← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 55

Sashe 28

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A harabar gidan Abba Hakimi ya yi parking motar, ganin motoci da yawa ya sanya shi taɓe fuska baya son hayaniya sam. Ya fito a kame yana jan gemunsa kaɗan ta baya yabi a ƙoƙarin shi na son shiga part ɗin nasa ba tare da kowa ya gansa ba. Yaje corner kenan yaji ance.
"Yaa Sheikh" Khalil Ahmad Sarki ya faɗa yana murmushi hannun shi riƙe da gorar ruwa. "Yanzu nake shirin zuwa can gida muji yadda al'amarin bikin zai kama, nasan dai bikin Yaa Sheikh dole ba events ba D.j" Sheikh ya ware idanu da kyau yana bin Khalil da kallo. Khalil ya ce "na ƙosa naga matar Yaa Sheikh, nasan dole ta zama Malama kamar haka, Wow! Ga Yaa Sheikh ga Malama what a beautiful couples wlh dole love yaci ƙaniyar shi"
Yaa Sheikh ya ɗauke Idanunshi tare da kama hannun Khalil Ahmad sarki suka nufi hanyar ƙofa Khalil ya ce "Ya dai kamata ka fito tun ɗazo Mai martaba ya shigo" har lokacin Yaa Sheikh bai ce komai ba, yana zuwa bakin ƙofa ya tura Khalil waje tare da rufo ƙofar ya murɗa key. Khalil ya dinga dry daman ya lura zan can damun Yaa Sheikh yake yana mmkin yadda baya ƙaunar ai masa maganar mace?. Ya juya inda yabar su Abba Hakimi yana zuwa ya ce "Abba Hakimi ai ga ɗan naka can ya gudu part ɗin shi" Abba Hakimi ya ce "Za mu yi faɗa dakai yanzu Ibrahimul-khalil" Khalil ya yi murmushi ya ce "Nikam ina ruwar gida Momi ne?" Abba Hakimi ya ce "Tana can tana kayan buɗe baki na Aliyu, ƙosai da kunun gyaɗa"... "Ah! Lallai aikin lada take kenan" Mai martaba Ahmad Sarki ya kalli Ishaq-Hakim cikin kamala ya ce "kira Sheikh" da mutumtaka ya ce "To ranka ya daɗe Allah yaja kwana" kafin Ishaq-Hakim ya miƙe El-bashir wanda tun ɗazo yake hakimce saman kujera ya miƙe cikin nutsuwa hannu cikin aljihun suit ya nufi hanyar fita Abba Hakimi ya bisa da kallo yana nazartar yanayin yaron wanda baya son haɗa inuwa da Yaa Sheikh gaba ɗaya. "El-bashir kada kai nisa" cewar Mai martaba. He just nods his head and quickly leave the parlour. Bayan sallar magrib Yaa Sheikh na zaune a ƙawataccen parlournsa gabansa ɗauke da kayan buɗe baki, inibi yaci sai ƙosan da yake mai zafi ya yi laushi sosai sbd ƙwai da aka zuba cikin haɗin, hakan yasa ya ɗan saki jiki ci ƙosan da kunun gyaɗar. Yana jin gine da jikin kujera yana kallon Aljazzera yaji Sallamar Abba Hakimi shi ne kawai ke shigowa kai tsaye cikin part ɗin na shi, ya gyara zama sosai yana mai amsa sallamar ta Abba Hakimi. Bayan Abban ya zauna ya dubi Yaa Sheikh ya ce. "Aliyu haydar" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa gaba ɗaya tare da kallon Abba Hakimi da yake faɗin "Jibi ɗaurin auren ka, ya ya zakai da uwar gidan naka kafin amaryar tazo?"
"Uuuu...uu... Uwar gggg gida? Am am amarya?" Ya faÉ—a yana kallon Abba alamar rashin fahimta. Abba Hakimi ya lura da gaske Yaa Sheikh bai gane ba ya ce "Yarinyar da aka É—aura maka aure da ita a can Yola? Ka tuna?" Tab yakan manta abubuwa amma wannan abun ya zama abu na farko da ya yi saurin mantawa da shi. "Ina jinka,ina so muje can rugar tasu ne" magana zarar bunu cikin rashin sani Yaa Sheikh ya ce "Uhm bani da labarin hakan Abba, idan akwai auren ma zan kunce shi yanzu...

*Don Allah kada a fitar😒 littafin IDAN BA KE na kuɗi it's 500 via this account 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Via evidence 08119237616.

SARAUTAR MARUBUTA

Surry da mamakin kaifin bakin Halisa Danejo Rome ya gama cika mata zuciya,domin yarinyar ƙwarai ta shayar da ita mamaki, alamu sun nuna da gaske take dukkan maganganun da take. Surry ta ƙara gyara zama ta ce.
"Ok sai ki shirya biyanmu dukkan kuÉ—in da muka kashe, kama daga kuÉ—in aiki, magani, kuÉ—in gado, dana abincin da kuke ci?" Bakinta har kumfa yake wajan faÉ—in.
"Aradu babu inda zani ina tare da Dadata ku bakwa abu saboda Allah ne yanzu ba lada zaki samu ba?" Surry da ranta ya fara ɓaci da abin da Halisa keyi wanda yake gab da shirin ruguza mata nata tsarin na ganin ta kai Zahrah ƙasa ta ce "To ba mu yi niyyar samun ladan ba, idan ba zaki iya biyan kuɗin ba, dole kije ko na kira ƴan sanda" Halisa na ƙoƙarin magana Dada ta kalleta tare da watsa mata harara cikin sanyin murya ta ce.
"Ki manta da ita, tunda tai al'ƙawari dole taje duk da nima bana so, amma babu yadda za a yi ƙila hakan shi ne alkairi" murmushi ya bayyana saman fuskar Surry ta ce "Ai alkairi ne ma, zaki mamakin Halisa aikatau ɗin data samu mai kyau kuɗi sosai za a bata" Dada ta jinjina kai alamar gamsuwa.
Halisa banda tura baki gaba babu abin da take,duk abin ta bata iya musu ki jayayya da maganar Dada maganar ta kamar yankan wuƙa take. Surry ta miƙe tana duban Halisa ta ce "Ki tabbatar kin fara aiki da kayan nan kamar yadda na nuna miki?"

