Sashe 5
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
3.
"Na shiga uku ta ya ya zan iya wasa da maciji? Wallahi kashe ni zai yi" Danejo ta faɗa a fili cike da tsora wanda ya sanya har ta kusan sakin fitsari gaba ɗaya ta firgita. Shatu ta ce "Ki faɗa masa ba zaki iya ba a zaɓi wata, idan Mashijin ya kashe ki na shiga uku na lalashe aradu" da sauri Danejo ta fito tsakiyar fili idanunta akan Alƙalin wasan muryarta na rawa ta ce "A yi mini afuwa Alƙalin wasan ba zan iya wasa da maciji ba aradu sarata zai yi" Alƙalin wasan ya kalli Danejo sosai, shi ya ɗan jima bai ganta ba, ta ƙara girma da wayo sosai ta zama ƴar budurwa irin girman ƙauyen nan dai. Sai rashin tsafta da addini dake ɗawainiyya da ita duk da ana ƙoƙarin ganin an magance hakan a cikin Rugar Rome. Murmushi alƙalin wasan ya sake yi cikin kulawa ya ce "Zaki iya mana? Ai Baffanki ya ƙware wajan iya sarrafa maciji, a wasan ƙarshe kuma macijin ya zama silar mutuwarsa, ki yi wasan ko dan ƙarasa cikawa Baffanki burinsa na zama gwarzo a Rugar Rome. Tabbas zaki iya Halisa Dajeno Rome" girgiza kai tai da sauri idanunta cike da hawaye ta ce "Ba zan iya wasa da maciji ba, mene ya sa sai ni? Baffana daban ni daban kalleni ƙarama ga maza nan da yawa a zaɓi wani daga ci" Sarkin rugar yai saurin faɗin "Ke aka zaɓa, kuma dole kiyi domin ba zamu taɓa sauya ra'ayinmu ba, ya zame miki wajibi muddin kina cikin Rugar Rome" a tsorace Shatu ta ce "Hande en boni, yau mun shiga uku" kasa cewa komai Danejo tai domin gani take kamar ma ta mutu ne lokaci kawai take jira.
Da sauri ta juya idanunta cike da hawaye ta nufi cikin bukkarsu zuciyarta cike da zullumi da kuma fargabar abin da zai je ya dawo. A haka ta shiga cikin bukkar Idanunta akan Dada wacce take kwance cikin halin ciwo, domin a kullum ciwon nata ƙara tsanani yake. "Dada Alƙalin wasan ya zaɓi Danejo matsayin wacce zatai wasa da maciji a gobe" da sauri Dada tana jan numfashi ta kalli Danejo cikin damuwa ta ce "Mene ya sa baki cewa masa ba zaki iya ba?" Shatu tai saurin faɗin "Sarkin ruga ya ce wai dole tayi domin cika muradin Baffanmu" Dada ta miƙawa Danejo hannunta cikin kulawa ta ce "Waye yace muku Baffanku wasan maciji shi ne burinsa?" Danejo ta kasa magana sai ajjiyar zuciya take saukewa Shatu ce tai ƙarfin halin cewa "Sarkin ruga ne ya faɗa" Murmushin taƙaici Dada tai bata taɓa ganin zalunci irin haka ba, ta rasa me suka tsarewa Sarkin ruga da yake shirin ƙarar dasu ta hanyar kashesu da maciji wanda wasu suka tabbatar macijin tsafi ne. Cikin ƙonar zuci ta ce "Baffannku bai taɓa sha'awar yin wasa maciji ba, halima babu wannan al'adar ta wasa da maciji a Rugar Rome, daga baya Sarkin ruga ya samar da ita, bayan ya samar da ita ya zaɓi Baffanku matsayin wanda za'ai wasan dashi" shiru tai sbd tarin daya sarƙe mata numfashi, da sauri Shatu ta ɗauki ruwa ta bata, numfashi ta sauke kafin ta ce "Bisa dole Baffanku ya amince, yasha wahala kafin ya kashe macijn bayan ya samu raunuka wanda ya sa ya kwanta jinya, da shekara ta zagayo aka ƙara zaɓar Baffanku abin mamaki shi ne babu bambanci tsakanin macijin shekarar data shige da kuma wanda aka fito da shi, Baffanku ya tsorata, gashi idan ya ce ba zai ba to za'a kuresa daga Rugar Rome, tun daga wannan shekarar Baffanku ke gabatar da wasan Maciji, har zuwa shekarar da maciji ya kashe shi wanda kuma anyi hakan ne domin aga bayansa. a ruɗe Danejo ta ce "Kenan kashe Baffa akai Dada?" Dada ta girgiza kai ta ce "Ba zance ba, bani da hujja akan haka koma mene hukuncin na wajan Allah".
Danejo taja numfashi cike da raunin murya na rashin sanin mafita zuciyarta cike da tarin zullumi ta kalli Dada ta Shatu ta ce "Dada ba zan iya ba, ina jin tsoro" "Halisa idan ba kiyi korarki za su yi daga cikin Rugar Rome, ni kuma ba zan jure hakan ba, Ubangiji na tare dake. Dole kiyi wasan imma ki mutu ko kiyi rai Kinji ko?" Kafin Danejo tai magana Hamma Yabi ya shigo da sauri idanunsa akan Danejo yana faɗin "Tashi mu tafi Danejo daman nasan bayanki suke son gani kamar yadda suka kashe Baffa" kallo Hamma Yabi Danejo tai idanunta ya kumbura sbd kuka ta ce "Hamma ina zamu?" Muryarsa na rawa ya ɗaga ta tsaye ya ce "Zanje na ɓoyeki sai an gama wasan zaki dawo, zan nuna ban san idan kike ba" Dada tai saurin cewa "A'a Yabi, kada ai haka kamar Halisa tare damu, idan ta tafi to Shatu ce zata maye gurbinta kasan haka ai" zama yai sosai ya ce "Yanzu haka zamu zauna? Ke baki da lafiya ita kuma muna kallo maciji ya kashe ta?" "Akwai Allah" Dada ta bashi amsa tana rufe idanunta. Halisa kasa bacci tai ga yunwa ga tsoro can cikin dare ta tuna ai ha tayi sallar issha ba, da sauri ta fito daga bukkar gaba ɗaya rugar shiru babu kowa sai wutar da aka kunnawa ko wanne garke dake ci hankali. Can bayan bukkarsu ta nufa tai tsari a wajan tai alwala babu ko shafar kai ta kwararan ruwan ta dawo. Sallar ma dungure tai Fatiha kawai ta iya cikakkiyar babu gyara. Yadda taga rana haka dare, dab da Asuba ta nufi garke tare da tatsar nono, tana gamawa ta Ajjiye. Gari na fara haske bayan tai sallah ta kaɗa shannun zuwa cikin jeji. Har zuwa lokacin bata da nutsuwa ita a yanzu ba wasan majin ya dameta ba, illar rashin lafiyar Dada idan har macijin ya kasheta waye zaici gaba da kula da Dada? Zama tai a gefen wani dutse ta shiga rusa kuka da iya ƙarfinta.