Sashe 3
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zaton ganin abinda ya gani ba. Yaushe ma'u ta zama haka? Ashe ta zama mace cikakkiya bai sani ba. Bugun kirjinsa ya fara sauyawa, sai ya Kau da kansa da sauri yana kokarin nemo nutsuwa, ya sanya cikin ranshi sai ma ya fice da sauri ya bar dakin domin ya kula bata cikin nutsuwarta, cire kayan take son yi gaba daya, yau babu 'yar kunyar da take nunawa a gabansa saboda bata cikin nutsuwarta. Ta dauko wani zanin ta daure, kafin ta fito ya zuba mata ruwa cikin bokiti ya sanya mata a bandaki, tana fitowa yace "maza shiga bandaki kiyi wanka" ba tare DA ya kalleta ba ita ma bata kula da komai ba kawai ta nufi bandakin. Yana shiga ya shige cikin dakin da bokiti a hannunsa ya fara kwashe kayan nata da suka baci, yayo waje da su, sannan ya fice domin siyo mata audigar mata (pad) Har ya dawo tana cikin bandakin bata gama wankan ba, hakanya ba shi damar gyara dakin. Yana tsaka da gyaran ta shigo da sallama, ya daga kai da sauri ya kalleta yana amsawa. Cikin shagwaba tace "yaya na gama amma har yanzu yana zubowa kadan-kadan" dariya ta kwace masa ya daga kai yana kallonta. "Wai ke wacce irin sakarya ce ma'u? Amshi nan ki sanya da pant dinki, ai kin san yadda ake yi ko? Ta daga masa kai alamar eh ta sani. "Yauwa shirya kafin ni ma na watso ruwa yanzu na dawo, na dan gaji" Ya amsa ya fice. Shi ma ya juya domin shiga wankan, amma zuciyarsa tana cigaba da sakawa da kwancewa. A haka dai don wautar ma'u ta dage wai sai sun je chemist din yaya auwal. Saboda burinta kawai ta shiga gidansu don ta ha ummanta. Ahmad ya gyada mata kai yana fadin "sannan ba abun damuwa bane amma ki tabbatar idan mun je ke da bakinki zaki yiwa yaya auwal din bayanin komai ba ni ba, kin yarda da hakan? Sai a lokacin ta gano wauyar da take shirin yi ya fashe da dariya tace "kai na fasa, WALLAHI yaya kunya nake ji, sai dai muje wani chemist din. Amma don ALLAH idan mun je wani chemist din zaka kai ni naga umma da baba? Don ALLAH yayana ka taimaka min na dade ban gan su ba" tana maganar ne cikin shagwaba. Ya kada kai yana kwaikwayon maganarta "sai abinda hali tayi, wuce kawai muje" ta fashe da dariya tabi bayansa suka fice daga gidan. A haka suka je chemist din wata ma'aikaciyar jinya da take dan taimakawa a cikin unguwa idan dare yayi. Duk karadin ma'u kasa yi mata bayani tayi, sai rufe fuska da dariya kawai ta iya. Aunty Deejah ma'aikaciyar jinyar ta dinga dariya tana zolayar ma'u. Daga karshe ta yiwa Ahmad bayanin babu wata matsala daman wasu matan sukan yi haka a farkon fara al'adarsu, amma da sun yi sau daya shi kenan, idan zasu kara yi jinin baya zuwa kaman farko. Ta ba su magunguna da shawarwari sannan suka bar gurinta. A hanya ma'u ta yi shiru taga inda yayan nata zai kai su, domin taga ba hanyar gidansu suka yi ba. Ga mamakinta sai taga kamar hanyar gidan su ummanta aka nufa, tayi shiru dai ta shanye murnarta, saidai sanda taga sun shiga layin dadi ya cikata har ta gaza boyewa sai da ta rukunkumeshi tana zabga ihun dadi. Da fari ya dan tsorata da yanda yaji ta makalkale shi har suka kusa faduwa, amma da ya gano murnar jin dadi ce sai ya saki ranshi, amma rikon da tayi masa ya kara tsinka jijiyoyin jikinsa, cikin ranshi ya fara korafin abinda yarinyar ke masa cikin wannan lokaci, ya gaza jurewa yana ganin zai iya karya alakwarin da ya daukarwa zuciyarshi na barin ma'u ta zama cikakkiyar mace, ta san kanta kafin ya tunkare ta da wasu al'amura na aure. Haka dai ya daure ya karasa kofar gidan ya tsaida babur dinsa. Yana tsayawa tana dira tun bai karasa tsayawar ba. Caraf ya cafko hannunta ganin tana shirin zurawa da gudu tayi cikin gida. "Ma'u baki da hankali gudu zaki sanya a tsakiyar titi? Ko baki san ke matar aure ba ce yanzu? Sai ki sanya mu koma WALLAHI ki fasa shiga gidan" Ta kwantar da kai cike da fargaba domin ta san kadan ne daga abinda yayan nata zai iya aikatawa ne. "Yi hakuri yaya Ahmad ba zan kuma ba" Ya saki hannun nata yana girgiza kai. "To ki tsaya mu shiga tare, bana son zumudi na gaya miki" Ta kada kai kawai ta kasa cewa komai, amman murna da zumudi sun cikata ta dan daure ya tsaya ya gyara tsayuwar babur din ya kulle shi sannan suka nufi cikin gidan. Yaya auwal yana cikin chemist dinshi a zaune ya hango su, tun daga nesa ya fara wangale baki da fara'a don ganin yadda ma'unsa ta zama bukekiya. Suna gab da shagon ma'u ta kufce ya fella da gudu tayi cikin