← Book details Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 55

Sashe 49

Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

If you read for free🤷🏾‍♀️ it's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.
Kokawar ƙwace kanta take amma ta kasa ya sauke ta saman kujerar dake kusa da bed ɗin ɗakin nasa, bai kula ta ba ya nufi deep freezer ya ɗauki Apple guda ɗaya wacce tai sanyi. Cikin nutsuwarsa da son kame kansa daga yanayin da yake ciki ya nemi waje saman gado ya zauna, kyakkyawan numfashi ya sauke yana ƙara daidaita kansa a karo na babu adadi. Ya ɗago kai yana duban direction ɗin da take, dole sai ta sanya ma gantu ya miƙa hannu cikin taushin murya ya ce..
"Zonan naji, rigimar me ce?" kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake domin bata iya bijirewa umarninsa. Ya dubeta da kyau amma taƙi yarda ta kallesa cikin son jin meke faruwa ya kamo hannunta zuwa inda yake zaune muryarsa har kullum a taushashe ya ce. "Ya akai matar malam? waye?" Hawaye na sakko mata ta ce "Abba kai ne, Mother ta ce kai miji na ne, me ya sa kake bari Anti Zahrah take taɓa ka" ya dafe kansa cike da mmkin kaifin bakin Halisa ya ce "Ba zaki bar mganar mijin nan ba? You're too young to understand that"
"Abba ina son ka ai" Ya girgiza kai ya lura rigima take ji kuma ta shirya bashi kunya a Idanun kowa. Yana mamakin yadda maganar miji ta zauna a bakinta raɗau kamar wacce akewa bita akan hakan. Ya dubeta yana dawo da ita gefensa tare da riƙe hannunta ya ce "Matar Malam ki bar mganar mijin nan, ba zaki gane ba, ki dai bar Anti ta faɗa ok?" Ta maƙale ka faɗa alamar bata amince da zancan ba kaifin ta ce "Abba...." Sai kuma tai shiru ya ɗago kanta tare da tallafo haɓarta yana duba cikin idanunta da hawaye ya kwanta. "Matar malam" ta marairaice fuska tare da faɗin "Abba yaushe zan zama matar malam ɗin? Kuma yaushe zan zama kamar Anti Zahrah nima na dinga rungomeka?" Ya kau da fuska tare da lumshe idanunsa a hankali ya ce "Baki son Antin naki tana haka? Ni kuma fa" ya ƙare maganar yana ƙara riƙe fuskarta a hannunsa da kyau, gaba ɗaya ta marairaice fuska ita a dole bata son abin da Zahrah ke masa, haka kurum ranta ke ɓaci taji kuka yazo mata ta ce "Abba zanna yi maka, da safe da rana, da daddare" ya shafa kanta cikin nutsuwa ya ce.
"Kada mu fara haka, ki tsaya a ƴar rainonki" ta langwaɓe kai ta ce "Abba ni ban son rainon Ummul ta ce kayi mini karatu" bai biyewa surutun nata ba, ya amshi littafin nata duk dan a rabu lafiya, burinsa kuma bai shige ta tafi part ɗinsa ba, ko zata barshi ya samu salama daga surutun nata mara dalili da toshe.
Cikin sauƙin harshen yake mata bayani akan Social studies ɗin, da kuma muhimmancinsa. Ya kama hannunta ya ɗora saman littafin a hankali ya ɗora nasa hannun akan nata ya fara nuna mata yadda zatai rubutu, yana lura da ƙwazonta ko dan akwai son karatun a ranta duk abin da ya nuna mata ɗauke shi take.
Ta É—ago kai ta kallesa taga hankalinsa baya kanta gaba É—aya ya tattara nutsuwarsa zuwa ga abin da yake nuna mata.
"Abba" Halisa ta faɗa tana ƙarewa fuskar shi kallon yaƙi kulata ta leƙa fuskar shi ta ƙara cewa "Abba kana da kyau sosai, kaga gobe idan naje makaranta zance mijina ne ya yi mini aikin ko?" Nan ma bai kulata ba amma tsat yake ɗauke zancan nata a zuciyarsa tasbihi kawai yake. Taja gemunsa cikin sauri ya miƙe tsaye yana damƙa mata littafin tare da janta zuwa bakin ƙofa kamar an masa dole ya ce. "Ki kula, akwai sanyi" ta ɗaga kai tana faɗin "To Abba" har ta juya zata fita ta dawo da sauri zuwa bedroom ɗin Yaa Sheikh kuma a lokacin ya juya hannunsa ɗauke da azkar na dare yana dubawa..
Kyakkyawar rungumar data bashi da baya ya sanya Azkar ɗin suɓuce masa cikin In-inar data zo masa a lokacin zufa na yanko daga goshinsa ya ce.
"Yaaa....yaaaa... Allahu ya ya... Ya Rahman, Yasubuhanallah" ta saki dry tana riƙesa ta ce "Abba kaga nayi maka ta dare sai da safe" kasa magana ya yi tana sakinsa ya buɗe ƙofar bathroom ya shige ciki... Cikin farin ciki da murna yau itama tayi abin da Anti Zahrah keyi ta nufi part ɗin Ummul. Ummul ta kalleta ta ce "Kin dai gane karatun ko?" Ta ɗaga mata kai kawai tana jan plate ɗin da Ummul ke mata, tana cikin cin abincin ta ce "Ummul kin same?" Ummul ta girgiza kai ta ce "Sai kin faɗa matar malam" Halisa ta ture abincin dan ba wata yunwa ta keji ba ta ce.
"Me ya sa gumi ke fitowa a goshin Abba? Kuma naga wani abu a jikinsa ba, duk sanda na gani kaina juyawa yake" Ummul a zuciyarta addu'a take Allah ya sa ba wata maganar da zata bata Kunya zatai ba, ko wani abu ne ya faru tsakaninta da Yaa Sheikh ɗin take son faɗa, duk tai mamakin haƙurinsa, daya kawo har yanzu, ta riga tasan waye Yaa Sheikh da kuma yadda ya ɗauki al'amarin Halisa da girma ko yana jin tsoran yanayin rigima da ƙuruciyarta ne?.
Halisa ta dawo da Ummul daga tunanin data tafi ta hanyar faɗin "Ummul ni ina son Abbana" Ummul ta ce "Kina iya bakinki, ba dan abinci kawai Ubangiji ya bamu ciki ba, hadda ɓoye maganar da bata da ikon a faɗa da riƙe sirri, ki nutsu idan kina wannan shirman Abban naki ba zai so ki ba" Halisa ta kwanta tana juyawa Ummul baya ta ce "to naga mijina ne, kuma ina son sa" kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri domin abu biyu ne ya faɗo mata a wannan lokacin, da maganin da El-bashir ya bata, wanda take tunanin shi ne ya sanya Abban nata Yaa Sheikh yake fitar da zufar goshinsa, sai kuma tuna Dada da tayi.
Ummul tabi bayanta da kallo sai kawai ta girgiza kai ta ce "Ubangiji ga Danejo ka shirya mana ita, Allah ka kawo zama na har abada tsakaninta da Aliyu, ita ce farin ciki Aliyu, Aliyu shi ne garkuwarta"
Chapter 49 · 0% Book details