← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amsa tana kokarin mikewa tsaye, ta nufi randa ta debo mata ruwa mai sanyi ta kawo mata a kofi ta ajiye a gabanta. Amma Ma'u ta kasa taba komai saboda takaicin cikin da ta gani a jikin raliya. Umma ta fito daga cikin daki ta kalleta cikin mamaki ganin bata ci komai ba. "Au wai har yanzu baki ci komai ba daga cikin abin dake gaban naki? Ko ruwan baki sha ba" Tayi ajiyar zuciya tana fadin "umma damuwa ce ta cika ni da takaici. Ko baki hadu da Raliya bane tunda ta dawo gidan? Umma taja kujera 'yar tsuguno ta zauna tana tabe baki. "Idan na hadu da ita din ma sai me? Mene ne abin mamaki ko damuwa don raliya tayi cikin shege? Uwarta ce da kanta ta tura ta bariki tace da auren ahmad matsiyaci gwara yawon karuwanci. To ai ga shi nan ta kawo mata lada ko nace tukuici, sai mu ga kuma wanda zata kara yiwa gori cewar shi shege ne" Ma'u ta kada kai cikin damuwa da jinjinawa. "ALLAH ya kyauta amman WALLAHI raliya ta cuce mu ta bata mana sunan zuri'a, yanzu ace shege zata haifa mana" "Zata haifawa kanta dai" umma ta amsa. "Kin ga don ALLAH ki daina yi min maganar mutanen can ki ci abincinki kawai. Shin kin samu ganin likitan ne?" Ma'u ta kada kai "na samu ganinsa har ya dubani da kansa, kuma yace komai lafiya kalau umma" Ran umma yayi sanyi tace "Masha ALLAH haka nake son ji. Maza ki gama cin abincin ki shiga ki watsa ruwa ko kya ji dadin jikin naki" Ita dai ma'u kai kawai ta daga, amman hankalinta sam baya tare da ita, domin 'yan magana sun ce _hannunka baya rubewa ka yanke ka zubar dashi_ duk lalacewar raliya jininta ce, kuma KO taki ko taso dole a kirawo raliya 'yar uwarta. Haka nan ma'u ta yini a gidan sololo babu kuzari ko kadan a tare da ita. *** Malam jibril ya shigo gidan fakan-fakan ransa a bace, domin bai kaunar ko lekowa gidan idan ba ya zama dole ba, don bai son ganin raliya dake da cikin shege a jikinta wanda yake jin kamar ya harbata ya kashe abinda yake cikin. Yana son gayawa dan uwansa amman bai san yanda zai dauki abin ba, don haka ya ja bakinsa yayi shiru, amman bakin ciki yana cin ransa da zuciyarsa. Ya debi ruwa ya zuba a cikin buta ya nufi bandaki DA sauri. Lami ta fito daga cikin daki da sauri ta fara kwalla masa kira. "Malam! Malam!!" Bai ko kalleta ba ya shige cikin bandaki abinsa. Lami ta tsaya turus, ta rike kugu tana masifa. "Amma wannan wulakanci ne ina maka magana ka min banza ka shige bandaki. To zaka fito ka same ni ina tsaye ina jiranka" ta cigaba DA tsayuwa tana ta faman mita. Raliya ta fito daga cikin daki ta sami guri ta zauna ita ma. Malam jibril ya fito daga cikin bandaki ya sami guri ya durkusa ya fara alwala. Lami tayi kansa DA sauri. "Malam wai ko cutar rashin ji ce ta fara shigar ka ban sani ba" Ya daga kai a fusace "ALLAH ya kiyaye, sai dai ki ga wannan bala'in a kanki ba dai ni ba" "Ni ma din ba zata same ni ba aniyarka ta bika, ashe kana jina kayi min banza. Naga ka sauya hali da lokacin shigowa gidan nan tunda yarinyar nan ta dawo, kaki zama kaji damuwarta sai fushi da kumburi kake yi' Malam ya kuma fusata ya dago kai ya kalli lami. "Damuwar me zan ji bayan wacce manne a jikinta? Ai ko me ya same fa kece kika sai mata da kudinki, sai ta haifa miki shegen ki raine shi, ba haka dama kike bukata ba? Lami ta daga masa hannu idanunta cike da masifa. "Tsaya-tsaya malam ka daina kiran cikin diyata shege, domin wannan ciki ba shege bane WALLAHI da ubansa' Malam jibril ya mike tsaye da sauri ya fasa alwalar yana fadin "au ko kin daura mata aure ne ban sani ba, wato tayi aure kan aure kenan, laifi biyu akanta" "Babu batun aure kan aure, auren nan dai guda daya shine akanta har yanzu na ahmad, kuma ciki nasa ne ya san da haka shi..." Malam jibril ya fashe da dariya yana kallon lami wacce ta fara kuluwa da irin dariyar da yake yi mata. Yace "WALLAHI na yarda lami baki da hankali. Yarinyar da bata tare da mijin nata tsawon shekaru ta tafi yawonta amman ta samo cikin shege kice nasa ne. Tana yayi mata cikin ta iska ko kuma ta wayar salular zamani? "Ko ma meye cikinsa ne idan kuma baka yarda ba sai kaje ka yi tambaya akan haka. Tunda ta bar gidansa da ciki ta fita wanda ya kwanta mata sai a wadannan watannin ya tashi. Kuma shi kansa ya san tana dauke da cikin, kuma kowa ya san ciki yana kwanciya ko a cikin addininmu da gurin likitocin zamani, za a iya sakin mace bayan shekaru ta haihu in dai ba wani mijin