Sashe 19
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo dake nan? Cikin karfin hali tace "tun a gidan su umma naji cikina yana ciwo, shine da muka dawo ya dan yi shiru yanzu kuma ya dawo na shigo daukar magani sai kafata ta rike na kasa tashi" Ahamd ya matsa gabanta sosai yana kokarin tayar da ita zaune. "Bari na tayar dake ko kuma mota zan nemo muje asibiti? "Wash! Yaya! Ba zan iya tashi ba, wani abu ne ya rike min kafa. Wash! Innalillah... Wayyo yaya...!!!" Ahmad duk ya rikice ya saketa ya ma rude ya rasa me zai yi. Ya nufi kofar fita yana fadin "bari na kirawo babar A'ilo..." "Kar ka fita... Kazo na mutu a gabanka yaya... Ka zo don ALLAH...!!! " Ya dawo da sauri da tsananin tashin hankali rungume ta gaba daya ya fita daga cikin hayyacinsa, labarin yanda mahaifiyarsa ta haifeshi kawai ke yawo a ransa, yanzu idan Ma'u ta mutu yaya zai yi da rayuwarsa? DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Ma'u kam tana durkushe kankame da kujera sai gyada kai take yi tana nishi. Shi kuma ahmad ya rasa mai ya kamata yayi mata. Cikin ikon UBANGIJI ya zabga wani irin nishi hade da doguwar kabbara, sai ga yarinya ta fado facal. Ihun yarinyar ne ya ankarar da ahmad, ya zura hannu ya janye yarinyar gefe a hankali don yaga kamar zata zaune ta, sai ga mahaifa ta fito itama gaba daya. Ma'u ta kwantar da kanta jikin kujera tana mayar da numfashi. Ahmad kam ya rasa me zai yi saboda sai ihu yarinyar take yi, ga mahaifa a jikinta. Ya Kalli Ma'u yace 'Ma'u me zan yi mata ne?" Ta dan kalli yarinyar tace "nima ban sani ba yaya, ka kirawo babar A'ilo" Da sauri ya fice daga falon ya nufi gidansu A'ilo ya tarar DA kofar gidan a rufe, don haka ya fara bugawa. Bai jima da fara bugawar ba suka bude. Mahaifin A'ilo ne ya fito yana tambayar "wane ne?" Yana budewa yayi arba da ahmad hankalinsa a tashe. Nan take ahmad yayi masa bayani, ya juya gida ya sanar da babar a'ilo, suka fito da hanzari suka garzayo gidan. ALLAH ya sa bai jima da yin siyayyar kayan haihuwar ba har da reza a cikin kayan. Kafin karfe dayan dare babar a'ilo ta kammala komai, ta gyara maijego da jaririya da kuma dakin. Ahamd kam shi ya wanke dukkan kayan da suka baci, cikin ransa yana jin son Ma'u da tausayinta na kuma shigarsa. Cikin daren su umma suka ji labari, don haka ana idar da sallar asuba umma ta gidan tun gari bai gama sha ba. Ta tarar da diyarta fes! Ranta yayi fari tas! Shi kuwa ahmad kwana yayi idonsa akan diyarsa, komai dake jikinsa shine a jikin wannan yarinyar. Ya rungume ta a jikinsa kamar zai mai da ta ciki. Yayi tayi mata addu'a duk wacce tazo bakinsa. Ma'u dariya kawai take yi masa, da yake su kadai suka kwana a cikin dakin nasu, suna ta sambatu akan diyar tasu. Umma ta dora mata ruwan wanka, tayi wa Ma'u da jaririyar wanka, duk inda suka shiga ahmad ma biye da su, sai da ta hada shi da rikon diyar tasa ta shiga yiwa Ma'u wanka sannan ta sami lafiya, domin zama yayi ya kurawa diyar ido kamar ya lasheta, amma yana jin abu biyu a cikin ransa farin ciki da bakin ciki. Tun yanzu har ya fara tausayawa diyar tasa, domin 'yar zata tashi cikin gori DA tsangwamar cewa babanta shege ne, har su umma suka fito bai sani ba sai DA umma tace "Ahmadu wai me kake kallo ne haka? Sannan ya wayance ya goge hawayen dake zubo masa ba tare da ta gani ba, ya mike ya ajiye yarinyar ya fice. Tun safen umma tace masa ya kamata su wuce da ma'un asibiti a duba ya sosai da kuma jaririyar tata, domin haihuwar gida hatsari ce, musamman ga masu karancin shekaru irin ma'u. Sannan daga can asibitin sai ta wuce