← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 55

Sashe 44

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kasa ƙarasa maganar ya yi sbd gemunsa data kama tana cewa "Yasunan wannan abun? Kuma da gaske ni matar malam ce, naje na faɗawa Ummul nace kace mini matar malam?" Ya lumshe idanunsa na wani lokaci kafin ya buɗe su a kanta tare da ɗora hannunsa akan nata data riƙe gemunsa ya zare yana girgiza mata kai.
Zata sake yin magana ya miƙe tsaye yana nufar hanyar bedroom ɗinsa dole sai ya sauya kaya gaba ɗaya ta goge masa maiƙon hannunta a jiki, da sauri ta biyo bayansa ta ce "To baka faɗa mini sunan wannan dugun abin ba, kuma waye zai kaini makarantar ina son zama babbar mace" ya juya tare da kallonta a nutse yana mai mamakin surutun ta, yana da masaniyya akan yadda take amma bai ɗaukan surutun ya yi girma da tsayin haka ba. Bai ce mata komai ba ya juya yana mai sakin murmushi shirmanta a karo na farko da suka kasance tare domin sauran duk baɗini yake ganinsu. Ummul na kitchen Halisa ta dawo ta kalleta cikin kyakkyawan lafazi ta ce "Ba dai haka kika je da hannunki ba?" Ta kalli hannun kuma ta kalli Ummul ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na goge masa" Ummul tai shiru daman tasan za a rina, kuma sam ba tayi mamakin hakan ba. Maid Suhaima ta ce "Wa kika gogewa?" Da sauri Halisa ta ce "Malam, nikam ya sunan wannan dugun abin na fuskar shi? naji yana da laushi aradu" Ummul ta dafe kai da sauri kuma ta miƙe tsaye tana kama hannun Halisa suka nufi can part ɗin Ummul ɗin.
Bayan sun shiga Ummul ta kalli Halisa sai kawai tai murmushi kafin ta ce "jeki wanke hannun ko?" A sanyaye ta ce "To" ta nufi bathroom ta wanke tas tare da wanke bakin ta fito har lokacin Ummul na zaune tai shiru tana kallon hanyar toilet ɗin, ganin yadda Ummul tai shiru yasa Halisa faɗin "Ummul" ta buɗe idanu ta ce "Kin gama? Lokaci na tafiya zaki buƙaci abinci a can, lunch box naki yana cikin mota" suka fita Main parlour daidai nan Zahrah ta fito da kayan barci da alama ko sallah ba tayi ba, balle ashirin zancan wanka tabi Ummul da kallo ta ce.
"Wace ke? daga ina bana hana ana shigowa kai tsaye ba, ba tare da permission ba, ke kuma jeki gyara mini bed ki haÉ—a mini ruwan wanka" Halisa ta ce "makaranta za a kai ni, idan na dawo zan haÉ—a miki sai Kiyi wankan" Ummul ta danne dryar data zo mata. Da mamaki sosai Zahrah ta ce "School? Da izinin waye kuma? babu wata makaranta da zaki, baki zo gidan nan dan kije makaranta ba" ta faÉ—a tana fisgo hannun Halisa daga kusa da Ummul.
"Ke kuma da kika tsaya kina ƙwalala mini idanu da alama kina da masaniyya, tell me waye zai kai ta makarantar"

"Ni ne" ya faɗa a taushashe yana mai fitowa daga inda yake tsaye, yana sanye da sabbin shiga saɓanin ta ɗazo, farar dakakkiyar shadda ya sanya mai jamper da babbar riga, ya ɗora hirami ɗaya a kansa ɗaya kuma a kafaɗa..
Ta saki Halisa ta nufi inda yake ta ce "My Excellency amma daga zuwa sai batun makaranta, kuma ya kamata a faÉ—a mini, ni bani da ra'ayin yarinyar nan tai makaranta" Halisa ta tura baki tana mai jin haushin yadda Zahrah ta wani matsa kusa da Yaa Sheikh haka kawai taji zuciyarta ta cunkushe, amma hakan bai hanata cewa. "Amma ai Dada tana da niyya ko Anti, da izinin zani makaranta ta baki...." Cikin rawar murya Zahrah ta ce "Oh ok it's ok you can go, but waye zai kai ta?" Sai a lokacin Ummul ta ce.
"Umar-khan, kafin driver ya fara kai ta, Aliyu yana da lecture da ɗaliban shi, zai iya magana" Ummul ta faɗi haka ne domin Zahrah ta bawa Yaa Sheikh hanya. Haka kurum Zahrah taji sha'awar kasancewa da mijinta ya bijiro mata, musamman da ƙamshin Roja ke ƙara narkar da zuciyarta, Yaa Sheikh na musamman ne, idan zaka kalli cikin idanun shi yayin magana to ba zaka taɓa yi masa ƙarya ba, ɗaya daga cikin baiwar shi kenan. Babu kunya ta rungome shi a gaban Ummul tana faɗin "Am going to miss you My Excellency back soon please" gani sukai Halisa ta juya da sauri zuwa part ɗin ta, Ummul ba tai magana ba. A hankali ya zame jikinsa daga na Zahrah ta ce "Bari naje nai wanka da Sallah bye" Ummul ta kalli lokacin 7 harta gota ba dai sallar asuba ba, sai dai walaha.
Bayan shigewar Zahrah Yaa Sheikh numfasa yana mai gyara murya a kasalance ya ce.

