Sashe 35
Idan Ba Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tambayoyin. Halisa ta marairaice fuska tare da shagwaɓewa ta zama wata narkakkiyya hannunta cikin baki alamar shagwaɓarta a zahirance take bata ɓoyewa. "Uhm magana nake" tai saurin ɗaga kanta zuwa fuskar shi, baki da hanci ta saka ta kasa cewa komai El-bashir ya ƙifta mata idanu tare da ware su ya ce "Keee. "Wallahi kama muke, kai ma kasanni ya naga fuskarmu iya ɗaya?" Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin taɓa fuskar shi domin tabbatarwa. El-bashir ya haɗe fuska ya ce "Bani amsa? Wace ke?" Ta tura baki gaba ta ce "Sunana Halisa Danejo Rome, kuma ni matar Balarabe ce" El-bashir ya ware idanu ya ce "What are you married? Waye Balarabe?" Ta ce "Ace kada na faɗawa kowa sai lokaci ya yi amma dai ni zan dinga yiwa Matar Yaa Sheikh aiki, kuma ance jibi zamu tafi ko'ina ne, haka.....," "Heyyy will you shut up your mouth caaaaa haba" ta tura baki gaba fuska duk a shagwaɓe taƙi cewa komai. Ya gyara tsaiwa ya ce "Oh Halisa, dake Yaa Sheikh zai tafi ko?" Tayi saurin kallon shi ta ce "Eh" ya ce "Ok good, daman shi ya aike ni yanzu, kuma ke ya ce na bawa aikin domin ya yarda da hankalinki" tamkar wacce bata yarda da maganar El-bashir ba haka take kallon shi, wanne aike? daman yana sane da ita kenan yana son ta shi ma?.. "Riƙe wannan, ya ce ki ɓoye wajanki har sai kunje Madina, maganin shi ne, zaki zuba masa a cikin shayi ko abinci, kada ki bar kowa yasan da abin a wajanki, idan ba haka ba zai kureki daga gidan shi kinji?" Ta ɗaga kai ta ce "Amma bari na bawa Mother ajjiya ko?" Ta faɗa zata juya ya yi saurin riƙe hannunta ya ce.. "Ai har Mother ba a so tasan da maganin a wajanki, ki zama mace mai sirri ki tabbatar kin zuba masa, idan ba haka mutuwa zai gaba ɗaya" ta shiga girgiza kai tsoro da fargabar abin da El-bashir ɗin ke faɗa suka firgitar da Halisa ta ce "Wallahi ba zai mutu ba, ba zan barshi ya mutu ba, ni da kai na zan zuba masa maganin" wani irin kyakkyawan murmushi mara sauti El-bashir ya yi kafin ya ce "Good girl" ganin ya yi gaba ta ce. "Kai ya sunanka to?" "Ki ce El" ya faɗa a taƙaice tayi saurin faɗi "Ban iya faɗa ba, tunda muna kama ɗaya zan dinga cewa Hamma ka yarda?" Ya tsaya tare da juyawa wani abu nayi masa yawo akan abubuwa da yawa, kalmar kamannin data faɗa suka ƙara dagula masa lissafi. Ya jinjina mata kai tare sakar mata murmushi. Halisa bata da riƙo lokaci guda ta mance marin da Zahrah tayi mata. Cikin sauri ta ɓoye maganin da El-bashir ya bata tare da juyawa tabar wajan. Barinta wajan ya sanya Yaa Sheikh sauke numfashi tare da zame idanun shi daga saitin wajan da Halisa da El-bashir suka tsaya, yana mai ɗan girgiza kai tare da ya motsa fuska. Father ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Kaje ka duba visa ɗin Zahrah da Yarinyar da zatai mata aikin" Yaa Sheikh ya jinjina kai alamar "to" tare da miƙewa sai da ya je bakin ƙofa Father ya ce "Ka shiga part ɗin nata, da kanka ba aike ba kace ta shirya kuje tare, matarka ce saɓa mata tamkar zaɓa mini ne, kai ne mai auren amma ni ne mai zartar da hukunci ko da wasa ka sake Zahrah ta kawo ƙararka za kaga yarda za mu yi dakai Aliyu, kaji tsoran Allah kai Malami ne kasan