← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 55

Sashe 43

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"You can go,
Ina buƙatar gyaran part,
With food" shi ne abin da ya rubuta mata a jikin Jotter ɗin, ta duba kenan dole mutum ɗaya ya tsaya, ita gasky ba wani gyaran ɗaki da zata iya, bayanta ciwo yake idan ta yi,kuma bata saba ba. Fita tayi ta samu Halisa a main parlour a kwance barci ya ɗauke ta tunda ta farka da asuba bata koma ba, gashi tai aiki ta gaji sosai bata san barcin ya ɗauketa bama sbd kallo take. Tana zuwa ta fisgo ƙafar Halisa zuwa ƙasa ta faɗo daga kan kujerar, a tsorace ta ce "Hande en boni me na yi Anti?" Zahrah ta ce "Ai hutu kika samu kenan? Ai babu ranar da zaki huta, zaki ta wahala har abada, kije ki gyara part ɗin Yaa Sheikh, ki kai masa lunch zan fita unguwa" kanta a ƙasa ta kasa cewa komai, tana zaune a parlourn Zahrah ta fito cikin wata duguwar riga ta yana mayafi hannunta riƙe da hand bag, kamar yadda Zahrah bata kulata ba itama bata kula ta ba. A compound ta ci karo da Umar-khan yana fitowa daga mota hannunsa riƙe da takarda. Ya ce "Evening" ta share sa, ta nufi wajan wani da alama shi ne drivern gidan.
Kai tsaye Umar-khan gidan ya shige ya samu Halisa zaune kanta a ƙasa tana gyangyaɗi ya ce "Matar Malam" tai saurin jan mayafin abayar ta ɗora a kanta tana yi masa murmushi ta ce "Ina yini?"
"Lafiya, barci a nan kuma? Yaa Sheikh ɗin yana ciki?" Ta ce "Ban sani ba" ya jinjina kai ya ce "Ok bari na duba, kije ki kwanta mana" ita dai ba tace komai ba ya nufi Part ɗin Yaa Sheikh barci yaci ƙarfinta, ta kwanta nan ƙasan carpet.
Umar-khan ya zauna bayan ya gaida Yaa Sheikh ya ce "Na cike komai na makarantar, gobe aka bada izinin ta fara zuwa, Mother ta ce komai cikin gaggawa take buƙata" ya miƙawa Yaa Sheikh file ɗin takardun Halisa bai amsa ba, sai tsare Umar ɗin da idanu da ya yi, Umar yana fahimtar shirun na Yaa Sheikh hakan ya sa ya ce.
"Al Aqeeq International School for Girls, Safiya Opens 7:30 ita ce makarantar" Yaa Sheikh ya jinjina kansa tare da miƙewa ya shigewa ɗaki. Wajan mintuna goma suka fito tare da Umar-khan wata Milk ɗin jallabiya ce a jikinsa, sai golden ɗin Alkyabba daya ɗora a kan jallabiyar, ya fito a babban malaminsa sai ƙamshin Roja yake bazawa, yana fitowa idanunsa ya sauka akan Halisa wacce ta cure waje guda tana barci, ya tsaya cak tare da kallon Umar-khan, Umar ya nufi ɓangaren Ummul babu jimawa suka dawo tare, Ummul ta kallesa ta ce "Malam za a fita ne?
Ba kaci abincin kirki ba?" Ya É—an É—auke kai zuwa hanyar fita yana faÉ—in. "Sanyi zai illata ta, a sauya mata waje" sai a lokacin Ummul ta lura da Halisa.
"Tom babu damuwa, Allah ya tsare" ta nufi wajan Halisa ta shiga tashinta tare da faÉ—in "Matar Malam, matar Malam" ta buÉ—e ido tana kallon Ummul ta ce "Maza ta shi ki koma É—aki, a kwai sanyi zai kama jikin ki" ta buÉ—e ido sosai ta ce "Anti Zahrah ta dawo ne?" Ummul ta ce.
"Fita tayi ne? ta shi lokacin sallah ma ya yi ai muje ko" har part ɗin Halisa Ummul ta shiga, akan idanunta Halisa tai alwala kana tai Sallah. Ummul ta ce "ƙarfe biyar kizo ɗakina, zan nuna miki yadda ake cikakkiyar sallah, na fara karanta miki Alkur'ani, yanzu ki kwanta wajan ƙarfe 4:30 ki tashi ki wanka ki wanke baki, ki sauya komai na jikin ki, kinji ko?" Ta tura baki sosai ta ce "To wannan duk na mene Ummul" Ummul ta ce "zaki sani ne" ta fice daga ɗakin.
Yaa na fita kai tsaye Al Masjid an Nabawi ya nufa sbd wani karatu da yake dashi na musamman, kuma acan yake son yi Sallah ma, da kuma zaman tattaunawa da za su yi da mahukunta kula da Masallaci harami ana son naÉ—a Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu matsayin limamin masallacin Haramin wanda zai jagorancin sallar Taraweeh da Tahajjud, gaba É—aya azumi saura wata guda ya rage a fara.
Tamkar uwa mahaifiyya haka Yaa Sheikh ya ɗauki Ummul yana ɗaukan minti goma yana magana da ita, tasan kusan komai nasa kuma tasan da yawa abin da Mother bata sani ba, tunda yafi rayuwa a Madina fiye da Nigeria. Sai bayan sallar issha Zahrah ta shigo a gajiye tana tafiya da ƙyar idanunta ya yi jaa, Halisa ta bita da idanu ganin yadda take tafiya kamar yaron da akaiwa shayi. Duk yadda Halisa tasu taga dawowar Yaa Sheikh bata gani ba, barci ya ɗauketa a Main parlour. Ƙarfe 12:30 ya shigo gidan shi kansa a gajiye yake sosai, ganinta a parlourn ya sanya ya tsaya yana binta da idanu, a hankali ya dubi lokaci sai kuma ya shige part ɗinsa.
Kiran sallar asuba ya farkar da ita, da mmki take bin makeken gadon da take kai da kallo, an rufe ta da wani haɗaɗɗan duvet mai ƙamshi ga laushi an kuma rage ƙarfin a.cn ɗakin, ita dai tasan a parlour ta kwanta waya kawota nan? Ko ita ta shigo da kanta.
Ta miƙe ta nufi toilet yadda Ummul ta koya mata haka tayi, tai wanka da ruwan zafi ta shafe jikinta da Vaseline Intensive Care Cocoa Glow Body Lotion.

