Sashe 20
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin mamakin dalilin zuwansa cikin wannan dare. A kidime malam jibril yayi masa bayanin abin dake faruwa. Malam Sulaiman ya ce "ai samun mota cikin wannan daren shine aiki, amma bari" Ya shiga yayiwa umma magana ko akwai wani abu da zata iya yi a kai. Sanda malam Sulaiman ya sanar da umma abib dake faruwa tayi tsalle ta dire tace "babu inda zani, nima diyata ta haihu har kwana bakwai yau amma daga lami har 'ya'yanta babu wanda ya leko, don haka babu inda zani" Tun yana mata fadan har ya fara yi mata magiya da kawo mata hadisai wadanda suka sanyayar mata DA gwiwa ta nufi gidansu lami. Tana zuwa taga halin da Raliya ke ciki ta san lallai ta jigata, ta kwanta sharbe-sharbe ga kan da na yunkurowa yana komawa, ta kasa nishi, lami sai kuka take yi ita da amina. Umma ta kalli lami tace "kuna da koko ko kunu? Da sauri lami tace "akwai" Ta fice ta dauko umma ta amsa tayi addu'a fa tofa mata a ciki sannan tace a dago mata raliya zaune, suka kama raliyar dakyar suka zaunar da ita. Umma tace ta dafa kujera ta tokare kafafuwanta a kasa ta kafa mata wannan kunu cikin katon sha ta dinga sha har sai da shanye shi tas. Cikin ikon ALLAH sai ga karfi ya zowa raliya ta fara wani irin nishi da karfi, umma ta rike ta. Sai ga diya ta fado, Cikin ikon ALLAH kuma har da mahaifar baki daya. Lami ta fashe DA ihun murna, umma ta dalla mata harara "ke da zaki godewa ALLAH sai kuma ki kama guda? To sai ki kawo reza" Lami ta juya da gudu ya fara nemo reza da zare, umma ta amsa ta yanke ta kulle cibiyar bayan ta yanke. Raliya tayi zaune ta kasa motsawa saboda abu biyu ke yawo a ranta, murna da rabuwa da abun dake cikin cikinta da kuma takaicin abin kunyar da zai fara bibiyarta har karshen rayuwarta. Malam jibril yana tsaye a bakin kofar dakin da damuwa akan fuskarsa yana jiyo sautin kukan jaririyar ya zame ya zauna yana sallallami da damuwa, shikenan ta tabbata shege ya bayyana a gidansa, diyarsa ce ta haifa masa shege ya shiga uku. Umma dai tana gama abin da zata yi ya kalli lami tayi wuki-wuki da ido tace "to lami ga dai raliya ta sauka ta sami irin abinda kika dade kina gorintawa ahmad a kai, sai nace ALLAH ya raya amin" lami ta bude baki da bakin ciki amma bata da abin cewa da zai daidai da irin maganar DA umma ta fada mata har ta fice daga dakin. Lami ta kalli raliya dake zaune kamar ta shake ta don bakin ciki, ta kalli diyar wacce ke ta kuka tana wutsil-wutsil da kafafuwa, sai tayi tsaki ta juya ya fice daga dakin da sauri. Raliya ta bi yarinyar da kallo ta mika hannu ta dauketa ta kura mata ido, fatanta bai wuce ta gano da wa diyar take kama wanda zata ce shine ubanta, domin maneman nata na DA yawa. Amman iyakacin kallon da tayiwa yarinyar ta kasa gano da wanda tayi kama. Hawaye ya dinga fitowa daga idanunta soyayyar tana shigarta a hankali. Me ya sanya bata zauna a gidan ahmad ta haifi wannan yarinyar ba ko bayan hakan ne ta bar gidan? Da ta huta da gori da dukkan abibda zai biyo bayan rayuwar wannan yarinyar da ta haifa yanzu. Dakyar lami ta iya dora ruwan dumi domin ta kaiwa raliya bandaki sannan ta dauki jaririyar tayi mata wanka. Ba su sami kwanciya ba sai wajen karfe hudu na dare sannan suka kwanta. Kiran sallar farko raliya ta mike tsam ta dauko jakar kayanta ta fara zuzzuba dukkan abun da tasan nata ne, daman sun gama shiryawa da ruky cikin dare, sun gama shirya abin da zasu yi. Bayan gama kammala shiryawar ta juya ta kalli jaririyar DA take bacci, hawaye ya zubo mata taji kamar kada ta gudu ta bar diyar nan, amma ba zata iya cigaba da harka yadda take so ba matukar tana tare da wannan yarinyar, ta goge idonta da sauri ta dauki jakarta ta fice. Har gari ya waye rana ta fara fitowa lami bata leka dakin da Raliya take ba, daman amina ta raba daki da Raliya tuntuni. Can yarinya ta fara kuka daga cikin dakin, daga lami har amina babu wanda ya kula da kukan da take yi, domin suna tunanin mahaifiyarta na kusa da ita. Shi kam malam jibril dama tunda ya fita sallar asuba bai dawo gidan ba. Musa kuma tunda aka yi rikicin nan bai kuma dawowa gidan ba, sai ya tare a can dakin wani abokinsa don bai san abinda zai faru da shi ba idan suka ci karo da lami. Kukan ya ishe su, lami ta mike a fusace ta nufi dakin tana fadin "raliya wai uban me kike yi ne kika bar yarinyar nan tana kuka haka?" Ta daga labulen dakin a fusace, sai dai ya mamakinta sai taga dakin wayam babu kowa sai jaririyar dake ta tsala