gidan domin ba zata iya jure wannan jan ran da Ahmad din ke yi mata ba. Ahmad ya bita da kallo DA tsananin mamaki kafin ya fashe da dariya. Yaya auwal ma ya fito daga cikin chemist din yana babbaka dariya yace "hoo ma'u autar mama wai haka take daman har yanzu bata yi hankali ba Ahmad? Ahmad yayi dariya "da sauki dai har yanzu yaya" ya mikawa yayan nasa hannu suka gaisa suna cigaba da dariyar duk su biyun. Yaya auwal ya cigaba da magana "rufe chemist ya kama ni domin ya zama dole naje naga autar umma don kada umma tayi fushi da ni" Suka sake yin dariya, sannan suka rankaya suka yi cikin gidan gaba dayansu bayan yaya auwal ya rufe chemist din nasa. Hajiya ma'u yau an zo ganin gida ai ko dole ki zumudi DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. A can cikin gida umma da malam suna zaune suna kallo kasancewar akwai wutar nepa. Labaran karfe Tara suke kallo. Ma'u ta shigo a guje ta manta babu ko sallama ta fada dakin tana kwallawa umma kira. Da sauri suka juyo suna kallonta don fargaba. Umma kam kasa magana tanata, sai malam ne yayi karfin halin daka mata tsawa lokacin da ta iso ta fada cinyar umma tana dariya. "Ke ma'u lafiyarki kuwa! Hala kina yin hauka ne ko? Cikin dariyar farim ciki tace "yi hakuri baba, WALLAHI dadi ne ya cika ni na dade ban gan ku ba, ina yini? Umma dai kallon autar tata take yi bakinta ya ki rufuwa domin ta koma wata babbar budurwa. Malam ya daure ya hadiye fadan domin yayi murna da ganin autar tasa yace "har kullum dai ba zaki daina sakarci ba, ina mijin naki yake kuma? Ta rike baki tana dariya. "Umma kinji abinda baba yace wai mijina maimakon yace yayana" abun ya ba su dariya gaba dayansu, suka bushe da dariya umma na shafa kan ma'un tace "ho autata na ga ran da zaki daina shiririta WALLAHI" Daidai lokacin auwal da Ahmad suka shigo. Ma'u ta kalli yaya Ahmad tana yar dariya tace "yaya ba zan kara gudu ba, ALLAH yanzu ma na kagu na ga ummata ne" ya kada kai yana murmushi bai ce komai ba. Yaya auwal yayi hararan wasa yana fadin "ni kuma meye laifina da aka ki tsayawa a gaishe ni? Ta rufe fuska tana dariya "yaya ina yini" bana cin kwantai" ya bata amsa. Umma tana dariya tace "duk kin cika mu DA surutu kin hana ni gaisawa da dana. Manya yaya aka yi ne sai ga ku da dare kuma, lafiya?" Ahmad ya sami guri ya zauna yana dan yake yana satar kallon ma'u da ta fara raba ido yace "lafiya lau mun zo kawai gaishe ku ne, baba ina yini" malam Sulaiman ya amsa da sakin fuska sannan ya gai da umman tashi. Daga nan aka balle da hira ana ta dariya. Ma'u dadi ya cika ta tana ji kamar kada ta koma gidan mijinta. Shi kansa Ahmad hirara tayi masa dadi, ji yake kamar kada ya bar gidan iyayensa, domin hira cikin iyayensa da danginsa yafi komai dadi. Malam ne ya fara ankara yace "kai sai yaushe zaku tafi ne, naga kun tsare su sai hira kuke sharba dije' Umma tayi dariya tana fadin "ni babu ruwana, su tafi mana ai ban hana su ba" ma'u ta turo baki gaba kamar zata fashe da kuja. "Ni dai mu kwana a nan don ALLAH baba" "Kwana kuma? Malam ya tambaya. Ahmad yace "eh gobe said mu wuce da safe" Auwal ya fashe DA dariya "kar dai ace yarinyar nan ta koya maka irin shiririyarta Ahmad banda haka kawai sai ku kwana gidan babu dalili? Ya mike tsaye "gwara na wuce ni domin naga baku da niyyar tafiya" "Ai tafiya ya zama dole kuwa. Ku tashi ku wuce gidanku" inji malam. Ita dai umma murmushi take yi idan zasu kwana anan din haka take so. Ta samu damar ganawa da diyar tata. Domin ta gaya mata dukkan abinda take son gaya mata. Saboda ta kasa zuwa gidan nasu. Duk DA tana son zuwa. Malam ne ya hana ta yana cewa wai me zata je yi gidan yaran tunda suna zaune lafiya ai shike nan. Haka dai ma'u ta tashi tana kumbura sai ga hawaye ya zubo mata, malam ne ya hau salati yace "Asma'u kuka kuna? To daga yau kin daina zuwa gidan nan tunda haka ne, kar ka kara barinta tazo ahmad" Sai ta fashe da kuka tana fadin "baba kayi hakuri, shine yake hana ni zuwa ko ina, idan na tafi yau ban san randa zan kara zuwa ba" "Hakan ya kamata yayi, ku je don ALLAH idan muka biyewa shiriritar Asma'u sai ku yi dare" Gana dayansu suka nufi kofa banda umma da ta Kamo hannun Asma'u da sauri ta ja ta baya. Dadi ya cika Asma'u don tayi zaton cewa zata yi ya zauna, amma sai taga ta hau ta DA fada amma cikin nasiha. "Kina jina asma'u yanzu kin zama matar aure ba iri daya kike da rayuwarki ta baya, don haka sai kin nutsu kin yi komai yadda ya