"To sannu Dada" Surry ta hangame baki cikin ranta al'amarin daÉ—i yake mata, Zahrah zata zauna da daidai ita wacce bata da tsoro sam cikin lamarin ta. "Ni kike haÉ—awa da Dadar taki?" Halisa ta ce "Eh Aradun Allah, naga ita kawai ta isa ta bani umarni na bi" Surry ta kasa cewa komai tayi waje abinta bayan ta ajjiye musu kuÉ—in mota na komawa can Rugar Rome.
Dada ta sauke numfashi tana kallon Danejo ta ce "Bakin ki babu linzami Danejo?" Ta tura baki ta ce "Ni ban san wani linzami ba, kin fi so aita cutarmu kina kallo, wai Dada waye Baffa ne?" Dada ta ɗaga kai da sauri kanta na sarawa zuciyarta na harbawa da ƙarfi najin tambayar na Danejo kamar daga sama. Halisa ta ƙara cewa "Dada waye Baffa mai yasa komai nasa sai a ƙwace mana shi?" Dada tai shiru har lokacin kallon Danejo take, irin kallon meke damunki ɗin nan? Me ya sa kuma kike tambayata wannan babbar maganar mai shirin tarwatsa zuciyata. "Do Allah Dada yau ɗaya ki faɗa mini waye Baffa a cikin Rugar Rome? Kuma....,"
Kyakkyawan marin da Dada ta saukewa Danejo shi ne ya taimaka wajan haɗiye sauran tarin maganganun da su ke maƙale a saman harshenta, cikin faɗa Dada ta ce.
"Hande en boni Danejo, banshe kada ki sake maganar Baffa? nashe ki barshu da Allah duk wanda suka ƙwace naggenku" Sai kuma ta fashe da kuka ganin yadda fuskar Danejo tai jajir saboda marin da tayi mata sai huci yarinya take alamar zuciyarta na kusa.
Dr ya turo ƙofar room ɗin hannunsa riƙe da file tare da kallon Danejo dake kuka ya ce "A'a yau mai akaiwa ƴar fillo ne?" Bakinta na rawa ta ce "Ba wanda suka kawo Dadata bace wai mijinta zai..." Kafin ta ƙarasa Dr ya ce "Ƴar fillo bari na fara duba Dadar taki yau dai kuka ya ƙare Dada ta samu lafiya" nan da nan ta washe bakinta tare da goge idon kukan kamar ba ita aka daka ba. Ta tsaya gefen Dada, Dr ya fara dubata cikin nutsuwa yana gamawa ya ce.
"Allahamdulillah, jiki ya samu, yanzu zan baku takardar sallama, tare da magani sai ku tafi gida" Shatu ta fara tsalle zasu gida. Cikin ƙaramin lokaci aka gama musu komai Sai da Dada tai Faɗa kafin Danejo ta ɗauki kayan da Surry ta bata suka nufi gida.

Zahrah na zaune ana gyara mata tulin gashin kanta sai kiran number Surry take taƙi shiga tai tsaki, tana ƙara danna wani kiran Surry ya shigo ta sauri ta ce "Heyy what's going on, see me here stop calling" ta faɗi Maganar tana shigowa cikin bedroom. Zahrah ta miƙe ta ce "Wai ina kika je? I have been trying to call your number amma yaƙi sai yanzu yake shiga, from where?" Surry ta zauna ta ce "Kin san kayan dinner ɗina bai zama ready ba, naje wajan tailor meye kike ta ihu ne?" Zahrah ta juya ta kalli Make up artist dake tsaye ta ce "Excuse us please" ta ce "Sure Maaah"
Zahrah ta kalli Surry da kyau ta ce "Surayyerh gabana faɗuwa yake, ina jin tsoron a gane ina da ciki Wallahi, ina mutuwarsa son Yaa Sheikh kamar rayuwata, kullum cikin fargabar ranar da zata zo wacce zai haɗa gangar jikinsa dana ƴar fillo, I'm scared Surry" wani shu'umin murmushi Surry tayi daman tasan tatsuniyar gizo ba zata shige ta ƙoƙi ba. "ko fasa tafiya da ƴar fillon zaki ne?" Zahrah ta waro idanu ta ce "Idan ban tafi da ita ba ya ya zan yi? Kina ganin ya ce idan bai saman matsayin mace ba zai sakeni, wlh ina son shi ba zan bari nayi wani abu wanda bai dace ba, dole zan tafi da ita, kuma dole ne ya kwanta da ita a matsayin ni, sai dai i have a plan ba zan bar ƴar fillo haka ba, dole nayi mata baƙin fenti" gaban Surry ya bada sauti sai ta share ta ce "Ya kamata kam, ƙila plan ɗinmu ɗaya me zaki yi mata ke?" Tai murmushi ta ce "sirri ne, muje lokacin na tafiya Finally Aliyuna zai zo na kansa, har imagine nayi hugging nasa nake" Surry ta ce "Uhm" kawai tana barin bedroom ɗin.
Chapter 28 · 0% Book details