"Mun kwana lafiya,
Ummul?" Ummul ta ce "lafiya lou, kaga Æ´ar rigima ko? kamar kuka naga ta nayi?" Ya saki fuska daga kamewar da ya yi shima yana duba lokaci a diamond rolex watch É—insa.
"Aje a duba, kin san hali tun ba yau ba" tai murmushi ta ce "Wallahi fa" ta nufi part ɗin Halisa shi kuma ya goya hannunsa a baya tare da tsaiwa a tsakiyar parlourn. Kwance Ummul ta samu Halisa ta cire baby hijab ɗin jikinta sai kuka take kamar ranta zai fita. Ummul ta zauna cikin sakin fuska ta ce "Matar Malam lafiya? Wani abun ne? ko wani gurin ke miki ciwo?" Kuka kawai take taƙi magana tamkar zata shiɗe haka take kukan. "Faɗa mini mene? ke dawa" ta miƙe zaune cikin shassheƙar kuka ta ce "Ummul Dada zani, ni na fasa zaman wajan Dadata zani ki saka a bayar dani" Ummul ta ware idanu da kaɗuwa sosai ta ce.
"Yanzu Matar Malam ina ke ina zuwa gida, keda kika zo bautar Ubangiji? Maza tashi akai ki makarantar ga shi can yana zuwa kin san kuma akwai inda zashi" idanunta ya yi jajir hawaye na zuba daga cikinsu ta ce "banso, na fasa makarantar ni rugarmu zan koma" yin duniya taƙi yarda Ummul ta ce "To dai na kukan bari na faɗa masa" ta juya tana mmkin sauyin da yarinyar ta samu lokacin gudu, me akai mata me kuma ya sauya mata tunaninta daga sha'awar zuwa makarantar.
A tsaye Ummul ta same shi, bai kalleta ba amma tunaninsa da hankalinsa na kanta ta ce. "Kuka take sosai, wai bata son makarantar kuma a bayar da ita can ruga" maimakon ya fita sai ya juya zuwa part ɗin shi ba tare daya amsa maganar ta Ummul ba. Ta gane yaran kuraman nashi dan haka ta ƙarasa juyawa zuwa sashin na Halisa. kanta kife idanunta data rufe su take hango rungumar da Zahrah taiwa Yaa Sheikh, kuma bata manta maganar da Maimoon ta faɗa mata ba, idan kana son mutum da zarar wata macen ta raɓesa zaka ji kishinsa, ita a yanzu ta kasa fahimtar me ya sa taji komai ya dameta zuciyarta babu daɗi ne? Da wannan tunanin Ummul ta dawo ɗakin tare da ce mata "Ki saka hijab ɗin, kije Abban naki yana kira zai mayar dake" ta kalli Ummul sosai amma bata ce komai ba, hijabin a hannu ta nufi part ɗinsa. Ummul ta girgiza kai tana sakin murmushi kawo yanzu ta gama gane abin da ke damun Halisarta ta fahimci zallar rigima da shagwaɓa ce ke damunta akan dalili mara toshe.
Yana zaune hannunsa riƙe da azkar yana dubawa yaji saukar siririyar muryarta tayi sallama, amsata ya yi a rai, yana mai ɗago kansa tsaye ya ganta taƙi ƙarasuwa sai cukurkuɗe hijab ɗin hannunta take. Shi bai fiya son yin surutu ba kwana biyu kuma tana neman sashi, gashi kamar ciwon kanshi na neman ta shi. Ajjiye azkar ɗin hannunsa ya yi, tare da miƙa mata hannunsa alamar tazo, kanta a ƙasa ta matsa inda yake zata zame a ƙasan ƙafafuwansa ta zauna a ƙasa ya kamo hannuna tare da zaunar da ita a gefen shi yana kafeta da idanunsa. Kafin ya ce komai ta fashe da kuka sosai tana jan numfashi, ya tallafo haɓarta da hannunsa mai taushi idanunsa na yawo a fuskarta.
"Ya akai?
Ke dawa?" Ya faɗa yana mai sauke numfashi tare da jan jikinsa zuwa jikin kujerar. Muryata na rawa ta ce "Abba gida zani, ni Dadata zan koma" ya lumshe ido kana ya buɗe a sauƙaƙe cikin son dakatar da kukan dake neman fasa masa kai ya ce. "Karatun fa? Ban son rigima" ta girgiza suna haɗa ido ta tura masa baki ta ce "Shi ma banso, kuma..." Sai kuma tai shiru tana ɗauke kai.
Kallon yadda fuskarta tai jajir ya yi sosai duk ta birgita kanta sbd rigima, he's still holding her face ya fesar da iska ya ce.
"Gida kike so? Ta É—aga masa sai kuma ta ce "Eh wajan Dada zaka kaini kaji Abba"
Chapter 44 · 0% Book details