← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 40

Sashe 29

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata bude, har sai da ta bude sannan ta kuma yin magana ba tare da ta waigo ba. "Ahmad ka sanya a ranka cewa ba karamin abu bane zai sanya mace kamata mai cika da daraja da kyau da arziki ta fuskanci namiji kamarka ta sanar dashi tana son shi ba" tana fadin haka ta fice. Ahmad ya doki tebur ya dafe kansa dake juya masa yana fadin "Ya Subhanallah! Lallai lokacin barina cikin wannan daular ya kusa" Ya koma ya zauna ya dafe kai, ya ma rasa me ya kamata yayi. Kiran wayar ma'u ya cika kunnuwansa amman ya kasa daga wayar. Rayuwa kenan Ahmad wacce ke cike da kalubale mabambanta. Fatan ALLAH ya ba mu ikon cinye dukkan jarrabobinmu Ameen DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Duk kwanakin da suka biyo bayan wadannan cike suke da rudani da tashin hankali ga Ahmad. Matarshi ta kasa gano kanshi, da farko hankalinta ya tashi, domin tayi zaton matsalar Ummi ce, sai dai sanda yace mata ta taya shi addu'a wani abu mai girma ke faruwa a ofis dinsu da yake shirin raba shi da aikinsa, sai tunaninta ya bar can ya koma kan dalilin da zai sanya a kori mijinta daga aiki. Shi ma wannan tunanin bata bashi dama ba addu'a tafi yawa a cikin ranta, domin wannan aikin shine rufin asirinsu da shine rayuwarsu da ta yaransu ta sauya baki daki. Makarantu da kayan da suke sanyawa da jin dadin da iyayenta da 'yan uwanta ke ciki kadai ya isa ta rike amfanin aikin cikin ranta da kuma yiwa mijinta addu'a akan ALLAH ya daidaita ko ma menene ya cigaba da aikinsa. Janye hankalin ta daga kan tuhumarsa da takeyi ya taimaka masa kwarai da gaske gurin sauwake masa irin tarin matsalolin dake kanshi, domin bata damu da wayarshi ba balle bincikar wayarshi ba da ta ci karo da sakonnin Ummi kala-kala wanda da sun shigo yake gogesu. Nana kam bata yi masa sako, sannan ta daina shiga ofis dinsa, sai dai su hadu a hanya ko gurin meeting, wannan zuru din da tayi masa shi yake damun sa. Game da Ummi kam yayi banza da komai nata har ta fara yin fushi, amma lamarin Nana kam yana daure masa kai kwarai da gaske, ya rasa gane me take nufi da shi. Nata haukan bai kwantar masa da hankali ba sai ma kara tsorata shi da yake yi. Yau yayi yamma gurin kammala ayyukansa, don har kusan magriba yana ofis, daidai lokacin da ya kammala ya fara kokarin tattara kayansa aka turo kofa aka shigo da sauri ya dago kansa ya kallo kofar ofis din. Nana ce ta shigo ta dan tsaya bakin kofa tana kallonsa tsawon lokaci, sai kuma ta kada kai ta fara karasowa kusa da shi. Gaba daya jikinsa ya sankame kamar jini bai zagayawa cikin jijiyoyin jikinsa. Cikin ransa addu'a yake yi ALLAH ya sanya ba waccan maganar zata yi masa ba. Ta karasa ta ja kujera ta zauna tana murmushi tana kallonsa yayi tsumu-tsumu kamar an tsamo shi daga cikin ruwa. "Da alama baka yi farin ciki da ganina ba ko? " Yayi yake cikin borin kunya yace "waye ya gaya miki haka?" Yanayinka ne ya sanar da ni" ta bashi amsa a takaice. Bata barshi yayi magana ba ta cigaba da magana "ka kasa gaya min amsar tambayar da nayi maka, na kula ma kamar mun fara wasan 'yar buya da kai, da ka gan ni ma sai ka dinga boyewa kamar baka son ganina. Ahmad na san baka sona..." Cikin sauri yace "me ya sanya kika ce haka Nana? "Ba ni nace ba yanayinka ne ya nuna haka, ka taba jin wanda ke son abu an kawo masa tallan abun ya kau da kai? Da ace da gaske kana sona ba zaka bari na bar nan ba tare da ka gaya min kana sona ba" Tayi shiru idonta ya ciko da kwalla. "Wai ace kamar ni mace mai mutunci da daraja na zo ina rokon namiji ya soni, hakan abin kunya ne kwarai da gaske a gare ni" Ahmad ya kada kai "ba abun kunya bane ba, ko baki ji labarin Sayyada Kadija macen da tafi kowcce mace daraja a duniya, ita ce ta sanar da Manzon ALLAH (SAW) tana son shi ba. Ina ganin wannan ba sabon abu bane tunda ya samo asali daga babban tushe" Tayi murmushi da jin dadin abin da yace "idan haka ne me ya sanya kake yunkurin watsa kasa cikin idona? Ka san ba karamar matsala bace zata sanya na iya fitowa nace maka ina son ka Ahmad. Wallahi mutanen dake sona ba zasu kirgu ba, amman ni kai ALLAH ya dora min son ka... Ka ce wani abu Ahmad ko naji dadi a raina, kada ka yaudare ni amman ka gaya min gaskiya" Yayi shiru kansa akasa tsawon lokaci, ta kasa dauke idonta daga kansa. Sai da ya jima sannan ya dago ya kalle ta yace "Nana WALLAHI tun ranar da naji sunanki ASMA'U sonki da kaunarki suka shiga raina, amman