Sashe 23
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasa dakan sanya shi dariya. Ya mike zumbur da sauri yana dariya ya rungumeta a jikinsa, tayi lamo tana ajiyar zuciya tace "yaya don ALLAH ka gaya min abin dake damunka, jikina da yanayinka suna sanar da ni akwai wani abu da ya sameka da kake boye min. Yaya nayi zaton nice sirrinka da dukkan nutsuwarka kamar yadda kake fada min, amma me ya sanya kake boye min wani abu yanzu? Ya shafi kanta mai laushi dake burge shi domin ma'abicumiyar yin kitso ce kanana, duk da bata shamfo, tana da santsi da laushin gashi, yana kuma zuwa har wuyanta. A hankali ahmad yace "ma'u ban boye miki komai ba don baki cancanci na gaya miki ba, sai don nemar miki kwanciyar hankali, amman kila hakan ma ba zai sanya hankalinki kwanciya ba..." Yayi dan shiru kamar ba zai ci gaba DA magana ba sannan yace "an kore ni daga wajen aiki ma'u" Ta janye jikinta da sauri daga cikin nasa cikin tsananin kidima da tashin hankali. "Me kace yaya, an kore ka daga gurin aiki, garin yaya? Shike nan mun shiga uku, wai garin ya hakan ya faru yaya? Ya mai da kan nata kirjinsa ganin tana neman fita daga hayyacinta yana cigaba DA shafar bayanta cikin sigar lallashi. A hankali yace "kwantar da hankalinki ma'u ki yarda dukkan abinda ALLAH ya kaddaro zai sami bawa babu makawa sai ya seme shi. Kiyi mini addu'a ALLAH ya sanya hakan shine mafi alkhairi agare ni DA ku baki daya" Idonta ya fara zubar da hawaye, ta san illar rashin aikin yi, domin wata makociyarsu da mijinta bai DA aiki an kore shi suna cikin matsala da tashin hankali sosai. Hatta ashana sai ta ara ga rokon abinci, har bara wani lokacin yaranta ke yi. Kayansu kuwa haka suke a yayyage gwanin ban tausayi. Idan matar tana bawa ma'u labarin irin halin da suke ciki da kuma irin wadatar da mijin yake DA ita a baya sai taji kamar tayi mata kuka. Yanzu ita ma haka zasu koma ita da mijinta da 'ya'yanta kenan? Maganar ahmad taci gaba da ratsa kunnuwanta. "Ma'u na san zaki ji babu dadi, amman tsira da mutuncina yafi komai muhimmanci cikin rayuwata. Diyar Alhaji Nura Kwangila maigidanmu ce tazo har gurin aikin namu zata ci zarafina" Ta kuma janyewa daga jikinsa tace "diyar Alhaji Nura Kwangila kuma?" Yace "eh ita fa" a hankali ya kwashe dukkan abinda ya faru ya sanar da ita. Bakin ciki da takaici ya cikata, sai taji abinda mijin nata yayi yayi daidai. Ta kalle shi tace "wannan shine dalilin dake sanya ni kara sonka, da kuma yiwa Abba addu'a da duk lokacin da nayi sujjada domin ya zabar min miji daidai da bukatata, ya zabar min rayuwa mafi kololuwar dadi da daraja. Ina son ka yayana" ta fada tana dariya. Wani irin dadi ya cika shi yace "tunda kin ce kina sona bari na gaya miki wani abu" ya kamo kunnenta yayi mata rada ta kankame shi tana dariya, kunya ta rufeta tana fadin "a'a yaya ni dai a'a" suka zube a tsakiyar gadon suna dariya kamar babu wani abu a cikin ransu. Da dare ma'u ta dauko saitin dan kunnenta na gold da ummanta ta sai mata ta mikawa ahmad. Ahmad ya kalleta cike da mamaki. "Wadannan kuma fa ma'u?" Tayi murmushi "yaya kenan, ni fa ban son kayi ta zama haka gara mu fara neman abin yi, na san ka iya rini sosai, to sai kayi ta yin rininka, tunda ga shago a jikin gidan nan sai ka gyara shi, wata kila shine mafi alkhairi" Ahmad yayi murmushi cikin ransa yana godiya ga ALLAH da suka aura masa ma'u. Yace 'ma'u ki bar abinki insha ALLAHU ba zamu Kai ga haka ba, tuntuni wannan tunanin yazo min a rains, amman kin san akwai kudin aikina na kwanaki ashirin da za a bani sai na gyara shagon na san abinda ya dace muyi. Sannan zan ci gaba da raba takarduna musamman abokina ishaq ya koma abuja da aiki, ina zaton zai iya taimaka min yanzu. Ta gyada kai tana fadin "shike nan ALLAH ya taimaka" Ranar lahadi Alhaji Nura Kwangila ya dawo daga tafiye-tafiyensa don yafi sati biyu baya gari. Nana 'yar gata ta sha tsaraba kamar yanda ta saba, dom mahaifinta yana ji da ita kwarai da gaske, ta so yi masa maganar ahmad dake cin ranta amman tana shakkar abinda zai biyo baya, don haka ta ja bakinta tayi shiru, amman ta kasa mantawa da ahmad mai taurin ran tsiya da kuma girman kai a ganinta. Washe gari da safe Alhaji Nura Kwangila ya fice domin bincikar gidajen mansa da sauran kamfanoninsa dake garin. Bai samu isa gidan man su ahmad ba sai rana wajejen karfe daya. Bayan gaisawa da masu zuba mai wadanda ke girmama shi kamar suyi sujjada, Bayan ya kammala ya tadda manaja a ofis dinsa Bayan sun gaisa suka tattauna akan gidan man. Cikin bayanin ne manaja yake gayawa Alhaji Nura Kwangila sallamar