Sashe 27
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"E, da kin kammala aikin naki zamu dawo dake ai ba can zaki zauna ba" Danejo tai murmushi ta ce "Aikin ba wahala Aradu na yarda nidai" ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke na jin daɗin kafin ta ce.
"Shiga mota muje Rugar taku" Danejo tai shiru kada taje kuma masu yanke kai ne, haka kurum su yanke kan a banza. "Shigo muje mana?" Surry ta faɗa domin tuni Zahrah ta shiga motar tare da yi mata key. Ƙwaryar nonon ta ɗauka tare da shiga inda Surry ta nuna mata, ta shiga a tsorace bakinta sai rawa yake na tsoro, a haka Zahrah taja motar tare dabin direction ɗin da map ke nuna mata har suka isa Rugar Rome.
Da gudu Danejo ta fito tana ƙanƙame ƙwaryar kindirmonta. Surry ce ta fara kallon rugar Zahrah ta dinga taɓe baki kamar wacce taga makusa domin Rugar Rome abin sha'awa ce ba ƙazanta cikinta.
"Bari na faɗawa Sarkin ruga anyi baƙi ko?" Da sauri Zahrah ta riƙo Danejo ta ce "A'a kada ki faɗawa kowa, sbd zasu hana akai Dada asibiti muje kawai" cike da gamsuwa ta yarda ta nufi bukkarsu, suka bi bayanta. A kwance suka samu Dada idanunta nayin sama kumfa na fita daga cikin bakinta kamar ko yaushe, Shatu na gefe tana jijjiga Dada sai ihu take domin jikin Dadar ya yi tsamari fiye da ko wanne lokaci. Surry ta zaro idanu sosai bata ɗauka ciwon yai girma har haka ba, da sauri ta ce "Kamata muje Zahrah subuhanallah haka jikin nata ya yi" Danejo na kuka ta ce "Na shiga uku na lalashe Dadata kada ki mutu ki barni kinji" Zahrah ji take kamar ta shaƙe Danejo sbd baƙin ciki haɗa jiki da zatai da mijinta nan da bada jimawa ba, hakan ya sanya taji harta fara tsanar yarinyar. A mota suka saka Dada shatu da Danejo suna baya kusa da mahaifiyar tasu, a wannan lokacin Surry ke driving motar, Zahrah na gefe lokaci zuwa lokaci tana kallon Danejo ta madubi anya batai kuskure ba?.
A Specialist Yola motarsu tai parking nurse's suka fito da gado kai tsaye tare da saka Dada akai, kasancewar Babban asibiti ne kuma an san Zahrah Farouk cikin ƙaramin lokaci aka buɗewa Dada file aka fara yi mata medical check up.
Dr ya fito da sauri Surry ta miƙe tsaye ta ce "Dr ake ciki?" Idanunshi akan Zahrah ya ce "ki saman office" yana faɗin hakan ya shige Office ɗinsa. Surry ta kalli Zahrah ta ce "Muje Madam" ta tsuna fuska ta ce "No I'll wait here, kije yadda ake ciki let me know" ta girgiza kai tare da bin likitan zuwa office nasa. Yana zaune akan kujera ta same shi bayan sun gaida Surry ta ce.
"Dr ya ake ciki ne?" Dr ya sauke numfashi yana zare Glasses ɗin idanunshi ya ce "Allahamdulillah kun kawota lokacin da ya dace, matar na jin jiki wani ƙari ne ya fito mata a ciki shi ne ke wahalar da ita" Surry ta ce "Thank God, yanzu mene mafita zuwa yaushe zata samu lafiya?" Ya gyara zama da kyau yana duba file ya ce "Zaku biya kuɗin da za ayi mata aiki, a daren yau misalin 10 za a yi aikin, muna da ƙwararrun likitoci cikin kwana ɗaya biyu komai zai daidai a ɗora ta bisa magani" cikin jin daɗi Surry ta ce "Dr hakan ya yi, nawa ne kuɗin?" Ya ce "Dubu ɗari biyu da hamsin ne har magani" ta miƙe tsaye tana ɗaukan waya da hand bag ta ce.
