Sashe 18
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cewa "ka cigaba da bayaninka mana jibrilu" Malam jibril ya kalli raliya wacce ke sunkuyar da kanta kamar ta nutse a kasa tana kara matsa layar dake jikinta wacce take ganin da ita ce zata iya magana a yarda da ita babu tantama. "Ke raliya gaya musu su ji daga bakinki mana" Raliya ta fara inda-inda tana zare idanuwa "Daman... Cikin jikina..." Lami ta amshe "meye kike wani in-ina? Ki fito ki fadi gaskiya kada ki ji shakka ko tsoron wani" raliya ta dan samu kwarin gwiwa ta cigaba da magana "cikin dake jikina na ahmad ne shine ubansa" Ahamd ya mike a gigice yana fadin "ni karya kike mini WALLAHI, karya kike yi..." Malam Sulaiman ya kalli ahmad wanda jikinsa ya dauki rawa yace "ahmad sami guri ka zauna kada na kuma jin bakinka" Umma ta kalli malam Sulaiman da tsananin mamaki, domin tana ganin kamar malam din yana goya musu baya ne, kuma yana nufin dole ahmad din ya amshi cikin dake jikin raliyan. Ahmad da sauran 'yan uwansa suka dinga kallon babansu da tuhuma suna ganin ko mahaukaci ya san ta yanda zai yi wannan shari'ar balle shi. Malam Sulaiman ya mai da dubansa ga raliya yace "ki ci gaba da bayaninki muna sauraronki" Raliya ta dan ji karfin gwiwa tana zaton har ta fara gamawa da malam din ne tace "tun kafin na bar gidansa da cikin na tafi, kuma ya sani, shi kuma cikin ya kwanta nayi zaton ya fadi amma sai cikin watannin nan naga ya tashi, shine nace bari na dawo na gaya masa don ya sani" Aka sake yin shiru dai ana kallonta tana ibda-inda, umma tana jin kamar tayi zage-zage ta huce, sai kwafa kawai take yi. Lami kuwa sai gyada kai take yi tana fadin "haka ne kam" Auwal ya daga hannu da sauri yace "baba ina son zan yi magana don ALLAH" Malam Sulaiman yace "in dai akan maganar raliya da ahmad ne baka da ikon cewa komai, wannan magana ce da ta shafesu su kadai" Ya kalli raliya yace "kin kammala bayaninki ko?" Tace "eh na gama, amma WALLAHI baba cikinsa ne ya sani" Malam Sulaiman ya kalle Ahmad dake zaune baki bude kamar an dasa shi yace "kace duk abinda ta fada, shin da gaske kafin raliya ta tafi daga gidanka akwai cikinka a jikinta? Gaba daya aka mai da ido kansa, idanuwan ma'u yayi kwalo-kwalo, kirjinta ya dinga bugu tamkar ana lugude a ciki, jikinta kuwa tana ji kamar ya mutu, domin yayi sanyi lakwas. A cikin ranta addu'a kawai take yi. Ahmad ya dukar da kanshi kasa yana kada kai ya fara magana "Abba kuyi hakuri da abinda zan fada dole zata sanya ni fadinshi. WALLAHI TALLAHI tunda aka daura aurena da Raliya ko magana mai dadi ban taba yi da ita ba balle wata harkar aure ta shiga tsakaninmu, ban taba kusantar raliya a matsayin matar aurena ba WALLAHI" Umma tayi ajiyar zuciya cikin ranta tana hamdala ga ALLAH. Sauran ma duk ajiyar zuciya suka yi da jin dadi ban da Raliya DA lami da kuma malam jibril da yaji kamar ya kasa ta tsage ya shige cikinta don kunya. Ma'u kam wani irin hawaye mai dadi ne ya zubo mata, sai taji dukkan damuwarta ta yaye. Raliya kam fashewa tayi da kukan bakin ciki da takaici, domin ta