← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 40

Sashe 2

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi shiru tsawon lokaci kafin ya yunkura ya mike tsaye, ta bushi da kallo tana fadin "yaya har ka koshi kenan? Cabdijan WALLAHI sai ma cinye ta duka, ni daman yunwa nake ji ban ci komai ba tum da rana" Bai ce komai ba ya fice. Kai tsaye dak in baccinsu ya nufa ya haye gado yayi rigingine ya kurawa silin ido yana kallo. Tattaunawarsu da ma'u ta dinga dawo masa daki-daki. Shin ko akwai wanda ma'u take so ba shi ba? Ko kuma dan yayar umma (shu'aibu) shine a cikin ranta? Ya mike zaune da sauri domin jin wani abu ya soki makoshinsa, ya dafe kansa kamar ya fasa ihu. Yaushe damuwa zata bar shi ya huta ne? Tabbas ummi ce abar son sa, amman tun randa aka daura aurensa da ma'u haji gaba daya hankalinsa da rayuwarsa ya koma kanta. Ya san ma'u yarinya ce amman yana fatan samun kwanciyar hankali a gurinta wata rana. Sai dai yau maganganunta sun daga mass hankali. Yana tsoron kada wata rana a wayi gari ita ma tace bata son shi. Ba ta kaunarshi, da kuwa ya shiga ukunshi. Ihun ma'u ya farkar da shi daga tunanin da ya luluka, ya mike tsaye a firgice ya nufi falon yana tambayar abinda ya faru. Ganinta yayi a tsaye tana tsalle. "Yaya Ahmad ba ka ga wutar NEPA ba? Ai ba manta kwan dakin ya mutu zan ci gaba da kallon debate din 'yan makarantarmu yanzu" Yayi ajiyar zuciya ya bita da kallo tana ta kokarin jogana kayan kallon, kamar ya koma sai kuma ya ga yafi dacewa ya zauna yayi kallon, wata kila ya dan samu sauki a cikin ranshi, don haka ya isa ya zauna har ta kammala jonawa, sai dai har suka kwashe awa guda babu wani abu da gidan talabijin din na N.T.A ke sakowa bayan talla da labarai, har ta fara zobaro baki gaba tana mita. Yayi murmushi yace "kin ga ma'u daman ba kullum ake yi ba, sanya mana receiver ki kunna mana MBC ACTION muyi kallo. "Gaskiya yaya sai dai mu ga ZEE AFLAM" "Na ji kunna mana ZEE AFLAM din mu gani' ya fadi yana dariya don ya kula ta cika. Ta kunna daidai lokacin da suke wani fin, suka yi shiru suna kallo. Ma'u da kanta tace fim din ba shi DA kyau. Ta sauya zuwa MBC ACTION a hankali wani fim ya fara fitowa THE DIRTY TEACHER, kasancewar ma'u na jin turanci ya sanya fim din ya shiga burge ta, sai dai ga Ahmad wani irin abu ya dinga ji a jikinsa yana yawo. Hankalinsa ya fara kasuwa gida biyu, ya dinga satar kallon ma'u babu wani abu a jikinta da zai iya gamsar da shi, sakar da azuciyarsa ta fara yi masa dama ummi ce matarshida tayi masa abinda yake so a yanzu, ya mike da nufin ya bar gurin. Ma'u ta kwalla masa kira. "Don ALLAH yaya ka tsaya mu gama gani mana, ni wannan shegiyar malamar ta babu haushi haka kawai ya raba masoya, ta kuma koya nasa iskanci, shikenan yanzu ya zama dan iska" Bai kula ta ba ya fice yana fadin "ina zuwa ma'u" ta cigaba da kallon ko a jikinta. Haka rayuwar tasu ta ci gaba da gudanuwa, kullum ma'u sai kara girma take halittun jikinta na kara bayyana. Shi kuma Ahmad sonta da sha'awarta na kara karuwa cikin ransa. Sai dai tsananin tausayinta ya hana shi aikata komai a kanta, hasalima ko gado daya bai bari su kwanta da ita ba. Ita tana gado shi yana kasa kan leda da filo ya wurgar haka ake baccin kullum. Ta saki jikinta da gidan domin ya bar yaran suna shigo mata su taya ta hira, su yi ya wasansu irin na yara. Sannan yana koyar da ita girki har ta soma iyawa. Sai dai abinda yake damun ta bai wuce rashin zuwan umma gidan ba. Gashi tayi kusan watanni goma sha uku, kuma shi yayan nata ya ki barinta taje, bayan shi kullum sai yaje, yana lallabata dai akan ta yi hakuri. Zaman aure kenan ma'u mai raba uwa da diyarta na tsawon lokaci. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Yau tun safe ya fice aiki ya bata damar ta dafa shinkafa da miya, domin ta iya yanzu, amman kada ta bari kowanne yaro ya fara shigar mata kicin. Zuwa yanzu ma nutsuwa ta fara shigar ta, duk wannan shiriritar ta 'yar auta ta fara dainawa, ta iya gyara gidanta tsaf kamar ba shi ba. Ta share ta goge ko ina, girma in dai ba mai wahala bane tana kokarin yinsa, iyakacinta da yaran aike kawai, ko su yi mata wanke-wanke da shara. Wajen karfe bakwai ya iso gidan, abunda ya bashi mamaki bai wuce yin horn da yayi sama da sau uku amman ma'u bata zo ta bude masa gidan ba, domin da yayi horn daya biyu a na ukun zata fallo ko ya jiyo muryarta tana fadin "yaya ina zuwa" Amman