38

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dawo da ita baya ya yi tare da zaunar da ita a ƙasa wajan ƙafafuwansa, yana mai sakin hannunta da sauri. Tamkar wacce take gane abin da shirun nasa yake nufi haka ta zauna waje guda taƙi yarda ta ɗago kanta kamar yadda yasu sbd ya fahimci abin da yake tunani.
Yasan har abada indai tana cikin wannan yanayin to ba zata taɓa kallon cikin ƙwayar idanun shi ba, sai dai idan marasa kunya ne suke tattare da ita.. hannunsa daya riƙe nata ya dunƙule waje guda a haka Mother ta fito sanye da duguwar riga ganin Yaa Sheikh a main parlour da sassafe ya bata mamaki, idanunta akan shi kana ta zame zuwa kan Halisa dake zaune kusa da ƙafar shi ta dama. Da mmki tana zama ta ce "lafiya dai Haydar? fitowa da safiya, Halisa fa?" Ta tambaya tana kallon Halisa elxty yadda Yaa Sheikh yake abu lokacin yana yaro haka yanzu Halisa tayi. Ya buɗe idanun shi yana ajjiye carbin hannunsa cikin kamilalliyyar muryarsa ya ce. "Mun tashi lafiya Mother?" Ta saki murmushi tana faɗin "Allahamdulillah Haydar, Halisa fa?" Ya ƙara ware idanu yana kwaɓe fuska alamar tambayar batai masa ba, kamar zai share ya numfasa kaɗan ya ce.
"Wafa?" Mother ta ce "Meya fito da Halisa da wannan safiyar kuma gata kusa dakai kamar bata da lafiya?" Ya jima yana tunanin amsar da zai bawa Mother baya ƙarya baya kuma faɗin abin da bashi da tabbacin sai ya yi shiru Mother ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Black tea ko? Bari na kawo maka,ka jira ina son magana dakai" ya jinjina kai. Mother na tafiya ya juya kansa zuwa inda Halisa take zaune a hankali ya miƙa tattausan farin hannunsa mai taushi ya ɗora saman goshinta.
Zabura tayi zata gudu ya riƙe kan da kyau, sosai yaji kanta ya ɗauki zafi yana harbawa. Ya jima riƙe da kan yana ɗan murza babban yatsar shi a tsakiyar goshinta kafin yaji taja duguwar ajjiyar zuciya tare buɗe idanu.
Ya zame hannun shi daga kan, itama ta kasa kallon shi ta kuma kasa motsawa.
Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe jiri na ɗaukanta ta nufi part ɗin su Maimoon domin anan ne take kwana yanzu. Barin ta parlourn ya yi daidai da dawowar Mother daga kitchen, bayan ta zauna tare da tsiyayawa Yaa Sheikh black tea ɗin tare da 2 spoon na honey yana tiriri ta miƙa masa.
A nutse yake sha ganin ya kusa shanyewa ta kalle shi ta ce "You need more? with chips or kunnu?" Ya jinjina kai alamar "Eh" kitchen ta shiga not too long ta dawo ɗauke da tray, Spoon ɗin ya ɗauka ya fara cakar chips yana taunawa a hankali, haka kawai jikin shi ya bashi ana kallon shi gently ya ɗago kai da sauri ta koma ciki tana dafe ƙirji, ya girgiza kai domin idanunsa sun riga da sun ganta tuni.
Mamakin cin abincin na Yaa Sheikh yau ya kama Mother tana zaune tasan ko tayi magana ba zai fahimta ba, sai da ya goge baki da tissue kana ya zaro Aswaq daga cikin aljihu ya fara yi.
"Ina son yin magana da kai ta fahimta Aliyu" ya maida hankali sosai akan Mother ta gyara zama ta ce.
"Halisa bata da kowa, bata da wanda kareta ya kuma ja ragamar rayuwar ta, ko da baka san yaya akai tazo gidan nan ba, amma ka tuna cewa matar kace, ban damu da kai mata kallon mata ba, wannan deal kai da Abbanka, amma ka zama garkuwa a gare ta don Allah don Annabi ba danni ba Aliyu" ta haɗe hannaye biyu alamar roƙo a gare shi, a taushashe ya kama hannun Mother duk biyun, ya jima kafin ya ce.
"Fiye da yadda kike zato, al'ƙawari ne" tai murmushi ta ce "Allah ya yi maka Albarka Malam, tare da matanka, kayi ƙoƙarin sauke hakƙin ko wacce mace a cikinsu, kada ka tauye na wani ko fifitawa" ya jinjina mata kai yana miƙewa tsaye.
Kai tsaye bedroom É—insa ya nufa tare da É—aukan system ya shige Library É—insa, wasu muhimman ayyuka ne dashi gashi yana son tattara komai wajan Saif-wazir tunda da Umar-khan zasu koma, É—alibai na can suna jiran shi da gidan marayunsa.