tabbatar shegen bokan nan yaci kudinta ne kawai a banza, tunda gashi aiki bai yi ba, amman dai bari ta kara jarrabawa. Cikin kuka tace "kaji tsoron ALLAH ahmad WALLAHI wannan cikinka ne" "Karya kike yi ban san komai game da shi ba, koda ace cikina ne ma me ya sanya baki haife min shi a gidana ba ko anan gidan kafin ki tafi, sannan me ya sanya kika gudu daga gidana? Balle ma ni ban taba kama hannunki ba, kuma ke ma kin tabbatar da haka. Raliya kiji tsoron ALLAH ki tabbatar zaki mutu, ki fadi gaskiyar wanda yayi miki ciki" Cikin kuka tace "WALLAHI cikinka ne, don ka auri ma'u ne kaki amsa' Musa ya shigo da sauri yana fadin "karya kike yi munafika ba cikin ahmad bane wannan" gaba daya idanuwan kowa ya koma kansa ana kallonsa da mamaki. Kamar daukewar ruwan sama kukan raliya ya dauke ta fara wara ido. Lami kuwa fusata tayi ta cika ta batse ta dube shi da fushi tace "ubanka ne ya sako bakinka cikin wannan magana? Idan baka kiyaye ni basai nayi maka baki. Tsakanin miji da mata babu wanda ya san tsakaninsu sai ALLAH" Umma ta kalleta tana tabe baki don dai malam ya hanata magana ne da lami taji amsa sai kwafa kawai tayi tana gyada kai. Musa ya cigaba da magana ba tsoro balle shakka. "Lami ko zaki tsine min yau WALLAHI sai na tadi gaskiya, domin wannan diyar taki raliya a komai bace face bala'i da masifa, dukkan abinda ya sami gidan nan itace ke janyowa, da ta riki aurenta tayi biyayya ga iyayenmu da hakan bata same ta ba, amman ta rufe ido ta watsa mana kasa cikin idonmu. Tabbas wannan cikin ba na ahmad bane, domin na jiyo hirarta da kawarta dazu ina bandaki a lokacin da ita kuma tazo kusa da bandakin bata san ina ciki ba, suke tattaunawa akan maganar cikin." Nan ya kwashe labarin dukkan abinda yaji suna tattaunawa a wayar ita da kawarta ya sanar musu. Raliya ta kara rudewa, kunya duk ta cika ta kamar kasa tsage ta nutse a cikinta. Umma ta daga hannu sama tana fadin "Alhamdulillah yau sakayya ta bayyana, ga SHGE ya tabbata a inda ake ambatonsa kullum" lami kuwa wuki-wuki tayi cike da tsananin kunya tana muzurai. Raliya ta gama cutarta. Shi kam malam jibril fashewa yayi da kuka yana fadin "kin cuce mu raliya, kin zubar min da kima, ALLAH ya isa ban yafe miki ba" Malam Sulaiman ya daka masa tsawa yana nuna shi da yatsa "kai rufe min bakinka jibrilu. A haka ma baka yi mata baki ba ina kuma ga kayi mata baki? Ka barta kawai duniya ce ta ishe ta Riga da wando da duk wani abinda take takama da shi, tsakaninka da ita addu'a ce kawai ALLAH ya shirye ta" "Amman dai yaya yanzu sai a hana ni la'antar wannan yarinyar wacce ke yawon duniya da aurenta? Malam Sulaiman ya ce "Ai maganar aure ta kare. Kai ahmad saketa yanzun nan duk da dama ta samu" Ahmad yaji wani irin farin ciki ya baibaye shi wanda bai taba jin sa ba tsawon rayuwarsa, sai yaji kamar mahaifiyarsa Asma'u mahaukaciya ce ta dawo duniyar ta sanar da shi waye shi. Cikin kwarin gwiwa yace "Ni Ahmad na janye dukkan igiyoyin aurena akan raliya, na haramtawa kaina ita har abada" Raliya ta ja baya a tsorace sannan ta fashe da kuka mai