Sashe 9
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fara shiri cikin satin nan sai ku wuce. Sannan albashinku yana nan kamar yadda na gaya muku da karin da nayi muku. Na gode." Manaja ya dafe kai DA tsananin tashin hankali, dakatawar watanni uku babu albashi da me zai dinga ciyar da iyalinsa har wannan lokaci balle kuma kudin da zai nemi mata, domin dukkan abinda yake samu jikin matan banza yake karewa. Bayan sanin halin babban manaja da ya roke shi arziki akan yayi hakuri, to ya san ko sauraransa na ba zai yi ba. Ahmad kam yafi kowa farin ciki, sai ga shi ya fara shirya jakarsa, domin babu komai acikin sai tsarabar kayan ma'u, dukkan abun da ya gani irin na mata ya ba shi sha'awa in dai bai fi karginsa ba sai ya siya mata. Isuhu kam yana ta zolayarshi akan yanda yayi magana ga babban manaja babu tsoro, mutumin da kowa yake tsoro fa shakkarsa. Ahmad bai sanar da kowa zai komo cikin satin ba, domin yana son yayi musu bazata ne kawai. *** Ranar asabar da dare suka bar birnin legas, mutum daya suka bari wanda yace shi yafi son aiki a nan legas. Ba su yi mamaki ha domin kowa ya san Magaji Abusa da bin matan tsiya, da shaye-shaye zai fi jin dadin zaman kurmi fiye da arewa. Wajen karfe Tara da rabi na safe suka iso garin Kano. Motarsu tana tsayawa yaji wani farin ciki ya cika shi, a ranshi umma da ma'unshi kawai yake son gani. Amman kuma yaji ya fi dacewa ya fara zuwa gidan Hajiya Amina domin idan ya shantake a gidan umma ba zai iya zuwa can da wuri ba. Idan kuma ta ji ya san zai sha fada, don haka daga nan tasha can ya nufa da lodin kayansa. Ta sha mamaki da ta ganshi, dadi ya cikata ta mike yace "Ahmadu kai ne haka babu sanarwa? Jiya ma can gidanku na yini, koda wasa ban ji sun ce zaka dawo ba" Ya yi mu rmushi da jin dadin ganinta cikin koshin lafiya yace "mama so nake na ba ku mamaki, tunda an yi ta sanya lokaci amman bana zuwa sai yanzu ALLAH ya nufa" "Kaga zauna ka sha ruwa ka karya tukunna" Bai yi musu ba ya zauna ya kawo masa abinci da abin sha yaci ya koshi, suka dan taba hira. Ta so ya kai shi gidan ma da kanta sai dai bakin da tayi ya sa ta fasa, sai dai ta dauko kudin mota ta bashi, dariya ta Kama shi yace "haba mama sai kace wani karamin yaro, ai yanzu ina da kudina" Ta bata rai "ban son sakarci, ka amsa mana nace" Ya zura hannu ya zari naira ashirin yace "wannan ta isa na nemi albarka da ita mama, na gode" Ya rataya jakarsa ya nufi fita. Ta bishi da kallo tana murmushi. Sai da ta dawo dakin ne ma tana yiwa bakinta magana ta hango jakar ledar da ya bar mata babba mai kyau, ta isa da sauri ta buda, leshi ne mai kyau da takalmi da turarruka, ta kada kai da jin dadi tace "Ahmadu ke nan, babu dama" DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Yana kokarin shigowa gidan ya ci karo DA Amina kanwar raliya. Taci kwalliya duk tayi bilicin ta koma kamar wata karuwa. Gabansa ya yanke ya fadi, domin kamanninta da kallonta sun tuno masa da raliya ne, gaba daya ta koma kamar raliya, cikin rawar baki tace masa, "yaya Ahmad sannu da zuwa" Ba tare DA ya kalle ta ba ya amsa mata da "yauwa" ya shige ciki da saurinsa ta bishi da kallo DA mamaki baki bude, gaba daya ya sauya yayi haske yayi kyau kamar ba shi ba, sai ta koma ciki da sauri domin ta bawa babarta labari, ita da kullum take addu'ar ALLAH ya sanya jirgin kasa ko mota ta taka shi ya mutu, ko 'yan fashi su tare shi sun harbe shi domin ta fara kishi da ganin yadda ma'un take komawa kullum, kuma a gidan ba a da magana sai ta ahmad. Sai kace shi kadai ne DA a duniya. "Lami! Lami!!" Ta shiga da gudu tana kiranta. Lami ta fito daga cikin daki da sauri tana kallonta. "Yaya dai, lafiya na gan ki kin shigo agigice kamar an koro ki?" "Lami Ahmad ya dawo" wanne ahmad kuma? Lami ta tambaya da sauri don bata fatan taji ahmad din gidan ne. "Ahmad din gidan baba Sulaiman mana, kin ga yanda ya zama kuwa, kuma da wasu manyan jakunkuna WALLAHI shikenan sun gama yin arziki lami kin ga girman jakar jikinsa kuwa? "Oh ni lami dukkan addu'ar da na yi ta tashi a banza kenan sai da yaron nan ya dawo amman muje zuwa dai wai mahaukaci ya hau kura. Ma'u tana durkushe tana wanke-wanke da T. Shirt a jikina da dogon siket ta daura kanta da dankwali tana 'yar wakarta ta jiyo sallamar ahmad. Ta daga kai da sauri da mamaki sai ta fasa ihu da jin dadi tana fadin "Yaya ahmad da gaske