Sashe 16
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
faru?" Malam jibril ya gyara tsayuwa yana tunanin ta inda ya dace ya fara bayanin nasa. Can ya nisa yace "yaya ka san raliya ta dawo gida kwana hudu da suka wuce kuwa?" Malam sulaiman ya dan zabura yace "raliya kuma?" Yayi wata doguwar ajiyar zuciya ya kara da cewar "Masha ALLAH yaushe ta dawo kenan? "Yau kwananta shida" malam jibril ya bashi amsa yana in-ina. "Haba jibrilu amman ka kasa sanar da ni tun randa ta dawo din. Amman babu komai tunda ka sanar da ni yanzu, amman ko karo ban taba ci da ita ba tsawon wannan kwanakin da tayi din ba" Malam jibrilu ya ja doguwar ajiyar zuciya. "Yaya Ina dan fargabar yanda zan gaya maka zuwan nata ne, saboda abinda ke tare da ita, wato raliya dai ta dawo da ciki tsoho, kuma..." Malam Sulaiman ya zabura da rudani yace "ciki fa kace jibrilu, ciki dai juna biyu na haihuwa? "Ciki na haihuwa yaya, wannan ne ma dalilin da yasa na kasa sanar da kai har sai da na sami hujjar da zan gaya maka, don na san hankalinka zai matukar tashi idan ka ji cikin nata shege ne, amman da yake da ubansa shi yasa na sami karfin gwiwar iya tunkararka har na sanar da kai yanzu" Har lokacin bakin malam sulaiman yana bude da tsananin damuwa a fuskarsa cikin takaici yace "aure ka daura mata ban sani ba da ya sanya cikin nata ya zama mai uba ba shege ba jibrilu?" Yanda yake maganar ya sanya gaban malam jibril faduwa har yaji yana shakkar fada masa abinda yayi niyyar fada din. Sai da malam sulaiman ya kuma cewa dashi "kai fa nake sauraro jibrilu, kace min cikin nata yana da uba, ka gaya min waye uban nasa? Malam jibril ya gyara zama yace "eh ka san lokacin da ta bar gidan mijinta da aurensa a kanta bai saketa ba..." Yayi dan shiru yana kallon malam sulaiman domin ya ga yanda ya dauki maganar. Sai ya ga ya nutsu tsaf yana sauraronshi, don haka malam jibril din ya ci gaba da jawabinsa. "Ko ka manta hakan ne yaya?" "A'a ban manta ba, Ina sane da cewar raliya ta gudu daga gidan Ahmad ba tare da ya saketa ba. Ina jin har zuwa wannan lokacin ma akwai aurensa akanta. Amma duk ba wannan ba, yanzu ina son na ji yanda ta sami ciki halattacce ne jibrilu." Malam jibril ya gyara zama yana duban yayan nasa. "Eh kafin ta bar gidan shi Ahamd din da ciki a jikinta kuma shi Ahmad ma da kansa ya san da shi. To wai cikin kwanciya yayi sai wannan karon ya tashi, shi ne ta dawo gidan don a shaida ya haifar masa abinsa ta ba shi." Malam Sulaiman ya shiru yana sauraron malam jibrilu sai yaji kamar ya shakoshi don bakin ciki ya rufe shi da duka. Ya rasa dalilin da ya sanya kanin nashi ya maida kanshi kamar tababbe mara hankali idan yana sani zancen. Ya dai daure yace "bari na tambaye ka jibrilu, tsawon watanni nawa mace take yin idda idan mijinta ya sake ta? Da sauri malam jibrilu yace "wata uku ne yaya" Malam Sulaiman ya kada kai. "Ita kuma macen da ta gudu daga gidan mijinta tsawon shekara biyu ko uku ma wanne hukunci ne akanta kenan? Malam jibril yayi shiru yana juya tambayar sannan yace "WALLAHI ban san hukuncin dake kanta ba sai dai idan malamai sun yi jawabi" Malam Sulaiman yace "to idan haka ne kaga bai kamata kai tsaye ka danganta cikin dake jikin raliya da na ahmad ba, domin ba sakinta yayi ba balle tace kwanakin iddarta sun cika kuma tana tare da ciki ba" yayi shiru yana kada kai. "Amman dai bari nayi shiru na fara jin ta baki shi Ahmadun domin shine hakkin komai ke hannunsa ko nace wajensa. Amman idan ka shiga gidan ka gayawa raliya ta zauna cikin shiri kafin Ahmad din ya karaso" Malam Sulaiman ya mike tsaye yana duban dan uwan nasa "bari na shiga daga ciki sai an jima" ya juya ya shige cikin gidan ba tare DA yaji abinda dan uwan nasa zai kara fada masa ba. Malam jibril ya bishi da kallo gwiwarsa da jikinta gaba daya sun yi sanyi, sai ya mike a zabure kamar wanda aka tsikarawa allura ya nufi cikin gidan kai tsaye ko sallama babu. Ya fada gidan yayi wuri-wuri da ido bai ga kowa ba a tsakar gidan, sai ya jiyo muryarsu cikin daki, sai ya juya da sauri ya fada dakin kai tsaye. Suna zaune suna sake-sakensu na banza suka ganshi ya shigo dakan kamar an jefo shi. Gaba dayansu suka dago kai suka kalle cike da mamaki da fargaba. Lami ta far karfin halin yin magana "malam lafiya ma shigo babu KO sallama? Amina tayi tsayi gami da murguda baki tana fadin "ni WALLAHI tsoro ma ya bani" "Tsoron ubanki ja'ira" cikin fushi malam jibril ya katse amina. Ya kai mata duka ta kauce da sauri ta boye a bayan lami tana