Sashe 31
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauri yana kallon screen din wayar. Lambar Alahji Nura Kwangila ya gani, gabansa ya fadi amman dai dole ya daga. Yana shirin gaisar da Alhaji Nura Kwangila din ya katse shi da cewa "kana ofis ne? Da hanzari Ahmad yace "Eh ina ofis Alhaji" Alhaji Nura Kwangila yace "OK to ga ni nan zuwa" Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake yi kamar ya gudu kada ya bari Alhaji Nura Kwangila ya zo ya tarar da shi, amman babu halin yin hakan, dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alhaji Nura Kwangila ya turo kofa ya shigo, Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar, saboda wani bugu da yaji kirjin nasa yayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana yiwa Alhaji Nura Kwangila sannu da zuwa. Alhaji Nura Kwangila ya dube shi yana murmushin yake yace "zauna Ahmad ina son yin magana da kai ne, kuma magana ce mai matukar muhimmanci a gare mu" Ahmad ya koma ya zauna cikin sanyin jiki, gabansa na dukan dari-dari. Alhaji Nura Kwangila ya janyo kujera dake fuskantar wacce Ahmad yake kai a zaune ya zauna ya tsare Ahmad da ido yana fadin "ba sai naji komai daga bakinka ba, na san Nana bata yin karya ko yaudara, abin da nake fata daga gare ka kawai shine ka amince Ahmad, bani da kudi ko ikon da zan iya siyan soyayya, domin da zan iya DA tun tuni na siyowa wani soyayyar Nana na aurar da ita. Tunda Nana ta taso ta ki jinin kula saurayi har zuwa girmanta, hakan ya jagoranci tunaninnu da kuma fadin wasu nalamai cewar wai bakin aljani ne ya aure ta, yanzu kuma sai ga shi ALLAH ya kawo mana maganin abun rana daya, Nana ta furta da bakinta cewa tana sonka Ahmad. Ahmad kayi duba da kyau ga wannan lamari. Nana yarinya ce mai kyau da tsari, kamar Nana ace ta tunkari namiji tace masa tana sonshi ka san ba karamin abu bane, ka taimake ni Ahmad ka auri Nana don ALLAH!" Ahmad yana kasa tunda Alhaji Nura Kwangila ya fara magana, da akwai mutumin da zai yiwa wani abu ko ranshi baya so to bai wuce Alhaji Nura Kwangila ba, amman ba zai iya yiwa ma'unshi kishiya ba, don yiwa ma'u kishiya kamar yiwa umanshi ne. Mutanen da suka raineshi suka bashi mace yaya zai iya yi musu haka? Ba shi da amsar da zai iya bai wa Alhaji Nura Kwangila, don haka ya dukar da kansa kawai. Alhaji Nura Kwangila ya zuba masa ido da mamaki sannan yace "Ahmad ko akwai wani da Nana take yi wanda ranka bai bukata? Ko kuma tana da wata illa ne ka gaya min, ban yi zaton wani namiji zai ki diyata ba a wannan lokacin" Ahmad ya girgiza kai yana fadin "ko daya babuvwani abun ki da na gano a wajen Nana amman..." Sai kuma yayi shiru ya rasa ma me zai ce. "Lallai Ahmad ka nuna min kai namijin duniya ne, hakan kuma ya sanya na kara yarda Nana tayi zabi nagari, don nayi imanin wani zai so Nana ko don arzikinta ko kyanta ko nasabarta, amman kai ko daya bai burge ka ba daga cikin wadannan abubuwa." Ahmad ya kada kai "tunda nake ban taba sanya kwadayin abun kowa cikin raina ba, na wadata da abun da nake samu, amman kayi hakuri Alhaji ina cikin halin DA ba zan iya aurar wata ba" Alhaji Nura Kwangila ya sake kallon Ahmad da tsananin mamakin irin karfin halinsa, amman hakan kara burge shi yake da kuma nuna shine mijin da ya dace ga diyarshi Nana. Yanzu cikin kwantar da murya Alhaji Nura Kwangila ya cigaba DA magana. "Yanzu kam alfarma bake nema ka dubi halin da Nana take ciki, bani da kowacce diya ko daya sai ita, zan iya rasa ta saboda sonka, ka ceci rai Ahmad, ka ceci rayuwarta daga cikin bakin cikin dake damunta" Jikin Ahmad yayi sanyi lallai ya kamata yayi wani abu a kai, amman kuma ba zai iya yi kai tsaye ba don haka yace "Alhaji ka bani dan wani lokaci zan yi shawara tukunna" Ran Alhaji Nura Kwangila ya dan yi sanyi, ko babu komai ya samu magana mai dadi, amma cikin ransa mamaki da tu'ajabi ne ke cikashi yau kuma haka ALLAH ya kaddara a kansa kamar shi ya buge da rokon wani abu da bai da iko akansa, bayan shi da kullum ake roko. Wannan kadan kenan daga ikon ALLAH. Alhaji Nura Kwangila ya girgiza kai yana fadin "hakan ma yayi, amman ba zan ba ka dogon lokaci ba, gobe kamar wannan lokacin zan dawo naji shawarar da ka yanke. Na gode." Alhaji Nura Kwangila ya juya ya fice. Ahmad ya bishi da kallo da fargaba da tsoron abin da zai biyo baya. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Yau kam ransa a sake ya isa gida, halin da ya ga ma'u ya kara sanya ransa dadi, ita da 'ya'yanta suna cikin kyakkyawar shiga gwanin sha'awa. Ma'u ta mike ta taro shi da jin dadin yanda ta gan shi cikin farin ciki, ya mannata a kirjinshi yana sumbatarta suna dariya. Tayi masa dukkan abun DA ta saba yi masa suka wuce daki. Yau suna cikin farin ciki, gurin cin abinci ne take bashi labarin zuwan Amina gidan da yake tayi aure shekaru hudu da suka wuce, ALLAH ya hada da wani dan kasuwa a kantin kwari da yayi mata karyar shima mai kudi ne, yana da katon gida da mota, aka yi aure sai gashi ta tare a daki falle biyu a gidan, haka nan ta tarar zaman da zata yi ita da kishiya ne da kuma tarin 'ya'ya guda shida tayi kuka da bakin ciki amman bata da zabi bayan zaman auren. Malam Sulaiman shi yayi komai na auren nata tare aka hadasu da Musa wanda yanzu yake zaune a gidan Ahmad da ya bashi aro saboda yawon haya ya ishesu, kuma tunda taje gidan gidan mijin ALLAH ya jarrabeta da haihuwa ga babu, don aikin karya yayi, irin mutanen nan ne 'yan kayi-nayi, masu tsayawa a bakin hanya wadanda suke tsayawa idan mutum zai yi siyayya su nuna maka shago, wata ran ma sai aje a wuni ba a samo komai ba, ga iyayenta suma babu ta ko ina, su abarsu suji da hidimar diyar dake gabansu wacce suke kiranta da 'YAR RALIYA don na a yi mata radin suna ba balle ragon suna ko wani abu ba. Wannan kadai ya zamewa lami ishara. Sai da ya kai loma bakinsa sannan ya kalleta yace "ina jinki ma'u yaya tazo nan gidan kuma ita da tace har abada babu ita babu mu?" Ma'u tayi murmushi tace "bari kai dai yaya, yunwa da bala'i ne suka isheta taje can gidansu babu shine tayo nan tana zubar da hawaye DA fadin na taimaka mata bayan ni babu mai bata cikin dangi, tasan tayi abubuwa marasa kyau ita da mahaifiyarta garemu, amman hannunka bai rubewa ka yanke ka yar, don kwanansu biyu babu abinci, sauran 'yan hayar gidan daman basa shiri sam da ita kishiyar sun hade mata kai, don haka dole tayo nan. Kai baka ji zance ba sai kace ta samu tabin hankali. Kai! Talauci bai yi ba a duniya. Haka haka na harhada mata kayan abinci har da kayan sawa da na yara ta dinga kuka tana godiya. Duniya kenan" Ahmad ya gyda kai "kadan ma suka gani, duk wanda ba zai iya kallon ikon ALLAH yayi shiru ba sai ya tofa tashi ko yayi kazafi akai ba ai yana da jin haushi da bakin ciki in dai a wannan duniyar ne" Suna ta cin abinci yana tunanin ta inda ya kamata ya bullo mata da abunda ke ransa, can ya daure yace "wai ya naji ki shiru ne an yi watanni da yaye malam fa? Ta dafe kirji "don ALLAH Yaya kada ka ja min, ina zaman zamana ALLAH ne yace na huta Ka bar ni kawai" Yayi yake "haka ne, idan kin gaji ba sai na kawo miki kanwa tayi ba" Ta kalle shi da sauri da mamakin jin abunda yace amma ta kasa furta komai sai kada kai da yake kawai. Ganin haka ya sanya yace "Nana yanzu ace ga wata mace tana neman rasa rayuwarta ni da kaunata har ta dinga shiga cikin mawuyacin hali na jinya, zaki iya yarda na aureta? Gabanta ya kuma faduwa duk da tasan wasa yake yi tace "wata kila zan iya wata kila kuma ba san iya ba" Dadi ya cika shi jin ta dan sauko har tana murmushi yace "wani abu ne ke faruwa mai ban mamaki ma'u, wai kamar ni Alhaji Nura Kwangila ke roko har da durkusawa kamar zai yi kuka, Kodayake yana da gaskiya" "Akan me yake rokonka kuma? Ta fadi da fargabar jin abunda zai fada. Ya kalleta ganin har lokacin babu wani tashin hankali ko bacin rai akan fuskarta ya sanya ya cigaba da magana "ba zan boye miki komai ba ma'u, Nana ta nuna tana sona naki bata fuska har ta gaji ta sanar da ni da bakinta" Ma'u tayi mutuwar zaune akan kujera, sai taji kamar ya faskara mata gatari ne a tsakiyar kanta, ta kasa motsawa. Ganin bata ce komai ba Ahmad ya cigaba da magana. "Ban boye mata ba na gaya mata gaskiya bana sonta, hasalima ba zan iya hada matata da kowacce mace ba, ba zan iya yi mata kishiya ba, rannan da bacin rai ta bar ofis dina, Ashe wai har faduwa tayi a gida, bayan an yi bincike aka gano tana dauke da ciwon zuciya da ya kamata cikin dan lokaci. Bayan mahaifanta sun gano dalilin faruwar hakan suka ritsa ni da magiya kamar zai mini kuka akan na auri diyarsa na rasa me zance masa tunda na gaya masa gaskiya bana son diyarshi, daga karshe nace ya bari nayi shawara da iyalina tukunna" Har ya kammala bayaninsa ma'u tana jinsa kamar cikin gajimare yake yi mata ihu cikin kunnuwanta. Ta daina fahimtar komai, bugun zuciyarta ya sauya abunda ta jima tana zargi ya tabbata kenan ta kuma tabbatar Ahmad karya ya shirya mata