← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 55

Sashe 17

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya ka kwana? da ciwon kan?" Rufe ido ya yi tare da buɗewa alamar "Allahamdulillah" Momi A'isha ta amsa gaisuwar Sheikh ɗin wacce ya yi mata ita cikin In-ina, tea ta haɗa masa mai zafi ta zuba 2spoon na honey ta juya kaɗan tare da bashi. Amsa ya yi a kame yake shan tea ɗin yana sauraran maganar Abba Hakimi da yake ce masa "komawa Madina ba yanzu ba, kada ya fara tunanin hakan" sanin ba zai iya ja da maganar Abba Hakimin ba yasa ya miƙe yana ajjiye cup ɗin hannunsa, Ishaq-hakim da Saif-Wazir suka miƙe tare da bin bayansa, wata farar mota ya shiga mai Sheikh no 5 yana shiga driver ya ja. Ishaq-hakim da Saif-Wazir kowa ya shiga motarsa suka nufi S.A.H BANK.
tun kafin ya Ƙarasa cikin bank ɗin wanda ya kasance mallakinsa ma'aikatan bakin Sheikh Aliyu Haydar bank suka shiga mutuwarsu ƙwarai. miƙewa ake ana gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu har ya shige wani baban office. Wunin ranar Sheik cikin duba files and Ducoments yake.
3:30 yana ƙoƙarin barin Office ɗin saƙon father ya sauka Wayarsa. Da fararen idanunsa yake bin message ɗin da kallo yana mamakin yanzu kuma kiran gaggawar mene?. Da wannan tunanin ya shiga mota Driver ya ja suka nufi unguwar su Sheikh.
Tun a harabar gidan ya san akwai matsala domin kai tsaye idanunshi ya sauka akan motar Abba Hakimi data Yaya Halima sai ta Uncle Haroon.

Ƙamshin turarensa ya bayyana zuwansa, Mother dake zaune saman Kujera yana kaɗa ƙafa ta kalle shi kafin ta ɗauke kai, Uncle Haroon ma kallon Sheikh ɗin ya yi, a kame ya ƙarasa kusa da Abba Hakimi ya zauna yana ɗauke idanunshi daga kan jama'ar daya rasa meeting ɗin me ake.

"Tun da Allah ya kawo shi sai aji ta bakinsa, amma Sheikh ya shige lokacin da za a yi masa auren dole, a baya ba ai masa ba balle yanzu?" Yaya Halima ta furta cike da jin haushin father. Shi ma father da zuciyarsa ke kusa ya ce.
"Bashi da amfani, domin ba zai faɗi abin da kowa ke buƙata ba, na daɗe da sanin cewa Aliyu shi ne ƙaddarata, shi da yake namiji wanda ya kamata ya tsaya kan dukiyata amma ya kasa hakan, duk mutanan da suke buƙatar contract daka gareni idan har suka ji yadda Aliyu ke banzar maganar shi suke contract In-inar Aliyu ta ja mini asara mai yawan gaske, don haka ni bashi da amfani a gareni" sai a yanzu suka fahimci rashin jituwar da babu tsakanin father da Aliyu cikin ladabi Abba Hakimi ya ce "Baka yarda Ubangiji ya ɗorawa Aliyu wannan larurar ba? kenan baka alfahari da Aliyun matsayin ɗa?" Cikin sauri Father ya ce "Aliyu bai taɓa yi mini rana ba, to akan me zan yi alfahari da shi? Idan yana so mu shirya dole ya daina wannan In-inar ko kuma ya yi aure cikin satin nan"