"Ok bari naje na biya kuɗin" tana faɗin hakan ta fito ta samu Zahrah zaune tana waya, Danejo da Shatu sun rakaɓe waje guda sai zare idanu suke. Danejo ta miƙe da sauri ta nufi wajan Surry domin tafi fuskar rahama akan Zahrah muryarta na rawa ta ce "Ina Dadata? Tun ɗazo ban ganta ba ina kukai mini ita?" Zahrah ta ja tsaki Surry kuma tai murmushi ta ce.
"Haba ƙanwata kin san babu inda zamu kai Dada sai wajan likita,ya ce gobe zata fara magana ki kwantar da hankalin ki" fararen haƙoranta masu kyau suka bayyana dalilin murmushi da tayi ta kalli Shatu ta ce "Shatuna Dada zata lafiya, aradu wannan ƴa ƴan albarka ne dole nayi musu aiki suma" Surry ta girgiza kai ta ce "ku zauna nan yanzu zamu dawo, kada kuje ko'ina har abinci zamu kawo muku" a tare suka ce "To Adda"
Surry da Zahrah suka nufi wajan biyan kuÉ—i, tare da cike komai da komai.
Driving take jifa jifa tana murmushi Zahrah ta gaji ta ce "Wai murmushin me kike haka Surayyerh ko tausaya mini bakya yi wata zata kwanta da mijina?" Surayyerh ta girgiza kai tana bin waƙar dezell can ta ce.
"Yarinyar ce abin tausayi bake ba Zahrah" Zahrah ta ce "kamarya? Mijina zai san wata bani ba" Driving amma bai hanata fashewa da dariya ba sosai tana buga kan motar
"What funny Zahrah? Serious daneja ko Danejo take ita ce abar tausayi, look how young she is bana tunanin zata iya É—aukan al'amarin namiji,and she didn't understand what we meant".
"And so what kuma? Idan har za a amshi budurcin nata? Look Surayyerh ni bana tausayin ta yadda na kai tsuhuwar ta asibiti dole ta cika mini nawa aikin" Surayyerh ta juya kaÉ—an ta kalli Zahrah ta ce "I don't feel sorry for her either,kawai Sheikh ba zai iya haÉ—a jiki da ita a yadda take ba, dole a sauya ta" Zahrah ta ce "like how wanne sauyi?" Kai tsaye Surry ta ce.
"Ta daina warin da take, ta zama mai tsafta ƙamshin ya zauna mata ki sanya ta nutsu sosai nutsuwar da shi kansa zai fahimta cewa eh da gaske ke ɗin ce" da ƙarfi Zahrah ta ce "Tab hauka kenan, Please stop it bana son jin haka.." Surayyerh taja tsaki a ranta ta ce "mahaukaciya"
Maimoon ce ke zaune tana tura baki Mother ta ce "Oh kina so ace ni na hanaku yin kwalliya a bikin yayan naku ko Maimoon?" Maimoon ta ce "Haba Mother bakya farin ciki da auren akan me mu kuma za mu yi har muje muyi wani henna da saloon?" Zeefa ta ce "Wallahi Moon, ni fa tun kafin naga amaryar naji na tsaneta kamar Father ya fifita ta akanmu" Auta Fattoumah fuska a haɗe hannunta riƙe da handle ɗin game ta ce "I hate her too, because of her the happiness in our house is gone"
Mother ta saki baki da hanci tana bin yaran nata da kallo kafin ta ce "Akwai wanda ya halicci Zahrah a cikin ku? Balle kuyi ƙorafin sauyin halittar ta? Kul na kuma jin magana irin wannan, musamman ke Maimoon, Mamana ke kuma waye ce miki sbd ita farin cikinmu ya tafi?" Fattoumah ta yarda handle ta ce "Mother nasan komai fa, gashi har father yana cewa ana nemawa Yaa Lee mahaifi" Mother ta runtse idanu sosai wato kaf yaranta idan aka ɗauke Sheikh babu mai kaifin tunani da basira irin Fattoumah,ga riƙo tana lura da komai. A sanyaye ta ce "Maza ga mai henna can tana yiwa Dr A'isha kuje ayi muku" tana faɗin hakan tai waje.
