← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 40

Sashe 6

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** Kamar yanda suka saba, kullum sai sun yi meeting kafin su fara aiki da manajojin gidan man, sannan ayi lissafin Abin dake cikin litar kowa. Yau mai gidan man ne baki daya da kansa yazo. Wato ALHAJI NURA KWANGILA 'YAN LEMAN duk ma'aikacin da ya ganshi sai gabanshi ya fadi, domin ya riga kowa isowa Ahmad ne kusan na karshe a shigowa. Gabansa ya yanke ya fadi, amma da ya dubi wayar hannunsa ya ga har lokacin bakwai bata karasa ba, ya dan ji dadi a ransa, domin ya san bai yi latti ba kenan. Bayan duk sun taru babban manajan ya sanar da su ya bude sabbin gidajen mai ne a legas yana son zai debi wasu daga cikin ma'aikatan nan suje su hadu da wadanda za a diba sabbi a can suyi aiki na tsawon watanni uku da su, har wadancan su sami gogewa, don haka kowa ya kasance cikin shiri sunansa zai iya fadawa. Da wannan yayi sallama da su ya tafi, kusan kowa bai son sunanshi ya fada don ba mai son yayi nisa da iyalinsa. Musamman shi ahmad da yake da danyar amarya shakaf, ina zai wuce ya bar ta har tsawon wadannan kwanaki? Don haka a fili da cikin ranshi yake addu'ar ALLAH ya sanya babu shi din. Yana gab da tashi daga aiki yaya auwal ya kira wayarshi bayan sun gaisa auwal yace idan ya tashi daga aiki ya biya ta can gidan. Ya amsa masa da to suka yi sallama. Sanda ya isa gidan yaya auwal matarshi Hafsat ta sanya shi a gaba da tsokana da zolaya, tun yana ramawa har bikinshi yayi shiru da ta fara hadawa har da matar tashi. Yaya auwal yace "kin ga Hafsat idan zaki taimaki yaron nan ki bashi abinda kika ce to, idan kuma ba haka ba yayi tafiyarsa" Ta mike tana dariya ta shiga cikin daki, suka cigaba da hirarsu da yaya auwal. Minti biyu Hafsat ta fito daga dakin hannunta rike da bakar leda ta karaso wajensu ta mika masa. "Amshi wannan ka kaiwa matarka tayi ta karatu Hausa novels ne" "Wai kina nufin irin littafan soyayyar nan ne anti hafsa? "Eh sune tunda yayanka ya bani labarin halin da kuke ciki da ma'u naga babu mafita bayan bata wadannan littattafan tayi ta karantawa, domin idan nace zuwa zan yi da kaina gidan na fahimtar da ita, to zata jima kafin ta fahimci abinda zan koyar da ita har ta koya ta kware, amma cikin wannan labaran zata koyi komai kuma ta san komai" Ya karba yana jijjiga kai, cikin ranshi yana fadin "na zata ai babu komai a cikinsu sai hirar soyayya mara kan gado, amma dai ba a kin ta mutum" yayi mata godiya sannan yayi musu sallama zai wice don yaga dare yana shirin yi masa. Lokacin DA ya iso gidan ya tarar da yara a falon suna ta kallo, amma yana shiga yaran suka fara ficewa. Domin tun ranar da yayi musu barin makauniya suke tsoronsa. Ya tsaya daga bakin kofar rike da labule yana kurawa ma'u kallo da ta kau da kanta gefe tana wasa da yatsan hannunta. "Ma'u baki gan ni bane ba? Na gan ka mana, sannu da zuwa. Ta fada a fili, a ranta kuwa cewa tayi "me zan yi maka kuma? Yayi murmushi don ya san shi mai laifi ne a gurinta ya karasa kusa da ita, ya mika mata ledar dake hannunsa. "Karbi wannan ledar inji aunty Hafsat yace ki yi ya karantawa har ki gama da su cika" Ta leka cikin ledar ya waro ido "duk wannan sai kace wata jaka, na dai karanta wasu kawai" "Duk yadda kika gani haka zaki yi. Me kika dafa ne yau a gidan? Dan wake mana Dan wake ma'u a wannan daren? Ya tambaye ta da damuwa. "Babu kyau ne cinsa da dare yaya? Ta mai da masa da tambayarsa. "A'a ban ce ba, zubo min amma kadan" Ta mike ta nufi kicin din, ya dafa kai cikin zuciyarsa yana addu'ar ALLAH ya sanya ma'un ta sauya sanadin karance-karancen kamar yadda anti Hafsat ya fada masa. *** Washe gari bayan ya fita aiki tayi shiru tunani duk ya cika ranta domin babu yaron da ya shigo mata, kusan kowa yana makaranta. Tunanin kawayenta ya dinga fado mata a rai, tana tina irin rayuwar da suka yi a baya. "Yaya suke yanzu? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta. Idonta ne ya ciko da kwalla damuwa fal a cikin ranta. Can sai littattafan da yayan nata ya kawo mata suka fado mata. Ta mike da sauri ta nufi daki ta dauko su, daya bayan daya dakyar ta zabi daya daga cikinsu ta haye kujera ta fara karantawa. Wasa-wasa dai littafi ya mata dadi har ta kasa ajiyewa. Koda 'yan hirar nata suka zo mata yau bata kula su ba, ko abincin rana bata ci ba, don bata iya tashi ya girka ba balle wanke-wanke ko shara, sai da taga yayan nata yana gab DA dawowa sannan ta mike ta fara gyara gidan. Soyayyar jaruman littafin ta burge ta kuma ta matukar kayatar da ita, domin har sun yi aure sun fara gudanar da rayuwar aure. Nan gurin kam ta jima shi ma tana tunani, wannan shi ne aure kenan? Itace irin hirar da take ji siniyoyi suna yi a makarantarsu, har yayan nata ya tadda ta bayan sallar magriba tana ta karatun. Yayi murmushi ganin yadda ta gwaggwafe ya kula bata san ya biya ba ma. Yayi gyaran murya, ta mike da sauri tana yi masa sannu da zuwa. "Yaya aka yi kanwata, da dadi kenan littafin? "Da dadi yaya, ka yi wanka kaci abinci na baka labari, labarin akwai dadi WALLAHI" Ya kada kai ya wuce. Yana cin abinci tana bashi labarin littafin da take karantawa. Ranshi yayi wasai domin ta fara sakar masa jiki, kuma ya gano karatun zai rage mata kewa da kadaicin makaranta. Haka yayi ta jin labarin yana kada kai. Kwanaki kusan uku kullum idan ya dawo daga aiki da labarin da zata bashi. Yau ya dawo ransa a cunkushe, domin yana daga cikin wadanda Alhaji Nura Kwangila ya sanya a tafiya legas, dukkan abinda zai nisantashi da ummansa da ma'u baya kaunarshi, domin kullum da safe kafin ya tafi aiki sai ya biya duk sammakon da yake yi, ita kanta umma har ta saba, don haka ko da ta idar da sallar asuba bata komawa bacci sai ta cigaba da yin lazimi har sai dan nata ya iso gidan sun gaisa sannan ta koma bacci ko kuma ta tashi ta kama aikace-aikacen gidan. Yau ma'un tana ta bashi labarin amma sam hankalinsa bai tare da ita, har ta gano wani yana damunsa tace "yayana ko baka da lafiya ne? Da sauri ya dago kai ya dubeta "eh bana jin dadi ne ma'u" Gaba daya yanayinta ya sauya zuwa damuwa ta mike "sannu yayana me zan kawo maka? "Kwantar da hankalinki na sha magani ma, ina son dai naje gurin umma ne yanzu" "amman dai da ni zaka je ko? Ta katse shi cikin hanzari. Da sauri yace "A'a ni kadai zan je" "ALLAH yaya tsoro nake ji" Yayi dan tunani yana son zuwa da ita amman ya san zuwa da ita din zai sanya su kasa samun nutsuwa, ganin ba shi da mafita sai ya dube ta yace "bari na kira miki a'ilon gidan kasa ku yi kallo, kin yarda? Da sauri tace "eh na yarda kirata, amma yaya na manta yau fa Hajiya tazo ta kawo maka kaya masu yawa nima haka, kuma tace yana gaisheka, bari na kawo maka kayan" Ya san kowacce Hajiya ce, Hajiya aminansa ce mai sonshi, da sauri yace "kinga barshi sai na dawo tukunna, bari na kirawo miki ita" ya fice da sauri. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. A can gidan umma ta shiga damuwa da jin an tura ahmad legas har tsawon watanni uku, har sai da fuskarta ta nuna hakan a fili. Tace "babu kuma wani abu da za a yi akai din dole sai kaje? Su ba su da tausayi ne ba su san kana da iyali ba? Malam yayi murmushi a fili yace "wai yaushe zaki yaye ahmad ne dije? Abin ya basu dariya ita da Ahmad din gaba daya, tace au haka ma zaka ce malam? Baka tunanin nisan da zai yi? Meye Abin nisa ga Namiji don ya tafi legas, yanzu idan ya samu aiki a can ba zaki bari yayi ba kenan? Tayi ajiyar zuciya "in sha ALLAH ko zai samu aiki a nan zai samu, malam ka dinga yin irin tunanina mana" "Ai tunanin kowa daban ne, na dai san ba za a cinye miki shi a can ba, yanda yaje guda haka zai dawo guda, ki yi masa addu'a da sanya albarka kawai" Ta kada kai "shike nan ALLAH ya tsare yanzu yaushe ne tafiyar? Ahmad ya gyara zama "wajen jibi suka ce insha ALLAHU, ina tunanin kawo ma'u gidan ma gobe zan yi kafin na dawo" "Gidan kuma a kan me? Malam ya katse shi da sauri. "A'a hakan ba zai iyu ba, ka barta a dakinta ta saba da aure. Yanzu ta zama matar aure dole ta koyi juriya irin ta mace mai aure" Yayi dan jimkamar ba zai yi magana ba, sai ya daure yace "gidan zai yi mata girma ne, gashi tana dan tsoro kuma akwai kuruciya har yanzu tare da ita, ina ganin kamar zamanta a nan zai fi tunda kwanakin da yawa. Umma kam tana bayan ra'ayin Ahmad amma ta gaza cewa komai, don kada malam yayi zaton hada baki suka yi. Amma a cikin ranta tana addu'ar ALLAH ya sanya ya amince din, hakan ne kadai mafita. Malam yayi jim yace "shi kenan tunda kana ganin hakan ne mafita, amma da ace tana da karamar kanwa da ita za a kai mata ta zauna har ka dawo" Cikin zolaya umma tace "ko za a kai mata amina? "Ai ba kanwarta bace yayarta ce, kuma idan taje gidan shiririta da shashanci za a yi tayi" _ko kuma ta bata min tarbiyyar ma:u ba_ ahmad ya ayyana hakan a
Chapter 6 · 0% Book details