Misalin 10 kowa yana zaune akan dinning ana dinner Father ya ajjiye Spoon ɗin hannunsa ya kalli Zahrah ya ce "Aliyu ya faɗa miki 12 jirginku zai tashi ko?" Ganin Idanun Mother yasa Zahrah faɗin "Eh Father, nama gama shirya kayana" Jadda ta fashe da kuka tana share majina da gefen zani ta ce "Ubangiji ya bawa Malam haƙuri, an haɗa shi da wacce tafi ƙarfin shi, na rantse uwata ta haifan ban taɓa ganin ƙatuwa budurwa irinta ba, an bashi sa'ar babar shi da kaɗan fa na girme mata, gaskiya dole Malam ya ƙara aure zan nemi Hakimi da kai na ai shela a sama masa mata ko cikin masarauta ne" gaban Zahrah ya faɗi sosai kishiya za ayi mata? To ai Yaa Sheikh shi da wata mace har abada,da ita zai ta rayuwa da daɗi ba daɗi,idan har tana raye babu wacce ta isa ta shigo cikin gidanta, ba zata taɓa haɗa Mijinta da wata ƴa mace ba.
Father ya ce "Bayan auren da yake dashi?" Jadda ta ce "A'a zan maka Allah ya isa Aliyu, tun nazo gidanka kaji na kulaka? Nifa ba zan yarda Malam ya zauna da ɗirkekiyyar mace kamar durunar ruwa ba, ko ni bata ban sha'awa ba balle namiji, kana kallon ƙirjin kamar an zuba kwalta a titin gwammaja, dole ya auri ƴar ƙarama wacce zai mure ƙuruciyarta ai Alsulhu khair" bakin Halisa na rawa ta ce "To ai nima matar shi ce kuma ƴar ƙarama ce ni....," Kafin ta ƙarasa maganar Mother tayi saurin rufe mata baki, faɗan da Jadda kewa Father yasa babu wanda yaji maganar sai Maimoon.
Baƙin ciki ya cika Zahrah jin daɗinta ɗaya babu Yaa Sheikh a wajan. Cikin makirci Zahrah ta fashe da kuka tana zubewa gaban Jadda ta ce "Don Allah kiyi haƙuri Jadda, kada ki rabani da mijina yana so na, ina son shi" Jadda tai mitsi mitsi da idanu tana riƙe haɓa ta ce "Mai ƙarya aƙona shi a wuta, nifa na rarrashi Malam na bashi baki akan ya aureki da ƙyar sai dana zubar da hawaye, nace zanbi duniya kawai idan bai yarda da aurenki ba, shi ne zaki ce yana son ki?" Da sauri Zahrah ta nufi part ɗin ta, sbd gab take da yiwa Jadda rashin mutuncin wallahi.
Jadda ta ce "To ai kaga nayi mata bayani cikin sauƙi,ta fahimta da faɗa nai mata sai ta ƙulla ce ni, ai Alsulhu khair"
"Ai kam dai munga Sulhu, bamu sani ba ko zai zama alheri" cewar Auta Fattoumah. Jadda ta ce "A'a kowa ya yi ta kansa, bana shiga abin da bai shafan ba, amma fa na girgiza a bawa mutum auren sa'ar uwar shi?"
Halisa ta ajjiye Spoon É—in hannunta idanunta ya yi jajir kalmar..
_“Yana so na, ina son shi”_ ya shiga yi mata yawo a cikin kunne. Ta miƙe a hankali tare da nufar ɗakin su Maimoon. Tana zuwa Mother ta biyu bayanta..
Ta kasa kallon Mother bakinta kuma ya ƙiyin shiru ta ce. "To yaushe zan faɗawa kowa ina da aure kuma Malam ne mijina?"
Mother ta girgiza kai ta ce "Ba yanzu ba, inda kika faɗawa wani to mun ɓata kuma zance Yaa Sheikh kada ya saki makaranta"
Da sauri tana zare ido ta ce "A'a ba zan faɗa ba, amma zan dinga ce masa mijina ko? ko Baffa?" Mother ta rasa me zata ce, surutun yarinyar baya sarrafuwa idan har ya fito to dole ta furta.. "duk yadda kika gani, amma idan kika ce miji ai Zahrah zata gane, kice Abba Sheikh" bayani ta ƙara yi mata cike da hikima na zaman rayuwa, da kuma wasu muhimman abubuwa akan Yaa Sheikh ɗin.
"Maza ta shi kije Maimoon ta ƙara yi miki saloon" ta miƙe tana cewa "To" sai da taje bakin ƙofa zata fita ta tsaya tare da kallon Mother ta ce.
"Amma idan naje can Madina zan iya faÉ—awa kowa ayi mini aure ina da miji?" Mother ta tafe kai tare da faÉ—in "Na shiga uku"..
Zahrah ce ke waya da Surry ta ce "Wallahi Surry ko da wasa aka bawa Yaa Sheikh auren wata sai na kasheta, ina da tsananin kishi akan abin da nake so, balle mutum kamar Yaa Sheikh wanda banyi tunanin zan same shi matsayin miji ba" Surry ta ce "Tab, sai ki san yadda ki kai kika tare da mijinki idan kuka tara zuri'a babu mai rabaki da shi ai" Zahrah ta ce "You're right jirginmu zai tashi, yama sunan maganin dake saka mutum feelings in 5 minutes?" Surry ta faɗa mata sunan maganin ta ɗora da faɗin "Amma dole Yaa Sheikh ya gane bake bace" murmushin mugunta Zahrah tayi tana girgiza kai ta ce "Idan kuma yana cikin maye fa?" Surry ta zare ido ta cikin wayar ta ce "Bugar dashi zaki? Kada ki cutar da ƴar mutane yafi ƙarfin ta ba"
Chapter 38 · 0% Book details