haki. Malam jibril ya ci gaba DA bala'i. "Banda iskanci da raini ace na shigo ana mini tsaki har da murguda baki, kin koyawa yara rashin tarbiyya, dubeki suna jera kafada dake babu kunya ko takaici a zuciyarki sam" Lami ta daga masa hannu da sauri cikin bacin rai. "Don ALLAH malam ka rabu da ni haka naji da abindake damuna. Don tayi maka tsaki ai ba zai zama laifi ba tubda kai ma baka cika hukuncin UBANGIJI ba na yin sallama da zaka shigo mana, ni WALLAHI tayi mini daidai." "Ai dole tayi miki daidai tunda halin tsiya ya cikata, amman ta cigaba da hi watarana zan karyata gaba daya sai naga abinda za kiyi" Ya mai da dubansa ga raliya dake kallonsa ranta a bace. "Ke kuma gurinki na zo, ina son ki kara gaya min gaskiyar abin dake cikinki na waye don ALLAH idan kika mai dani karamin mutum sai ranki ya baci fiye da yanda kike tsammani kin ji na gaya miki ko? Raliya ta zunburo baki gaba ranta a bace tace "ni fa gaskiya ba fada, cikinsa ne idan kuma ya musa na yarda mu sanya Al-Qur'ani ayi rantsuwa, wanda yayi wa wani karya a tsakaninmu ALLAH ya kona shi tun a duniya" Malam jibril ya yi shiru yana kada kai alamar ya yarda da abinda tace. To shikenan sai ki zauna cikin shiri don yanzu Ahmadun zai shigo" Lami tayi kwafa "WALLAHI gwara ya shigo ayita ta kare. Don ina ji ina gani ba zan yarda anuna bambanci tsakanin cikin dake jikin diyata da cikin dake jikin diyarsu ba. Domin shi ma da ne kuma na halak. Dukkan abibda aka yi mata sai an yiwa raliya an biyata dukkan ciyarwar da tayi wa kanta da cikinsa, duk sai an biya ta komai WALLAHI" Malam jibril bai kara kulata ba ya juya ya fice daga dakin da sauri ya barsu a nan suna ta surutunsu. Amina sai cika baki take yi tana fadin "banza a banza, ma'un ma ga kuma irin burgar da zata kuma yi mana, don har wani takama da iya yi take yi min wai ita gata mai aure da ciki. Ta manta mijin yayata ta aura kuma saura. WALLAHI banda lami ta hana ni da sai na ci ubanta da cikin nata baki daya, amman daga yau girman kai ya kare, domin mai guri yazo mai tabarma kuma ya nade" Lami ta amsa da fadin "lallai kam haka wannan batun yake domin dole raliya ta koma dakinta ko ana so ko ba a so." Ta dawo da kallonta kan raliya dake kallonsu tace "kina jina ko. Idan muka isa gurinsu ki dage akan kina son komawa dakinki domin kuwa daman kayanki ne dole ta bar miki gidanki, dole ta bar miki mijinki, tunda daman auren cin amana ne aka yi. Munafikan banza Munafikan wofi" Raliya tana kallonsu kawai tana ta addu'a acikin zuviyarta akan ALLAH ya sanya Ahmad ya amince har ya amshi cikin nata ma kafin aje ga amsar gidan ko mijin nata. Wayarta ta fara ringing da sauri ta kalli jakarta dake gefenta, sai ta zura hannunta ta daukota ta mike tayi kofar fita daga dakin tana danna wayar. Gaba dayansu suka bita da kallo ganin yanda ta fice bata kula da nauyin jikinta ba. "Hello Ruky Baby ya aka yi ne?" Daga can bangaren ruky ta fashe da dariya tana fadin "baby kin makale kin ki kiranmu ko? Wai me ake ciki ne akan dan kadafin da ya makale miki ne? Raliya ta makale jikin bandaki tana hango gidan taga babu kowa sai tace "shegiya sai yau kike nemana? To yau dai za a gara shirin yakin ba a yi komai ba, amman ni fa na dan fara shakka kamar ba zai amshi cikin nan ba" "Ke banza kada ki karaya ko ki bata mana shiri, boka ya tabbatar min da lallai sai ya amshi cikin nan, idan kika fara karaya kuma yaya za ai ya yarda ya amsa? Raliya tayi ajiyar zuciya tace "ba ki ji yanda ake min tambayoyi ba kamar ina gaban mala'ikan kabari, masu tambayar tashin hankali, ke duk na tsorata WALLAHI ruky da na sani na taho da ke ma" "Ki taho da ni? Ai da shirin ya ruguje domin suna ganinmu tare zasu yarda ribar bariki kika ci har kika samu ciki. Ke dai kiyi yanda boka ce, ki dora a layar akan cikinki, kuma kuma ki kuskure bakinki DA ruwan rubutun nan dole kowa ya yarda. Fatana dai da zarar kin haife masa cikin, ki ajiye ki dawo harka, kar ki yarda su kara kulla ki cikin gidan nan mai kama da akurkin kaji" Raliya tace "karki damu kawata, bariki ai ita ce gatanmu, cinmu kuma shanmu. Bari na koma sai na kira ki da karin bayani akan yanda muka yi da su" T kashe wayar tana murmushi, amman lokaci guda murmushin dake fuskarta ya dauke saboda ganin yayanta Musa da tayi ya fito daga bandakin yana mata wani irin kallo. Babu KO tantama yaji dukkan hirar da suke tattaunawa da kawarta cikin waya. "Sakarya kin yi asara raliya, amman da sannu zaki gane shayi ma ruwa ne WALLAHI" ya kada kai ya fice. Ta