ahmad daga aiki da yayi. Mamaki ya kama Alhaji Nura kwangila yace "Saddam dama kana da ikon korar wani ko daukar wani aiki a kamfanina ba tare da na sani ba KO na amince?" Ba tare da ko dar ba manaja Saddam yace "yallabai bani da ikon yin hakan, sai dai wannan din ya zama dole ne domin abin ya shafi diyarka ne Hajiya Nana" "Nana kuma, me ya faru tsakaninta da ahmad kuma?" Manaja Saddam ya kwashe labarin dukkan abinda ya ya faru ya sanar da Alhaji Nura Kwangila yana kallon yanda zai dauki maganar, domin ya san yana matukar ji da nana, amman sai yaga sabanin haka domin yanayinsa sauyawa yayi zuwa bacin rai lokaci guda. Ya dubi manaja yace "aikin banza, akan dan wannan abun sai a kori mutum daga gurin aikinsa? Wannan ba dalili bane" Ya dinga fada ya inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, har sai da manaja Saddam ya raina kansa har yayi da ya sanin aikata dukkan abinda ya aikata. Daga karshe Alhaji Nura Kwangila ya dubi manaja Saddam khan yace "sai ka kirawo shi ko?" Da sauri Saddam ya fara laluben lambar wayar Ahmad a cikin wayrsa. Dakyar ya samo lambar ya fara kokarin kira. A lokacin suna tsakar gida shi da ma'u suna ta wanke kayansu da na yara suna hira. Wayarshi ta fara kara, ya mika hannu ya dauka bayan ya goge hannunsa. Sunan manaja Saddam DA ya gani akan screen din wayar yayi matukar bashi mamaki, har ya ja hankalin ma'u ta kalle shi da tuhuma. Da kamar ba zai daga kiran ba, amma sai ya danna ok ya kara akunnensa tare da yin sallama. Bayan sun gaisa manaja Saddam yace "daman Alhaji ne ke son yin magana DA kai" ga tunanin ahmad Alhaji Nura Kwangila zai yi magana DA shi ne akan abinda ya faru tsakaninsa da diyarsa, koma dai meye baya shakkar abinda zai biyo baya. Saddam ya mikawa Alhaji wayar da sauri cikin ladabi. Alhaji Nura kwangila ya dauka yace "malam Ahmad kana ina?" Gaban Ahmad ya fadi amma sai ya dake yace "ina gida ne alhaji, lafiya?" "Ina son idan kana da dama ka dawo aikinka yau, dukkan abinda ya faru kayi hakuri ka dawo bakin aikinka" Wani irin mamaki da jin dadi ya kama ahmad. Wannan mutumin Alhaji Nura Kwangila mutum ne mai kirki da karamci. Cikin jin dadi yace "To yallabai, godiya nake" kamar zai durkusa kasa. Ahmad ya kashe wayar bayan sun yi sallama ya kalli ma'u DA sauri wacce ke kallonsa ita ma. "Ya ya aka yi yaya?" Ya fasa ihu gami da surarta ya fara zagaye gidan da ita yana ihu da rawa. Ta waro ido tana rokinshi akan ya sauke ta kada ya fadar da ita. Sai da ya gama hajijiya da ita sannan ya direta. Ta kankame shi suna dariya. Yana gaya mata abinda ya faru ta bude idonta cikin farin ciki, amma har lokacin tana rike da shi tace "ALHAMDULILLAHI! Tsarki da godiya su tabbata ga ALLAH. shiga wanka kaje da wuri yaya" ta ja shi da sauri suka nufi bandakin suna dariya. Wannan shine sanadiyyar komawar Ahmad bakin aikinsa. Daga nan shi kuma Alhaji Nura Kwangila gidansa ya wuce ransa a bace. Yayi sa'a ya tarar da nana a gida tana kallo ita da mahaifiyarta, ya rufeta da fada. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Mamaki da takaici ya cika nana akan wani can babanta yau yake yi mata rada. Cikin kuka tace "Daddy ka san abinda yayi min kuwa? Sai ta kara fashewa da kuka. Sai kuma jikinsa yayi sanyi yace "ai kin san na hana ki ciwa dan adam mutunci, baki san irin baiwar da ALLAH yayi masa ba, musamman mutum irin Ahmad mai magana daya da bin dukkan ka'idojin aikinsa. Idan kina son mu shirya dake sai kin sauya wadannan dabi'un naki dole" Sai kuma ya koma rarrashinta. Hajiya Batula ta dinga dariya tana fadin "yau dai na ganku a rana. Ai da idan na fadi laifinta gani kake yi kamar bana son jin dadinta ne" Alhaji Nura kwangila yace "to ina ruwanki ke kuma, wannan magana ce tsakanin uba da diyarsa" Ita dai dariya kawai take yi don jin dadin fadan da yayi mata. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Tun ranar da ahmad yayi mata wannan abun take mamakin waye shi, me kuma ya taka a rayuwarsa har yake yin abin da yaga dama? Abin da babanta yayi mata yau kuma akan ahmad din sai ya kara bata mamaki kwarai da gaske, don haka koda ta isa gadon baccinta kasa rintsawa tayi ta dinga tunanin kamanni da yanayin ahmad, surarshi ta dinga bijiro mata. Ta damu ranta da son gano wanene shi, me yake da shi da yake yin abun da ya so? Dogo ne shi sosai bai DA jiki akwai yanayin karfi da mazantaka a tare da shi. Ba fari ba ne, amman yanayin fatarshi yana da matukar kyau, irinsu ne ake cewa wankan tarwada. Akwai wani gyaran gashi da yake yi wanda ya zagaye bakinsa zuwa kasan hancinsa ko na komai dole a kira