karfi. Malam jibril ya fusata ya kai mata hauri da kafarsa. Ta ja ciki tana kuka. Malam Sulaiman ya yi sauri yace "baka da hankali jibrilu ko baka kula da abinda take dauke da shi bane? Hawaye ya zubo daga idon malam jibril ya juya a fusace yana goge idonsa yana kada kai da tsananin takaici a tattare da shi. Raliya ta cigaba da kuka zuciyarta na tafarfasa kamar zata kone. Lami kuwa kamar ta sanyawa gidan fetur da wuta su kone gaba daya kowa ya huta take ji, sai huci take yi kamar wata kububuwa. Malam Sulaiman ya dubeta yace "kin ga abinda ake gaya miki ko lami? Ka ki naka duniya ta so shi, ka so naka duniya su tattara shi su watsar a kwandon shara. Sannan kuma gori ba shi da amfani, bashi da rana, domin MANZON ALLAH (S.A.W.) ya hane mu da shi. Sannan dukkan abinda ka girantawa wani, kai ma wata rana sai ka wayi gari ALLAH ya jarrabeka da shi..." Lami ta tashi fuuu kamar an zabga mata bulala ta nufi gidansu. Suka bita da kallo da mamaki. Malam Sulaiman ya yi murmushi kawai don lami ba zata sauya ba. Raliya kam ta kasa yunkuri balle ta mike, domin kafafuwanta sun yi sanyi kwarai da gaske. "Ya kamata ku tashi ku wuce gidajenku haka ku kuma" umma ce ta fadi haka tana kallon yaran nasu, daya bayan daya aka fara mikewa domin tafiya. Raliya da ma'u kam suna jabe a wajen da suke zaune, kowacce daga cikinsu ta kasa motsi. Sai da Raliya ta jiyo ihun kiran lami daga cikin gidansu tana kwala mata kira sannan ta mike a sanyaye kanta a kasa cike da tsananin kunya da takaici ta wuce. 'Yan uwan nata suka bita da kallon tausayawa. Ma'u kam tun daga sanda taji irin sharrin da taso kullawa mijinta taji ta kara tsanarta bata ko jin tausayinta. Sai da umma ta kara yin magana sannan ma'u ta mike dakyar. Malam Sulaiman yana ta sanya musu albarka suka yi sallama suka fice. Akan babur suke tafe amma a tsakaninsu babu mai cewa da wani kala, kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa. Ahmad yana kara kallon iko da buwaya ta UBANGIJI yana masa godiya. Mutanen da suka sanya shi a gaba da gori yau an wayi gari ga yadda ALLAH ya nuna musu. Tun a duniya ma kenan. Ita kam ma'un tuananinta akan ace raliya ya cigaba da kasancewa matar ahmad ne da yaya zata yi da rayuwarta? A haka suka isa gidansu ba tare da wani yayi wa dan uwansa magana ba a tsakaninsu, sai tunane-tunanen zuci kawai suke yi. Sai da suka watsa ruwa tare sannan suka fara shirin kwanciya. Ahamd ya jima akan gado yana yin game a wayarshi amma Ma'u bata shigo dakin ba. Ya mike tsaye sanda ya ankara da jimawarta bata shigo ba, ya fito falo yana kiran sunanta da karfi. "Ma'u! Ma'u!! Ma'u!!!" Daga can cikin falon ya jiyo muryarta tana amsawa dakyar muryata kasa-kasa. Ya shiga falon da sauri. "Ma'u kina ina ne? Can bayan kujera ya jiyo ta tana fadin "gani nan yaya... Cikina da bayana zasu cire...! Ya isa gurin da take da sauri yana salati. "Cikinki da bayanki me ya faru? Ya tarar da ita ta kankame jikin kujera ta hada uban gumi sai kada kai take yi kamar mai hadiyar kunama. Cikin fargaba yace "yaya dai Ma'u lafiya, me ya faru me ya