yau yayi yafi sau shida bai jiyo motsinta ba, sai ya matsa jikin kofar gidan sosai ya tura da hannunsa sai yaji kofar ta bude, ya shigar da mashin din ya sami guri ya ajiye shi, ga mamakinsa sai yaga gidan kaca-kaca babu gyara kamar yadda ya saba gani. Ransa ya dan baci da ya jiyo karara talabijin, da alama kallo ne ya dauke mata hankali, ta manta da gyara har da bude masa kofar ma. Yayi nufin isa dakin ya jiyo kauri daga kicin, don haka ya nufi kicin din da sauri, shinkafa ce akan risho ta kama har ta kusa konewa gaba daya, miyar kuma gata can gefe murfin a bude hangam. Takaici ya kara kama shi, me ma'u ke yi yau na shiririta ne a gidan? Ya sauke shinkafar ya kashe rishon ya nufi dan falon nasu, ko bai daki ma'un ba zata sha fada. Ya daga labulen yana kwalla mata kira, ga mamakinsa sai ya ga babu kowa cikin dakin sai TV dake ta faman babatu ita daya, daga sannan hankalinsa ya fara tashi, da wutar nepa babu ma'u a gaban TV tana kallo, lallai akwai matsala. Me ke faruwa ne? Sai ya saki labulen da sauri ya nufi dakin gado yana ci gaba da kiran sunanta. "Ma'u! Ma'u!! " ya daga labulen yana wara ido ko zai hango ta, amman babu ita ma acikin dakin babu alamunta. Hantar cikinsa ta kada, a fili yace "na shiga uku, ina ma'u ta shiga ne? " "Ma'u!!!" Ya sake kwalla mata kira da karfi. Sai ya jiyo kamar shisshikar kukan mutum daga bayan gado. Ya shiga cikin dakin da sauri yana ci gaba da kiranta. Ga mamakinsa sai ya hango ta rakube a bayan gado ta tattare jikinta kamar wacce aka sanya a haka dole. Mamaki ya bayyana akan fuskarsa ganin yadda take ta hada gumi idanta jajur alamun taci kuka ta koshi, sai ajiyar zuciya da shisshikar kuka take ta yi. Ya isa gabanta yana tambayarta "ma'u lafiya, me ya faru, me ya same ki?" Sai kawai ta kara fashewa da kuka tana ja da baya tana fadin "don ALLAH yaya Ahmad kada ka dake ni, kaine kace ba zaka kara dukana ba, ko me nayi maka. Na rantse da ALLAH ban yi ban yi iskanci da kowa ba, ban yi irin abinda raliya tayi da sisco ba, ka kawo Qur'ani na dafa" Mamaki ya kara kama shi DA tsoro ganin yana kara nufarta tana kara ja da baya jikin lungu, ya dan dakata ya kwantar da hankali yace "tsaya ma'u, gaya min me ya faru ba zan dake ki ba na rantse da ALLAH ko me kika yi ba zan dake ki ba, ko baki san kin girma ba yanzu, ko umma ma ba za ta dake ki ba balle ni, me ya faru gaya min mene ne? Cikin shisshikar kuka tana kara tattare jikinta tana kudundunewa tace "amma dai ka san ni ba 'yar iska bace ko yaya? Ya daga kai cikin rawar jiki. "Na sani ma'una saliha ce, ba 'yar iska ba, me ya faru, wani ne ya shigo gidan yayi miki fyade ne ma'u? Ki gaya min zan iya daukar dukkan abinda ya faru a kanki, na san kaddara ce" "Ka ji har ka fara fada tun ban gaya maka ba. WALLAHI ban yi iskanci da kowa ba yaya, ban yi komai ba. Ya fara fusata. "Haba ma'u ki sanar da ni me ya faru? Ki gaya mini meye ne? Cikin karaji da ihu yayi maganar. Maimakon ta dawo cikin nutsuwarta sai ma ta kara gigicewa kamar zata shiga cikin gadon ta fashe da kuka mai karfi, jikinsa yayi sanyi ya gano ya tafka wauta. Ya dube ta yace "ok, calm down ma'u yi hakuri gaya min mene ne?" Ganin bata da niyyar magana ya sanya ya faki numfashinta ya cafke hannunta ya daga ya cak, sai ta sake fashewa da ihu ta kankame jikinta kamar zata suma, fadi take "WALLAHI ban yi iskanci da kowa ba yaya, na rantse da ALLAH" Gabansa ya dinga faduwa ganin jini guda-guda a jikin zaninta da gurin, ya bata gurin gaba daya, hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske, ta kasa ci gaba da kukan. Cikin karaji yace "ma'u meye wannan, me zan gani haka, ba jinin al'ada bane irin naku na mata ba..." Cikin kuka tace "ni ma da farko na zata irin abinda wasu kawayena keyi ne MISTRATION idan suka sanya audiga da ake goge hanci da shi kenan sai ya tsaya, ni kuma ba sanya sai ta jike na kara sanyawa ta kuma jikewa, sai kuma jini ya dinga zubowa bayan ban yi komai ba, WALLAHI ban yi komai ba" Abun ma sai ya ba shi dariya, duk da jinin ya zuba da yawa, ya saki hannunta domin ta dan sami nutsuwa sannan ya fara magana. "Ba komai bane ma'u, kowacce mace da yanda take fara yin al'adarta, amma zo ki cire kayanki ki yi wanka sai muje chemist mu ji ko wata matsalar ce" Ta yi doguwar ajiyar zuciya da jin dadi, ta ma manta da yayan nata yana gabanta ta fara kokarin cire rigarta da sauri, bai yi
Chapter 2 · 0% Book details