kai ne don ALLAH? Ta wurgar da kwanon dake hannunta ta nufe shi da gudu ta kankame shi tana ihu. Umma dake kicin tana kokarin dora sanwar rana, ta jiyo ihu ta fito da sauri ta leko. Dadi da mamaki ya cikata, tayi wurgi da ashanar dake hannunta tana fadin "ahmad kaine da tsakiyar ranar nan haka? Ke sake shi mana kin bi kin kankame shi kamar zaki kada shi" Kunya ta kama Ma'u ta sake shi da sauri, shi kam ji yayi kamar su dauwama a haka. Amman dai ya dake ya ajiye jakar hannunsa da sauri ya isa ga ummanshi ya durkusa yana gaishe ta. Umma ta dinga kallonsa cikin farin ciki da jin dadi tana amsawa. Ji take kamar ta goya shi a bayanta don dadi. Ma'u kuwa ta yi tsaye tana ta kallonsu yayan nata ya canja mata gaba daya. Yini aka a cikin hidima da murnar dawowar ahmad. Su Ma'u kuwa an kule a cikin daki sai aikin hada kaya take yi. Gaba daya gidan umman DA take doki a baya yanzu ya isheta domin shagwabar da take yiwa umma da yanzu ta daina, kuma tana son gwada irin abinda take koya a littafi a gidan mijinta musamman ma girke-girke da ta kware yanzu a kansa. Umma ta shigo dakin daukar abu ta hango ma'un ana ta hada kaya dariya taso kwace mata amman ta dake tace "Asma'u mene kike yi haka kuma? Babu kunya tace "umma kayana nake hadawa, ko ba yanzu zamu koma bane? Umma ta rike haba da mamaki tana kada kai. "Au har zaman gidan namu ya ishe ki kenan? Ma'u ta rufe fuska kunya ta kama ta tana dariya, umma tayi murmushi tace "ai sai ki huta da hada kayan domin ba yau zaku koma ba, sai an je an gyara gidan" ta fice ta barta, murnar Ma'u ta koma ciki ta turo baki gaba. Shi kansa ahmad abinda yake bukata kenan, ya koma gida ya kebe da matarsa ko hira su yi, amma yaya ya iya da hukuncin umman nasa dole yayi shirin kwanciya a dakin gwaurayen gidan, amma basu kwanta da wuri ba ana ta shan hira. Sassafe kafin kowa ya fito Ma'u ta sallara wankanta, sanda umma ta fito domin dama koko taci karo da ita ana shafa hoda da fesa turare. Umma ta rike baki "na shiga uku Asma'u, ba dai nan shirin tafiya gidan miji kike yi haka da sassafe ba? Malam ya dago labule yana kallonsu bayan ya dawo daga masallaci yayi murmushi. "To laifi tayi kenan? Ke fa kike mata gori kullum, yau kuma sai ki damu? "Amman dai ta bari a yi karin kumallo ko? Shi ma ahmad tun sassafe ya shirya, ya bawa kowa tsarabarsa sai ta matarsa kawai ya bari a cikin jakarsa. Ummansa iri daya ya siyo mata da na Hajiya, sai dai na ummansa ya hada mata da wani babban hijab, domin ya san tana son hijab. Shi kuma malam Sulaiman turare mai kamshi da tsada kawai ya samu da takalmi mai kwari. Hatta yaya sani da yaya auwal sai da ya kawo kusu takalma. Haka malam jibril ma, ita kanta lami sai da ya kawo mata takalmi kito mai kwari, umma ta hada da lemo da ayaba tace ma'un ta shigar musu da shi. Takaici ya cika Ma'u, yaushe rabon da ta shiga gidansu, amman yaya ta iya, dole taje ta amsa ya nufi gidan. *** Su lami suna tsakar gidan, 'yarta amina tana fadin tsefe kitson da tayi mai karin gashi, lami tana gyara mata gashin da ta cire, da alama za a kara yi mata wani DA shi ne. Ma'u ta shigo gidan DA sallamarta mai cike da nutsuwa. Babu wanda ya amsa mata a cikinsu, sai ma binta da suka yi da kallo suna turo baki gaba da nuna tsantsar takaicinsu da ita. Ta karasa kusa DA su ta mikawa lami kayan dake hannunta. "Ga shi umma tace a kawo miki tsarabar yaya ahmad ce..." "Ke ba a koya miki gaisuwa bane mara tarbiyya? Ma'u ta murguda baki "mutanen da ba su iya amsa sallama umarnin ALLAH ba ai ba bukata a gaishe su" Lami ta nuna ta da yatsa tana kada shi. "A Kul dai kika sake kika zage ni, domin na ga take taketakenki kenan, kina ganin kanmu daya dake ko? To auren naki ai mun san da yanda aka yi shi 'yar karoro kawai" Haushi da takaici ya cika Ma'u da jin abinda lami take fada mata. Zuwa yanzu ta mallaki hankalin kanta, ta san meye kishi da bakin ciki da habaici, ta san magana lami ta gaya mata don haka ta ga gwara ta rama ko ta huce. Don haka ita ma ta dubeta a wulakance tace "zaman auren karoro ya fi yawon ta-zubar" Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta nufi kofar fita. Amina ta mike tsaye a fusace tana fadin "ke karamar 'yar iska, ki iya bakinki ki kuma kama kanki, domin naci uwarki a rashin kunya, banza sakarya. Dube ki kina auren wani banza talaka matsiyaci amman kina hurawa mutane anci,