hakƙin aure da sauke nauyin miji ga mata, kada ka yarda saboda baka son ta kace zaka tauye hakƙinta wallahi wallahi Allah Aliyu akan aurenka da Zahrah sai nayi maka baki" Yaa Sheikh ya juya da sauri ya kalli Father kalmar shi ta ƙarshe ta daki zuciyar Yaa Sheikh, kansa a ƙasa ya nufi wajan Father yana zuwa ya zube a wajan ƙafafuwan Father, cikin ƙasa da murya mai tarin nutsuwa da Ilham yana mai ɓoye abin da yake ransa a kame ya ce. "Kada ka aibata ni Abbi, zan riƙeta, ka saka albarka a kai na a karo na farko na rayuwata Father" Father ya kalli Yaa Sheikh kafin ya ce "Kaje Allah ya yi maka Albarka" Yaa Sheikh ya kifa kansa a ƙafar Father farin ciki ko baƙin ciki zai ji? Yau Father ya saka masa albarka dalilin Zahrah?. "Ka tashi kaje nace, kuɗi ne kama fini shi me zan maka? Ko akwai abin da ka ke buƙata?" Yaa Sheikh ya yi shiru can kuma ya miƙe tsaye tare da yin waje. A hankali ya haɗu da Maimoon da Halisa shi sam ba zai ce yaga Halisa ba domin direct idanunsa ya sauka akan Maimoon ɗin. Part ɗin Zahrah ya nufa lokaci wata farar riga ce a jikinta iya gwiwa waya riƙe a hannunta ta ce "No Deen ka bari muyi 1week a Madina sai ka zo ɗin? I will arrange a day when we can meet, I don't want to be recognized....," Ƙamshin Roja da hancinta ya shaƙa yasa tayi saurin ajjiye wayar tana duban door way, idanunta ya sauka akan Yaa Sheikh dake tsaye bakin ƙofar yaƙi shigowa ciki. Zahrah duk ga ruɗe bata tsammaci ganin shi a yanzu ba, ta sakko tana yin murmushi tare da girgiza jiki ta ƙarasu tana faɗin "My Excellency" Yaa Sheikh ya duba ta da kyau, har zai larabci ya tuna ba lallai tana ji ba, shi kuma he's not interested akan english. "Ki saman waje, mota" ya faɗa a taƙaice cikin rarrabe murya. Bai aune ba yaji Zahrah ta shige jikinsa tare da rungome shi. Bakinsa na rawa cikin rashin ya ce "Asstagafirullah, Allah na tuba" ya faɗa yana zame jikinsa tare da barin part ɗin da sauri. Yana zaune a bayan mota idanun shi rufe yana ta Asstagafirullah akan rungumar da zara tai masa, ba wani sauyi a jikinsa amma that is forbidden. Umar-khan ya ɓoyewa Zahrah bayan mota har zata shiga sai kuma ta tsaya ganin kamar maca ce a gaban motar, ta tsaya tana faɗin "Umar-khan wace wannan a gaban motar mijina?" Umar-khan ya kalli Halisa wacce take sanye da wata Marron ɗin turkish Abaya wacce Mother ta bata, Maimoon kuma tai mata rolling vail ɗin abaya a fuskarta, ƙaramar round face ta fito sosai farinta ya ƙara bayyana, gashin idanun nan lub zara-zara dasu idan ba magana tai ba, ba zaka taɓa cewa ƴat fillon Rugar Rome bace, ta kame kanta sosai bisa gargaɗin Mother. Umar-khan ya danne dariyar dake cin sa ya ce "Motar mijinku dai" "me kace?" Cewar Zahrah ya ce "cewa nayi baki gane wace ba?" Ta girgiza ta ce "Idan na gane wace mene amfanin tambayar?" Yaa Sheikh dai duk abin da suke cewa yana jinsu bai magana ba. Umar-khan ya ce "Ikon Allah, Ƴar fillo ce fa? Mai aikinki ina nufin Halisa ce a gaban motar garkuwarta" wani irin bugawa ƙirjin Zahrah tayi ta ƙara leƙa motar Halisa ta sakar mata wani cute smile ta ce "Laa Anti ni ce fa, mai aikin ki Halisa Danejo Rome" wani jiri ya ɗebi Zahrah tayi saurin riƙe motar a cikin ranta ta ce "Da sake wallahi ba zai yiwu ba....