← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 40

Sashe 28

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ransa gaba daya kamanninsa suka sauya, idanunsa suka fara yin jawur, kirjinsa ya sauya bugu zuwa da karfi ya dai daure ya danne fushinsa yace "Ummi ya kamata mu bar tuna duk abinda ya wuce, mu baiwa juna wani labarin idan muna da shi ba wannan ba, wannan tamkar fama gyambon da ta jima ne" Tayi ajiyar zuciya gami da cewa "haka ne amman kai ai baka da wani labari da zaka bani bayan na auren ma'unka da samun cigaba a rayuwarka, sabanin ni Ahmad. Bayan rabuwata da kai mutane da dama sun yi ta zuwa neman aurena daga karshe dai ni da iyayena hankalinmu ya tsaya akan Salim, wani matashi mai ji da kyau da kuruciya, babana yafi kaunar asalin Salim fiye da komai a rayuwarshi, don ya kasance JININ SARAUTA ba da jimawa ba aka yi bikina da Salim. Kamar yadda Salim ke nuna min kauna haka ya dinga nuna min ita a gidansa har tsawon wata guda kafin mugayen hakayensa su fara bayyana. Duk wani abu da ka sani na bugarwa Salim yana shan shi, ga neman matan tsiya da dan banzan yawo, tun ina boye halin da nake ciki har iyayena suka fara fuskanta don na rame na fita daga hayyacina, bani da kwanciyar hankali sam ga dan banzan duka da nake sha a hannun Salim, iyayesa kuma tamkar kurame, domin sun toshe kunnuwansu daga duk wani kukana game da dansu, sai a sannan na gano Salim dan iyayene maras tarbiyya. Shekararmu biyar ina cikin wuya da tashin hankali, danmu daya. Kwatsam wata rana Salim ya dawo a buge daga yin magana ya rufe ni da duka har da karaya a hannu, wannan shine ya kawo karshen aurenmu domin na gaji da azaba, iyayena ke tausaya..." Tayi shiru tana maida numfashi, idonta ya cika da kwalla ta cigaba "shekaru uku da mutuwar aurena na kasa samun wanda ya dace da ni da burikana. Ahmad ka tuno Ummi da soyayyarta cikin ranka?" Gaban Ahmad ya fadu, Ummi ta dawo da shi ruwa tsundum, amma ya dake yace "Ummi ko kin manta kina magana da Ahmad ne SHEGE dan gidan Asma'u mahaukaciya? To nine yanda kika san ni ba a sauya ni ba, kuma ba a siyo min uba a kasuwa ba. Me zaki yi da shege Ummi? Hankalinta ya tashi ta kankame wayar tana fadin "WALLAHI ban ga laifunka ba akan dukkan abunda zaka fada, amma ka sani ko mahaifana sun yi da na sanin raba mu da suka yi, don sun gano wani maras iyayen yafi mai uwa da uba daraja da hali nagari. Ka yi hakuri Ahmad ka manta da dukkan abunda ya wuce." Yayi shiru bai ce mata komai ba yana ta maida numfashi har sanda muryata ta kara sauya masa tunani da fadin "Ka yafe min Ahmad" Yanda tayi magana ya sanyaya dukkan gabbansa, bai san sanda yace "na yafe miki ummi." Wani irin dadi ya cikata tace"na gode Ahmad, fatan zamu dora daga inda muka baro a soyayyarmu? Yayi wani tari da bai shirya ba yace "Nan fa daya, ai ma'u ce kadai matata a duniya insha ALLAHU. Farin cikinta ya gushe lokaci guda tace "ka yiwa ma'u alkawari ko rantsuwa cewa ba zaka yi mata kishiya ba Ahmad? Ya kada kai "ko daya ban taba yi mata wannan alkawarin ba, amman na sanyawa raina hakan, iyayen da suka rike ni suka mai da ni mutum kamar kowa, suka raine ni sanda ban san kaina ba, suka bani aure sanda na rasa shi yaushe zan hada son diyarsu da na wasu matan? Ba zan iya ba koda ma'u ace azabtar da ni take ba zan iya hada ta da kowacce mace ba, balle ina cikin mazan da ke cikin sa'ar aure da iyali a duniya, don haka bana bukatar kari sai dai nayi miki addu'a Ummi ALLAH ya baki wani mijin da yafi mijinki na farko alkhairi da ni kaina." Amman sai ta fashe masa da kuka tana fadin "don ALLAH kada kayi min haka Ahmad kada kace zaka Rama dukkan abinda na aikata maka, ni mace ce ba zan iya dauka ba" Jin Kalamanta zai iya karya masa zuciya, bayan kuma ya san ko kukan jini zata yi ba zai taba yi mata abun da take bukata ba, don da ma'unsa tayi kuka g ara kowacce mace a duniya tayi kukan jini idan an cire ummansa don haka da sauri yace "kiyi hakuri Ummi sai an jima" ya kashe wayar. Ya koma jikin kujera ya kwanta, tausayin Ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zucuyarsa har bai san sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa ya daga kai da sauri tamkar wanda ya farka daga barci. Nana ce ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance "Sorry Hajiya na tafi wani dan tunani ne" "Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka bai yi kama da komai ba sai na soyayya. Ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne?" DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Nana ce ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance "Sorry Hajiya na tafi wani dan tunani ne" "Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka bai yi kama da komai ba sai na soyayya. Ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne?" Yayi yake me ya sanya tayi saurin gano shi? Amman ya dake yace "waye ya gaya miki haka? Mu bar wannan maganar mu koma ta aikin da ya shigo dake" Ta ja kujera ta zauna ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace "yau ba aiki ya shigo da ni ba, hira ce ta kawo ni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don ALLAH ka gaya min ka taba soyayya Ahmad? Tambayar ta zo masa a bazata cikin mamaki yace "me ya sanya kika yi min wannan tambayar? Ta gyara "domin na gano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka ba zan yi kaffara ba ban taba soyayya ba, ban taba jinta cikin jikina ba a baya, dukkan rayuwata na karar da ita ne haka ban taba surkata da soyayya ba, ban taba son wani ba, hakan ne ma ya sanya iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aure ni, sun ce sai anyi da gaske zai bar ni nayi aure. Su fa sun yarda da hakan shi yawa suke lallaba ni da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa min akan nayi aure, don an fada musu da sun fada ko sun matsa min zasu iya rasa ni daga lokacin, don aljanin wai zai gudu da ni ne" Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada. Tayi ajiyar zuciya ta cigaba da magana "Ahmad babu abunda iyayena suke bukata a Yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna tsoron fada min haka, na san dukkan abunda aka gaya musu na kuma san karya ne, amman na bisu a haka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarara nan, shine ya dawo min da rayuwata irin ta mutane wadanda ke dandanar kalma da aman soyayya" Gaban Ahmad ya kama bugawa ganin irin kallon da take yi masa, amman sai ta basar ta kau da idonta da ya ciko da kwalla tace "bani labarin tsohuwar budurwarka ko ita ce matarka ne? Yayi murmushi yana kallonta ta kau da kanta gefe. Yace "ke da Bali san amo da dandanon soyayya ba ya kika gane ina cikin soyayya? Ko kuma na tuno da tsohuwar budurwata ta da? Tayi murmushi "kuma fa haka ne kana da gaskiya, amman ina zaton na gano hakan ne cikin littattafan soyayya na turawa da nake karantawa, ko kuma a yawan kallon fina-finansu. Ko ma dai meye sai ka bani labari nan yau" Yayi dariya "lallai da gaske kin shiga cikin soyayya, amman babu abunda zan iya gaya miki bayan na ce miki Ummi ce tsohuwar budurwata ta bugo min waya bayan ni kuma na ma'u ne ita daya" Gabanta ya fadi yanayinta ya sauya zuwa damuwa dakyar ta iya daurewa tace "wacece ma'un? Ya jingina da kujera yana murmushi tamkar tayi masa albishir da gidan aljanna. Yace "ma'u itace matata, mai sona, mai daraja ni fiye da yadda ya kamata a min, ban hada ta da kowa ba cikin raina da al'amuran rayuwata ba" Cikin gaggawa da rashin sanin abinda ta fada tace "Har ni ma?" Shirun da yayi yana kallonta ne ya sanya ta gano ta fadi wani abu ne da ya jima a ranta tana nuku-nuku da shi. Sai ta dauke kanta daga kallonsa da sauri ta kalli gefe gabanta na faduwa. Dakin yayi shiru sai karar AC da ta bugawar zuciyoyinsu. Ahmad kam addu'a yake a ransa ALLAH ya sanya abunda ta fada ba shi take nufin fada ba, amma sai ya jiyo sautin muryarya na cigaba da fadin "maza da dama sun so ni, masu kudi da masu mulki da sarauta, amman ban taba kallon kowa da mutunci ba tunda ban san meye SO ba, sai kwatsam wata rana na ci karo da wani tsageran matashi a gidan mai wanda ya tsaya cikin raina har ya karya tarihin zuciyata, tun ina yaudarar kaina da cewa zuciyata karya take yi ba zan taba son mutum irin haka ba har daga baya na sallama na yarda ina son ka Ahmad" Ta waigo ta kalle shi yayi mutuwar zaune. Ta cigaba da magana idonta yana zub da hawaye. "Na san ka jima da gano ina sonka domin na gwada maka abubuwa da dama irin na masoya amman kana basarwa na san ba don komai bane sai don ma'unka. Sai dai ina fatan zan ci albarkacin ma'un ka sammin kadan daga cikin son da kake yi mata" Tana kaiwa nan ta mike tsam da sauri ta nufi kofar fita. Ahmad yana zaune kamar an dasa shi ya kasa motsawa daga inda yake yana jin kamar ba shi bane ba. Yabi Nana da kallo wacce ta kama kofar
Chapter 28 · 0% Book details