Shiryawa cikin Abaya ta ɗora hijab a nutse take duba littafan da Ummul ta bata, Ubangiji ya bata fikirar hadda ce, da yawan lokaci ita abu a kanta yake zama, duk wani abu mai muhimmanci bata wasa da shi. Tana zaune taji saukar muryarsa a kunnanta yana data kabbarar sallah, shiru tai bata taɓa tunani muryar shi takai daɗin haka ba sai yanzu. Sallah ta gabatar sannan ta nufi ɓangaren kitchen ta samu tuni sun Bara'at sun fito. 6:30 Ummul ta ce tayi sauri ta shirya za a kaita makaranta, wani tsalle tayi ta rungume Ummul daɗi ya kamata jin za a kaita makaranta abin da take buri a rayuwarta. Ta shirya ta fito tsaf a cikakkiyar ƴar fillonta Ummul na ganinta tai murmushi tana cewa "Kije ki gaida Abban naki" Halisa ta ce "Abba kuma Ummul" ta ce "Eh, uban riƙon ka ai uba ne jeki maza" hannunta ɗauke da yam balls ta nufi ɓangaren shi.
Cikin siririyar murya tai sallama tare da shiga tsaye ta gan shi cikin kyakkyawar shiga mai ɗan kauri sbd sanyin garin da aka tashi da shi, hannunsa goye a bayansa ta ƙarasa cikin da sauri tana durƙusawa har wajan ƙafafuwan shi ta ce.

"Jamɓanduna,
Noi sare,Noi kuɗe" ta jera hausuwar ma'ana _“Ina kwana, ya ya gida, ya ayyuka”_ ya ware gajiyayyun Idanunsa a kanta, yana bin shigar makarantar nata, ta ɗaga kai ta gan shi tsaye ta miƙe tana kallonsa, ya dubi yam balls ɗin hannunta da raguwar na gefen bakinta. "Jiya nai barci baka dawo ba, yanzu kuma wai makaranta za a kai ni inji Ummul" ya jinjina mata alamar _"Eh"_ yana ƙoƙarin juyawa tayi saurin riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya ta ce "Miyetti masin, Allah ya ƙara arziƙi"
Ɗan ƙaramin bakin maganar kawai yake bi da kallo, gumi na tsastsafo masa ta goshinsa ta saki kyakkyawan murmushi ta ce "Mijina" da sauri ya kalli cikin idanunta ta ɗauke nata idanun sai murmushi take sbd daɗin zata makaranta.

A hankali ta buɗe baki a taushashe kuma cikin ƙasa da murya ya ce "Matar m......" Maganar ta tsaya sbd yam balls data tura masa a cikin baki ta dinga tsalle tana cewa "Nayi maka wayyo daman ance baka cin abinci" ya lumshe fararen idanunsa tare da nufar kujera har lokacin tana riƙe da shi. Yana zama ta zauna a ƙasa Yaa Sheikh sai mai da numfashi yake sam bai niyyar cin komai ba, bisa dole ya shiga tauna yam balls ɗin bakinsa yana goge zufar dake goshinsa, wanda kuma shi kansa ya san zufar ta mece ce. Ya ɗauki bottle water tare da tsiyayawa a cup bayan ya sha ruwan ya mai da numfashi. Halisa ta ce "nace Ummul tayi maka wani na cinye gaba ɗaya tas" gently ya buɗe idanun a kanta ganin yadda yake bin fuskarta da kallo sosai yasa tai masa kyakkyawar murmushi tana lumshe idanu tare da buɗewa kamar yadda yai, a hankali ya ɗan ranƙwafa daidai kanta ya sanya fararen tafukan hannayensa tare da kama fuskarta da kyau babban hannunsa yasa yaja kumatunta numfashinsa na sauka a fuskarta ya ce.
"Zaki fasa mini kai da surutu Matar Malam, shiru kan na É—inke bakin......

Not edited
Paid book
₦500
08119237616
Sarautar marubuta.

_Ubangiji ya haɗamu da alkairan da suke cikin jumma'h. Mu haɗu Monday🥰❤‍🔥_

_I unite you with the greatness of God a daina fitar mini da littafin IDAN BA KE. What you want will not be difficult for you to buy. This is not appropriate at all.🫰🏿har zuwa ake a nuna mini wai an samu book ɗin Idan ba ke as free irin ga masifaffiyar nan bari nai ta ihu a media😂 I love my book lovers wherever they are. Amma don Allah a daina fitar da book ɗin... It's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616_
Chapter 43 · 0% Book details