A main parlour ta samu Dr A'isha da Yaya Halima sai friends É—inta irin su Barrister Zainab. Mother ta zauna a kujera idanunta akan t.v ba tare data cewa kowa komai ba. "Sheikh ya yi lunch kowa?" Cewar Dr A'isha. Mother ta É—an kalleta kaÉ—an ta ce "Anya? Kamar dai azumi yake" Yaya Halima ta ce "ba kama bane, yau Alhamis ai"
"Oh haka ne fa, na manta azumin Alhamis da Litinin Allah ya bamu lada" Barrister Zainab tai murmushi ta ce "Wato ke Dr A'isha ba zaki iya ba? Shi yasa É—an naki ya rainaki" tai dry sosai ta ce "Azumi kam sai manyan malamai irin su Sheikh Aliyu haydar Aliyu".
Sheikh na zaune shigowar shi kenan daga masjid yin sallar asr, a hankali ya sauke numfashi. A nutse ya ajjiye azkar ɗin hannun shi tare da miƙewa yabar cikin Library ɗin na shi kai tsaye ya nufi haɗaɗɗan bedroom ɗin sa wanda yaji kayan more rayuwa ko'ina na bedroom ɗin ƙamshi yake, ya zame jallabiyar jikinsa wanda ƙa'ida idan zai shiga wanka sai ya cire komai ya rage daga shi sai boxer yake shiga. Tsarin halittar jikinsa ta bayyana yana ɗan kare jikinsa da hannu a haka ya shige bathroom tare da sakarwa kansa shower ta warm water. Fitowa ya yi sanye da towel jikinsa ka fitar da ƙamshin MUD BEGIN Natural shower Gel. Idanunsa na lumshewa kamar mai jin barci a haka ya shafa versiline mai kanshi tare da fesa body spray. Wata duguwar Jallabiya mai nauyi da tsada ya ɗauka ya sanya, jallabiyar daban take domin har wani zane ne jikinta kamar alkyabba. Yana gama sawa ya naɗa rawani kamar kullum tare da ɗora hirami saman ƙafaɗar shi. tsaf ya kammala shigar shi irinta manyan malamai wanda suka san me suke ko a maluntar. Jikinsa na fidda ƙamshin Roja wanda ya bayyanar da zuwan shi cikin Main parlour ɗin gidan. Kansa a ƙasa ba tare daya kalli kowa ba, kamar yadda zuciyar shi ta raya masa hakan ce ta kasance Dr A'isha na ganinsa ta fara buɗa tare da faɗin.
"Ayyiri yiri the lastest ango of the year" ya ƙara kame fuskar shi babu walwala hannun shi akan gemunsa yana ɗan ja haka yai waje ba tare da kalle ta ba, balle yace mata wani abun duk da yaso ya tsaya yayi mata bayanin aya da hadisai Manzon Allah akan muhimmancin muryar mace. Da kuma rashin amfanin wannan ihun da take.
Chevrolet silverado car wacce ta kasance blue black ya nufa, harabar gidan shiru hakan yasa ya rufe idanu yanayin na masa daɗi na shaƙar fresh air ga ƙamshin na'ana'a dake ɗan nesa da shi, Bismillah ya yi tare da shiga motar sai da ya yi addu'a kafin a hankali ya yi wa motar key gatekeeper ya buɗe masa, cikin nutsuwa da haiba yake driving motar har ya harbata kan titi.