"Aliyu akwai wacce ka ke so ne?" Sai a lokacin Sheikh ya kalli Uncle Haroon yana runtse idanunshi zufa na yanko masa a ƙoƙarin shi na ganin ya yi magana babu In-ina amma ina ba zai iya ba ƙaddarar shi ce hakan.
Cikin fitar hayyaci yana rirriƙe jikinsa da kyau tare da buga ƙasa da hannun kujera ya ce "ba...ba ba bana son son kowa uncle.. ba ba bazan iyyyya zama dadda da mace ba" shiru duk sukai baƙin ciki ne kuma ya hana mother magana. Father ya ce "Ok good a Sbd haka ka shirya zama da Zahrah ƴar gidan babban aminina, cikin satin nan za a yi aurenku kai da Zahran babu fashi" miƙewa Mother ta yi cikin faɗa ta ce "Wallahi Aliyu kayi kaɗan ka saka Sheik ya auri wannan Yarinyar da ban amince da tarbiyyar ta ba, me Sheikh zai da ita? Yarinyar da take kusan sa'ar shi kaɗan ne babu ta girme shi ba? duk shekarun da Aliyu ya yi babu aure sai kuma ya ƙare wajan tsohuwa, ban amince ba kuma ban yarda ba, ka bawa Aliyu duk wacce kaga dama amma ban da Zahrah" murmushi father ya yi ya ce "Idan har ni ne uban Aliyu ba wani ba? Ya zama dole ya auri Zahrah idan kuma bani ne mahaifinsa ba sai ki bashi wacce kikai niyya Barrister Maryam" hawaye ya cika Idanun Mother ta ce "Oh yanzu kuma sheganta Aliyu zaka fara bayan zarafinsa da ka ke ci akan larurarsa?" Banza father ya yi mata. Uncle Haroon ya numfasa ya ce "Engineer Aliyu Wannan bai kamata ba, idan kana so Aliyu ya yi aure,Let him choose the woman he wants to marry himself, ka sassauta yanayin da ka keji game da Aliyun" Father ya ce "Abu ɗaya ne zai kawo Shira tsakanina da Aliyun shi ne auren shi da Zahrah idan bai amince ba yaje na zare hannuna daga Lamarinsa kuma ya zare sunana a matsayin Uba" Dakawa Father tsawa Uncle Haroon yai ya ce "Wai Aliyu wanne irin banzar magana ce kake haka? Ni da kai na zan iya samawa Aliyu matar aure, ka daina ganin kai ne ubansa ni ma uba ne a wajansa, ga kuma babban Uba hakimi duk mun isa mu tsayawa Aliyu, ka daɗe baka cire hannunka ba, kuma wallahi ka sake na rabaka da Aliyu ka rabu dashi kenan har abada" Girgiza kai Abba Hakimi ya yi ya ce "Ba za a yi haka ba Haroon, haƙƙin Aliyu ne samawa Sheikh matar aure a barshi ya aura masa Zahrah Allah ya sa albarka,kada ka damu da Sheikh nasan zai amince" miƙewa Sheikh ya yi cikin zafin e da kutuwar zuciya irin ta kurmaye Aliyu ya fara faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, idanunshi gaba ɗaya ya rufe Innar ta hana ya ji abin da yake faɗa, idan kuma ya fara faɗa babu wanda ya isa ya tsayar da shi daga faɗan da yake. Saukar wani zazzafan mari da Sheikh ya ji a saman kamilalliyar fuskarsa ya sanya ya yi saurin rufe idanunsa Father ya nuna Sheikh ya ce "Ni kake ɗagawa murya Aliyu? Ni sannu kuturu uban ƴan zuciya daman zuciyar taka nake buƙata auranka da Zahraan kuma babu fashi" ƙwafa Sheikh ya yi domin baya iya riƙe kansa idan zuciyar ta motsa uban kowa sai ya san babu lafiya a gidan. Wuyan rigar Father ya riƙe da kyau zufa na mamaye dukkan goshinsa a wannan karan bai buga ƙafarsa ba amma tamkar zai ɓalla wuyan rigar haka ya riƙeta da kyau cikin huci da faɗa ya ce "heee na... na na amince amma ka ka ka tabbatar mutuniyar kirki ce" Father da yaji shaƙar Sheikh ɗin har ransa ya ce "Idan kuma ba ita bace ba fa Aliyu?" Sheikh ya girgiza kai idanunshi ya yi jajur ya ce "Haaaaa ɗakkkkkk" yana faɗin haka ya saki Father tare da barin gidan baki ɗaya...

We're still in free pages🫰🏽 Littafi nan na kuɗi ne, a koda yaushe zan iya datse free pages. Salo na musamman biya 500 ta Wannan acct ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616.

*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Nimcyluv sarauta_*

12....
Bayansa suka bi da kallo ganin yadda ya fice a fusace. Father yaja numfashin wahalar da ƙyar kafin ya ce "Irin wannan ban zan yaron za a bawa mace mai ƙarancin shekaru? Ai ko Zahrah sai dai ta yi haƙuri da shi" Mother zatai magana Yaya Halima ta hanata ta hanyar danne hannunta tare da girgiza mata kai. Ganin ba wanda ya sake cewa father komai ya juya zuwa upstairs. Uncle Haroon ya kalli Abba Hakimi ya ce "Afuwa ranka ya daɗe kayi haƙuri da halin Engineer Insha Allah komai za yi daidai, Jadda ba zata barshi ya aikata hakan ba, I'll talk to him" murmushi Abba Hakimi yai yana faɗin "Me ne na haƙuri Haroon? Sheikh ɗan sa ne ba wanda zai yi jayaya da hukuncin da uba ya yi akan ɗan sa, idan hakan zai sa shi farin ciki da amincewa da Sheikh a barshi ya yi" "She's 32 years old Hakimi, tayi wa Sheikh girma ba zata iya yi masa biyayya ba, babu tarbiyya a wajan yarinyar nan na jima da saninta" Mother ta faɗa cikin damuwa. Yaya Halima ta ce "Barrister ke uwa ce a kullum, addu'a kawai za kibi Sheikh da shi, addu'ar ki zatai ta zagaya rayuwarsa sai kiga albarkacin haka Ubangiji ya daidaita tsakani kuma ya shirya yarinyar, ba a jayaya a cikin lamarin aure" Uncle Haroon ya ce "Ki bar Barrister ta faɗi abin da yake ranta, idan akwai wanda yafi sanin halin Sheikh da raninsa to ita ce mai biye mata shi ne Hakimi, babu kyautatuwar a zuwa Engineer idanu yana abin da ya ga dama, idan baya ra'ayin Sheikh a rayuwarsa sai muyi yarjejeniya mun ashe sa mu suke sunan shi daga jikin na Aliyun" miƙewa tsaye Abba Hakimi ya yi yana gyara zaman alkyabbar jikinsa cike da nutsuwa ya ce. "Wannan shawara ta Haroon ba dani ba, ban taɓa jin inda aka raba uba da ɗana ba, lokaci ku barshi ya bayyana mana komai" yana faɗin hakan ya yi waje yana dogara sanda. Uncle Haroon ma ya miƙe tare da yi musu sallama.
Bayan tafiyar su Yaya Halima ta kalli Mother ta ce "Barrister ki nutsu kada kiyi jayaya da hukuncin da uban yaron nan ya zartar ni ina ji ajikina akwai wani abu ɓoyayye a ƙasan auren mu amince da hakan" ƙwafa kawai Mother ta yi tana girgiza ƙafa kafin ta kalli Yaya Halima ta ce "Kin san Allah Yaya ko zan amince da auren nan sai dai Sheikh ya auri mata biyu?" Yaya Halima ta waro idanu sosai ta jima tana kallon Mother kafin ta numfasa ta ce "Tab, mata ɗaya ya zata ƙare wajan Sheikh bare mata biyu? Ai Wallahi mantawa zai yi da zamansu a gidan"
Chapter 17 · 0% Book details