bayan kin furta min kina sona sai naji tausayinki ya dami zuciyata, idan nace miki bana sonki nayi karya, sai dai ba irin son da kike bukata bane, wato ba soyayyar aure ba, ina miki so irin na 'yan uwantaka. Nana ba zan boye miki komai ba, Ma'u ce kadai matata har abada har karshen rayuwata. Wannan wani alkawari ne da na daukarwa kaina da rayuwata. Kiyi hakuri Nana" Idonta ya fara zubar da hawayen da ya taru, ta kada kai tana zubar da majina tace "ba zan matsa maka ka soni ba, Sai dai ka sani daga yau har na koma ga ALLAH ba zan taba son wani da namiji ba bayan kai, ba kuma zan auri kowa ba, zan cigaba da rayuwa da bakin aljanin da kowa ke zaton ya aureni" Ta mike tsaye tana goge idonta. "Na gode... Ahmad... Na gode!" Ta nufi kofa da sauri idonta yana zub da hawaye. Ya mike da sauri yana kiran sunanta amman bata kula shi ba, bata ma tsaya ta saurari abinda zai ce ba ta fita ta banko masa kofar ofis din. Ahmad ya koma ya zauna da damuwa ya dafe kansa zuciyarsa na tafasa, dama zai iya taimakonsa kamar yadda ta taimake shi da yayi, amman ba zai iya ba, ba zai taba hada son wata 'ya mace da ma'u a cikin ransa ba. Haka ya koma gida a ranar sukuku babu walwala har sai da ma'u ta fahimci yana cikin wani hali, bata matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tun tuni akwai matsala a ofis dinsa, don haka addu'a kawai take yiwa mijin nata. Duk yanda ta so ta faranta masa ta sanyashi farin ciki ta kasa, dole ta barshi shi daya cikin daki, don ta kula abinda yafi bukata kenan. Nana kam dakyar ta iya kai kanta gida, domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainahin sashinta ba jiri ya dauketa ta yanke jiki ta fadi kasa. A daidai lokacin Hajiya Batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya Batula ta fasa kara ta nufeta da gudu tana salati, ta kamota ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka karaso kowa a rude jin kiran da Hajiya Batulan take musu. Ganin halin da Nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma. Hajiya Batula cikin kuka take cewa "ku bani ruwa na yayyafa mata" Daya daga cikin matan ta kwasa da gudu, sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi. Hajiya Batula ta karba saboda tsabar gigicewa ma zubawa Nana tayi a jikinta gaba daya. Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya Batula tayi doguwar hamdala sannan ta kalli 'yan aikin tana cewa "ku taimaka min ku kamata mu kwantar da ita akan kujera" Suka ciccibci Nana aka kwantar da ita, ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake Abuja. Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali Hajiya Batula tace masa "Alhaji Nana bata da lafiya, yanzu ta fadi har da suma" Alhaji Nura Kwangila ya gigice yace "suma kuma, me ya sameta?" Ta kalli Nana dake kwance akan kujera tace "ban sani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi, amma da nayi mata magana sai tace babu komai" "Kin ga bar bayanin haka, zan yi wa likita waya yanzu ya zo, ni kuma zan biyo jirgi na taho yanzu. Ki kula da ita kafin na iso" Ya kashe wayar da damuwa, a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa Kano. Hajiya Batula ta isa kusa da Nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. "Sannu Nana meke damunki? Nana ta runtse ido hawaye ya zubo mata, bata son tunawa, amman ba zata taba mantawa ba, domin soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, ba zata iya rayuwa ba Ahmad ba. Ganin hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyar tata tace "shike nan ya isa daina kukan" Bayan min tuna goma sai ga likita ya iso gidan nasu, hadiman gidan suka yi masa jagora har cikin gidan da yake kowa ya san shi a gidan. Hajiya Batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin "Yauwa karaso likita ka duba min ita" Likitan ya isa da sauri ya sauke jakar DA yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala-kala. Cikin 'yan mintuna kadan ya kammala auna Nana. Yayi mata wasu 'yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da Hajiya Batula sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje-gwajen. Hankalin Hajiya Batula ya kara tashi sosai, ta dubi likitan tace "likita ka gaya min meke damun diyata?" Cikin kwantar da murya likitan yace "kwantar da hankalinki Hajiya, ba wani abu bane ba, ina dai so na samu sakamakon da nake bukata" Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti. A cikin mota tayiwa Alhaji Nura Kwangila bayanin sun wuce asibiti. A lokacin shi kuma yana
Chapter 29 · 0% Book details