← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 40

Sashe 17

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lafe jikin bango cikinta na hautsinawa tana zare idanuwa, ta shiga uku. _Amma idan ya san wata ai bai san wata ba_ ta raya hakan a cikin ranta. Ta nufi daki da sauri kamar mahaukaciya. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. A can gidan malam Sulaiman ma'u ce ke zaune akan tabarma tana cin tuwonta suna hira da ummanta dake gefe. "Umma baki kula baba ya shigo cikin damuwa bane? Ko hirar da ya saba yi da ni yau bai yi ba, dakyar ma ya iya amsa gaisuwata ya shige dakinsa" Umma tace "Na gani mana, wata kila sai yau ya samu labarin abinda raliya ta zo DA shi, kin san daman cikin maganarta yake yi" Sani days fito daga bandaki ya kalle su da mamaki yace "ciki kima umma? Raliya ce ta dawo dauke da ciki? Suka mai da kallonsu kansa gaba daya, umman tace "wai duk ba ku san meke faruwa ba ko? To ciki ta dawo DA shi tsoho kuma..." Sani ya dawo kusa da su ya zauna akan kujera yana salati da sallallami. A hankali 'yan uwan suka cigaba da shigowa kamar yadda aka sanar da su su zo. Aka ci gaba da tattauna matsalar kowa na cikin damuwa. Auwal ya kuta cikin fushi yace "shegiya ai hakkin ahmad ba zai barta taji dadin rayuwarta ba" daidai lokacin ahmad ya shigo kamar an wurgoshi, suka mai da kallonsu kanshi gaba dayansu. Ya iso wajensu yana fadin "umma ni fa yunwa nake ji" ya sami guri ya zauna. Auwal ya kalle shi yace "kai Ahmad sai kace wanda ya kwana da yunwa babu KO gaisuwa ka fara tambayar abinci? Ahamd yayi murmushin yana fadin "tuba nake babban yaya, bari na fara ya kan uwata. Umma ina yini? Umma ta amsa tana yake sannan ta mike tana fadin "ka rabu da su, sai ka koshi zaka gai da kowa. Suka yi dariya gaba dayansu. Duk maganar da ahmad yake yi idonsa da hankalinsa yana kan matarsa ma'u wacce ranta ke bace har lokacin, domin tafi kowa damuwa da abinda ya sami raliya, ko don ita macece ita kadai ta san ciwon mace 'yar uwarta. Ahmad ya kura mata ido yana son yi mata magana amman yana jin nauyi har umma ta iso DA tuwo ta ajiye a gabansa da ruwa a kofi da kwano daban tace "miko hannunka ka wanke a nan" ya kalli kwanon yayi murmushi ya mika hannu kan kwanon ta tsiyaya masa ruwan ya wanke hannunsa. Sani yayi murmushi yace "gaskiya umma mun gaji da wannan wariyar launin fatar, duk gurin nan don ALLAH wa ta zubawa ruwa ya wanke hannu? Suka kara fashewa da dariya gaba dayansu. Auwal cikin dariya yace "babu sai dan gatan umma" Umma tayi murmushi cike da jin dadi, domin haduwar yaran haka yana sanyata cikin jin dadi. Bata ce komai ba ta juya suka cigaba DA shakiyancinsu, ma'u tana dan murmushi kawai ba tare da tace komai ba. Sai DA Ahmad ya kai loma guda bakinsa sannan yace "wai ita waccan uwar biyun meke damunta ne na ga tayi shiru sai yake kawai take yi? Umma dake kokarin zama tace "abinda bai shafeta bane take kokarin dorawa kanta har yaje ya haifar mata da wata cutar ta jawa mutane tashin hankali" Auwal yace "haba umma ai kuwa abinda ya shafi raliya ya shafeta, dole ta shiga damuwa" Ahmad ya dauko loma guda zai kai bakinsa yana jin an ambaci sunan raliya ya dakata, ko sunanta bai fatan jin an ambata a rayuwarsa balle zancenta. Wani irin bacin rai da takaici ya saukar masa ya kasa sanya lomar a bakinsa ya maidata cikin kwanon. Ma'un ce ta kula da hakan, domin su duk hankalinsu yana kan maganar da auwal din keyi. Umma tace "damuwar me zata yi? Dukkan macen da ta bar gidan ubanta ta tafi yawon bariki don tayi cikin shege meye abin mamaki, ko abin daga hankali? To sai tayi domin abin bakin ciki ba zai a kare a gidan kanin ubanku ba har abada in dai ba su gyara halinsu ba" Ahmad yaji wani irin gingirin! Ya cika da tsananin mamaki da kuma takaici. Idan ya fahimci abinda suke tattaunawa akan raliya, to suna batun raliya ta dawo GIDAN da cikin shege. Nan take jikinsa ya dauki rawa, ransa yayi tsananin baci, domin idan har bai yi ciwon hauka ko na mantuwa ba ya san bai saki raliya ba, don babanshi bai bashi wannan izinin ba, hakan n a nufin da aurenshi tayi cikin shege kenan. Sani ya kalle shi ya kula ya daina cin abincin yace "Ahmad ba dai har ka koshi ba? Kai da kake kukan yunwa" Ummata kalle shi da sauri tace "wai kai ma ja sanya abin a ranka har zai hanaka cin abinci? Fitowar malam Sulaiman daga cikin daki ne ya katse musu hirar da suke yi, gaba daya yaran suka kama kallonshi. Salisu ne ya fara fadin "au dama baba yana cikin daki bamu sani ba