ta aura ba idan cikin ya kwanta, balle ita da bai saketa ba, bacin rai ne ya sanyata guduwa kuma yanzu ta dawo masa da rabonsa, don haka dole ya amsa, idan kai ba zaka iya kwatar mata 'yanci ba ni zan yi. Duk kotun dake duniyar nan na shirya shigarta domin kwatarwa diyata hakkinta" Ya tsaya yana kallonta kyar! Yanda ta dage take zuba bayani yayi kama da na masu hankali amman kuma yana da tantama. Tabbas mace kan yi shekaru da ciki kuma ta haihu daga baya. Indai da gaske raliya da ciki ta gudu kuma Ahmad ya zan da haka to babu makawa wannan cikin nasa ne. Ya dire butar dake rike a hannunsa ya karasa kusa da Raliya dake zaune tana kallonsu yace "ke raliya ki sanar dani gaskiya, shin da gaske ne kin tafi da ciki a jikinki daga gidan ahmad ko karya ce kika shirya kawai? Ta karkace baki. "WALLAHI da gaske ne baba, wannan cikin na Ahmad ne, domin ya san DA shi tun kafin na tafi, ni nayi zaton ya zube ne da na ga ya daina girma, sai kuma daga baya cikin watannin nan naga yana tashi. Idan kuma shi ahmad din ya musa muje asibiti a gwada a gani za a ga jininsa ne a jikina" Malam jibril yayi shiru hankalinsa ya dan soma kwanciya. Idan haka ne lallai ya sami mafita, ya tsira daga abin kunyar da yake tunanin ya shiga a baya. Ya kada kansa. "Shi ke nan bari na je masallaci na dawo sai mu yi maganar da yaya. Ina zuwa" Ya durkusa ya karasa alwalarsa ya fice daga cikin gidan. Daidai lokacin da yake fita sai kuma Musa ya shigo ya gansu a tsaye cirko-cirko, yayi tsaki ya dauki buta ya nufi bandaki domin bai son kallon raliya shi ma. Lami ta doka masa tsawa "uban wa kake wa tsaki da wannan hararan iye?" Tayi kansa kamar zata rufe shi da duka. Ya dan dakata yace "ni fa ba da ke nake ba, shin baki bakin cikin abinda yarinyar nan ta aikata. Banza zata batawa mutane suna. Koda yake hakkin ahmad ne..." "Hakkin ahmad ko kuma rabon ahmad ne? To idan baka da labari bari na gaya maka, wannan cikin dake jikin raliya na ahmad" ta nuna cikin DA hannunta. Raliya ta murguda baki ta tafa hannu. "Gwara dai ki sanar da shi ko ya sama min lafiya" Musa yayi jum. Da mamaki sannan ya daure yace "cikin ahmad kuma kamar yaya? "Ko ma yaya ne zaka ji ai, amman wannan cikin nashi ne, kwanciya yayi sai yanzu kuma ALLAH ya tayar dashi, dole ya amshi kayansa. Musa ya waro ido cikin kidimewa yace "lami haka ta tsara miki kuma? To WALLAHI karya take yi, wannan ba cikin Ahmad ba ne, kada ta sanya ku cikin karyarta da shashancinta" "Sai ka hana cikin ya zama nashi. Kai tsaya na gaya maka, ko kotu zamu je WALLAHI sai ya amshi wannan cikin domin na kula kai ka fi kaunar shi da mu tunda ka taso, to ko ubanka daya da shi a wannan karon kayi karya ka hana shi ansar cikin DA ya san nashi ne" Ta kalli raliya "tashi mu shiga daki don idan na biyewa wannan yaron sai ya sanya zuciyata ta buga farat daya na mutu" Musa ya bi su da sauri. "Lami ki tsaya don ALLAH ki saurare ni, kada ku yi abinda zaku sanya mu shiga uku" Lami ta waigo a fusace. "Idan baka ja bakinka kayi shiru ba WALLAHI zan tsine maka, zan yi maka baki duniya ta juya maka baya baki daya na dak gaya maka" Ya tsaya turus da damuwa yana kallonta. Jikinsa yayi sanyi sabodajin abibda ta fada. Ta ci gaba da bala'i. "Idan ma na kara jin bakinka a cikin wannan maganar sai na saba maka WALLAHI. Wuce ciki mu je raliya kin ji ko" Raliya ta shige ranta yayi fes domin abinda ta tsara ya tabbata. Babu kuma wanda ya isa ya karyata ta. *** Su ma'u suna can basu san wainar da ake toyawa ba, sannan umma ta ki bata hadin kai akan su jajanta abin, sai sabgoginta take yi. Ma'u ta kagu mijinta ya zo ya dauketa ko sa sami damar tattauna matsalar raliyan da shi. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Malam Sulaiman ya dawo daga sallar magriba ya nufi gida da casbaha a hannunsa yana lazimi, ya jiyo kiran dan uwansa daga bayansa yana fadin "Yaya! Yaya!!" Malam Sulaiman ya tsaya cak gami da juyowa ya kalleshi har ya karaso inda yake ya mika masa hannu duka gaisa. Malam Sulaiman ne ya fara magana "ina ka shiga ne jibril kwana biyu bana ganin ka? Malam jibril ya shafa keya. "WALLAHI yaya ina can gurin 'yan buge-bugena, daman ina son muyi wata muhimmiyar magana ne da kai" Malam sulaman yace "to mu karasa wajen dakalin can sai mu zauna" suka nufi dakalin dake kofar gidan suka zauna dukkansu. Malam Sulaiman ya kalli malam jibril yacr masa "ina jinka jibrilu me ya
Chapter 15 · 0% Book details