kuka. Ta shiga dakin da sauri ta fara bincike. "Raliya! Raliya!! Raliya!!!" Amma taji shiru babu ita balle alamunta. Ta fito da sauri ta kalli amina cikin ihu. "Ke duba min bandaki ko raliya ta shiga" Amina ta mike da sauri ta nufi bandakin ta fara dubawa, ta dawo da sauri domin taga mahaifiyar tata a rude take tace "lami bata nana" lami ta dafe kirji a kidime tana fadin "na shiga uku kar dai ace yarinyar nan ta gudu ta bar mana diyar nan? Ihun jaririyar ya cika mata kunne ta koma dakin da sauri ta dauko jaririyar ta rungume ta tana jijjiga ta DA fadin "ke maza duba mana gidan nan sosai har can gidan su dije ma ki gani ko tana can" Amina ta juya da sauri ta nufi hanyar fita. Lami ta cigaba jijjiga jaririyar hankalinta a tashe kamar ta zabga ihu ko ta ji sanyi a ranta. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Domin duk inda ake tunanin za a samu raliya an duba babu ita babu alamunta, dole lami tana ji tana gani ta wanke mamanta da magunguna ta fara baiwa jaririyar nan nono, domin ba zasu jure siyan madara ba, don malam jibril kokarin ganin ya siyi madarar amma ba zai iya jurewa ba yayi mitar tasa har ya gama. Lami kam kukan jini ne kawai bata yi ba, ko tsakar gida bata iya fitowa saboda kunya da nauyi, gashi yara da 'yan mata har shigowa gidan suke yi kallon 'yar da aka gudu aka bari bayan an haifeta. Umma kam ji take yi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don dadi. ALLAH bai barin hakkin wani akan wani, ita ke yiwa ahmad gori akan shi SHEGE ne sai ga SHEGIYA a gidansu. Sannan ita ce ta sanya raliya ta gudu da kanta, yau kuma ga gudun raliya ya zame mata matsala da tashin hankali a karo na biyu. Haka nan dama ALLAH yake ikonsa. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. BAYAN SHEKARU BIYAR Rayuwar ahmad da ma'u an samu cigaba da kuma karuwar zuri'a, domin cikin shekarun nan ma'u ta kara haifar yara biyu namiji da mace, an sami Hajiya Amina da kuma Malam Sulaiman, har wannan lokaci mijinta yana matukar kaunarta da nuna mata soyayya, 'ya'yansa kuwa sune abokan rayuwarsa tare suke cin abinci tare suke sallah hatta da su yake yi, domin yana ganin sune sabuwar zuri'arshi a duniya, bashi da kowa bayansu, don sun sha rigima da ma'u ma akan kwanukan da take yi yace WALLAHI bata isa tayi masa tsarin iyali ba, idan ma 'ya'ya dari zata haifa yana so. Abin ya sanya musu rikici, don tana ganin ba zata iya ba amman da ya gaya mata wata magana wata rana yana hawaye bayan haihuwar Hajiya ya sanya ta hakura ta sallama masa tana ta kuka ne sanda ta samu cikin malam ya zauna a gabanta ya kwantar da murya yace 'ma'u ba Zan sanya ku dole ki haihu ba, rayuwarki ce kina da damar yin yanda kike so, amman zan so ki tausaya min ki tuna ni bani da kowa da zan kalla da sunan dangina na jini bayan 'ya'yana. Da sune zan haifi zuri'a da za a iya kallo a kirata da DANGINA shin idan baki yarda kin haifa min 'ya'ya ba ta ina zan samu dangi? Haba ma'u ki tausaya min mana, kece kadai wadda zata iya bani abinda nake bukata, ki taimaka min ma'u" Jikin ma'u yayi sanyi ta daga kai ta kalli mijin nata wanda ke durkushe a gabanta yana zubar da hawaye, tausayinsa da sonsa ya dinga shigarta. Ahmad yana sonta yana kuma kaunar duk abinda take so, yana tattalinta, me ya sanya itama ba zata so abinda yake so ba? Tabbas ita ce me daukar cikin ta haihu, amma rainon abun da wahalarsa ne take ji. Ta kamo shi ta rungume a kirjinta tana shafar kanshi. Sai kawai ya fashe da kuka yana cigaba da magana "ki taimaka min ma'u... Ki taimaka min..." Gaba daya hankalinta ya tashi, cikin rawar murya take fadin "na daina mijina ba zan kara ba, zan yi maka dukkan abinda kake so, zan haifa maka 'ya'ya insha ALLAHU" Ya rungume ta a akan jikinsa wani dadi yana shigarsa, yana mata godiya, wannan ya kwantarwa da ma'u hankali suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin soyayya da nishadi. iskaKasancewar ya jima a gidan man da yake aiki, wato 'YAN LEMAN PETROLEUM na kurna aka sauya masa zuwa wani sabon gidan man DA maigidansu Alhaji Nura Kwangila ya gina a cikin G.R.A. duk DA gurin ya yiwa ahmad nisa sosai bai damu ba, domin Alhajin yayi masa karin albashi har yayi sabon mashin don haka bai da matsala wajen zuwa aiki da komowa gida. Yau an tashi da rade-radin kamfanin mai zasu yi yajin aiki cikin satin, don haka mai ya fara ja da baya, gidajen mai da yawa ya kasance a ciki, ciki kuwa har da na su ahmad, layi har kan titi sai hayaniya ake tayi. Daga can nesa