umma" Ta amsa da "eh yana yin dan wani abu ne, amman na san zai fito ya ganku bayan ya kammala" Suka fara kokarin gaishe shi yana amsawa, hannunsa yana rike da tabarma katuwa. Ahmad ne ya mike da sauri ya karbi tabarmar dake hannunsa cikin girmamawa ya shimfida. Malam Sulaiman ya zauna yana kallonsu daya bayan daya. Kowanne daga cikinsu ya sha jinin jikinsa domin ganin halin da mahaifin nasu yake ciki, saboda basu saba ganinsa a haka ba, domin duk sanda ya shigo ya gansu a haka dadi yake ji, shi ma sai ya shiga cikinsu ai ta hirar da shi, amman yau sun ga sabanin haka, yana gidan ma sun shigo kwata-kwata bai fito ba, basu ma san yana ciki ba sai yanzu. Bayan an gama gaisawa sai yayi shiru yana kallonsu, hakan ya kara sanyayar musu da jiki gaba dayansu. Daga can malam Sulaiman yaja numfashi ya dubi Salisu yace "kai Salisu jeka wajen su jibrilu kace yazo shi da maidakinsa da kuma raliya" Salisu ya mike DA sauri domin cika umarnin mahaifin nasu. Ahmad ya yunkura da nufin ya tashi, don baya son ya kara koda kallon fuskar raliyan, amman malam Sulaiman din ya katse shi ta hanyar yin magana. "Ahmad ina kuma zaka je? Ai wannan zaman naka ne koma ka zauna" Ahamd ya koma ya zauna yana mamakin jin abinda malam Sulaiman rada, amman yayi zaton ko akan maganarsa da ita ne malam din zai yi masa umarnin akan ya sake ta ne ya huta. Umma juws bata so hakan ba, don ba ta ga dalilin da zai sanya ya gayyato su cikin gidansu ba, gwara ma ya tafi can gidan ayi maganar tunda su ta shafa. Kowa yayi shiru ganin yanda mahaifin nasu yayi shiru. Bayan shudewar wasu mintuna kalilan Salisu ya dawo da sauri yazo gaban mahaifin nasa ya risina yace "ga su nan zuwa" Malam Sulaiman yace "shikenan kai ma samu guri ka zauna" ba musu ya koma wajen da ya tashi ya zauna, aka sake yin shiru ana sauraron abinda malam din zai ce, amma sai suka ji shi ma yayi shiru bai ce da kowa komai ba. Can malam jibril ya shigo lami da Raliya na bin bayansa har da amina. Ma'u da sauran 'yan uwanta suka bi raliya da kallo wacce ta zunduma katon hijabi kamar gaske. Ahmad ya kasa ko dago kai ya kalleta saboda bakin ciki da takaici. Ko jin muryarta baya son ji balle kamshinta mai tayar masa da zuciya. Ya kara yin kasa da kansa bai son ko dago idonsa har suka sami guri suka zauna. Abin mamaki sai ga raliya na kallon ahmad da yake akwai hasken wutar nepa tana son ta gano yanda ya koma, shin ya cigaba ko ya koma baya? Ta kasa dauke idonta daga kansa. Malam Sulaiman ya kalle su saya bayan daya bayan sun zazzauna yayi gyaran murya ya kurawa malam jibril ido ya fara magana. "Yauwa kamar yadda ya faru dazu jibril ya kira ni akan maganar ahmad sa raliya wanda nayi tunanin mun wuceta a baya, amman yau ya dawo da wata sabuwar magana wacce ya dace ku ji ta daga bakinsa ba nawa bakin ba, domin masu salon magana sun ce waka a bakin mai ita tafi dadi" Malam jibril yayi wuki-wuki yana kallon mutanen wajen, shi kana yana da shakku akan abinda zai fada din balle su, yana jin kamar ana iza shi lallai sai ya fada. Ya kalle su yace "eh to, akan maganar cikin dake jikin raliya ne, daman wai tace cikin na ahmad ne..." Gaba daya suka kalle shi da mamakin jin abinda yace. Umma kam kai tsaye ta mike tana fadin "kan uban can! Wannan wacce irin magana ce maras kan gado haka?" DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Umma kam kai tsaye ta mike tana fadin "kan uban can! Wannan wacce irin magana ce maras kan gado haka?" Lami tayi caraf ta amsa "daman ba zata yi kan gado a gurinki ba dije, amma mu a gurinmu tafi maganar shahararren malami tasiri, ki karkade kunnenki da kyau ki ji..." "Kai! Meye haka ne, wannan wanne irin hauka ne, kune kuke yin magana ko mune, waye ya sanya bakinku a cikin wannan maganar?" Malam Sulaiman ya doka musu tsawa ta hanyar fadin wadannan maganganu. Shi kuwa ahmad baki ya saki yana kallon ikon ALLAH, sai yake ganin abin kamar shirin fin din nan. Ma'u kam mutuwar zaune tayi, zuciyarta har ta fara raya mata miyagun abubuwa. Kar dai mijin nata zagayawa yake yi gurin raliya suna watsewarsu ba tare da ta sani ba? Koda yake ai ance bai sake ta ba, matarsa ce kenan, in dai haka ne kuwa lallai yaci amanarta. Wani tukuki ya taso ya tsaya mata a wuyanta mai daci da ciwo. Ta dinga kallon mijin nata wanda shi kuma yake kallon raliya da mamaki da takaici. Gaba daya gurin aka yi tsit, kamar mutuwa ce ta gifta. Amman fuskar kowa ta nuna abindake zuciyarsa a fili. Malam Sulaiman ne yaci gaba da
Chapter 17 · 0% Book details