da ita gida ta zauna a can. Duk da bai ji dadin karshen maganarta ba, amma ya danne yayi ta maza, domin umman tashi tafi shi iko da su baki daya. Sarai ta kula da yanda ya dan sauya, amman sai ta basar da shi domin idan ta biye masa ba zata je da ma'un gidan ba. Tunda cikin Ma'u ya cika wata bakwai taso Ma'u ta koma can gidan ta zauna, amma yanda ahmad ke nunawa da an tayar da maganar ya sanya ta rabu da su. Domin ta kula akwai wata soyayya mai karfi da shakuwa a tsakaninsu, sai taji tausayinsu, amman a yau dai babu wannan maganar. Ta katse shi ganin yanda yayi soror yana kallonsu tace "yaya dai, yau ba zaka je aikin bane? Da sauri yace "umma nayi musu waya na sanar da su matata ta haihu, bari naje na dauko motar taxi sai mu tafi asibitin" Umma tayi murmushi "Ahmadu babu dama, sai kace kaine ka haihu din? Mintuna kalilan ya dawo DA mota taxi. Umma tace masa "ba tare da kai zamu tafi ba fa manya" ya kalle ta DA mamaki "umma saboda me, ai ko diyar na rike muku ko? "Diyar gidanku mara kunya." Kunya ta kama shi ya kau da yana dariya, Ma'u ma dariya ta saka. Umma tace "goyata zan yi, kai ka hada kayan ma'un kayi gaba sai ka wuce da su gida sai mu tadda ka acan" "Amma dai umma har nawa kayan zan hada ko? Don WALLAHI ba zan iya kwana a wannan gidan ni kadai ba" ya marairaice kamar zai fasa kuka. Umma tayi dariya tana fadin "idan dai zaka iya kwanan shago ai shikenan" gaba daya sika fashe da dariya. Duk wani duba an yiwa Ma'u bata sami matsalar komai ba, su kansu likitocin sun yi mamaki, domin ganin ma'un tana da karancin shekaru, amman dai sun san kowacce mace da irin jikinta, musamman ita da ta haihu a durkushe. Daga karshe dai sun bata magunguna ita da diyar suka wuce gida. Matan yayyenta da su yayyen dukansu suna gida suna jiran dawowarsu. Ahmad sai basu labarin kamannin diyar yake yi ana dariya, kowa ya kagu su dawo din. Sanda suka iso gida ya cika da hayaniya, aka dinga shigowa barka. Hayaniyar ce ta sanya lami da 'ya'yanta suka gano wani abu yana faruwa a gidan, ta kira amina ta turata domin ta gano mata abin dake faruwa a gidan. Amina ta dawo ranta a bace ta kasa yin koda magana. Lami ta dubeta tace "malama ki gaya mana abin dake faruwa mana kin shigo sumsum sai kace tunkiya" "To me zan gaya miki, wai wannan banzar ce ta haihu" lami ta tashi a gigice cikin firgici tace "ba dai Ma'u ba" "Ita mana, sun cikawa mutane gida da ihu banzaye kawai" Lami ta koma ta zauna tana huci kamar zata fashe da kuka. Raliya kam ta kasa cewa komai sai kallonsu kawai take yi, ita kadai ta san me take ji a cikin ranta. Lami tsinuwa da baki babu irin wanda bata yiwa diyar nan da aka haifa ba, amman da ikon ALLAH ya cika babu yanda za a yi. Ma'u taga karamci daga gurin 'yan uwanta da mijinta, don duk kudin hannunsa da wanda yake tarawa akan diyar nan ya karar dasu. Ita ma Hajiya Amina ta dauki soyayya ta dora akan diyar nan, kullum sai tazo ta ganta, sai take tuna mata da ahmad sanda yana jariri. Rashin shigowar lami da 'ya'yanta bara ya daurewa umma kai kwarai da gaske, amman ta danne abun a cikin ranta. Ma'un ce ma mai yi mata korafi har sai da umman ta kwabe ta. Gurin yiwa diyar huduba ma sai da aka sami sa'insa, domin shi Ahamd sunan umma yake son a sa mata, ita kuma umma ta dage sunan mahaifiyarsa za a sanya, domin ita sunayenta da tawa. Auwal ya saka, sani shima ya saka. Ita kuwa bayan Ma'u babu mai sunanta. Dakyar ya amince da hakan aka sanyawa diyar suna ASMA'U, sai yake ji kamar mahaifiyarsa ce ta dawo masa son diyar ya rinka shigarsa. Ranar suna anyi suna main kayatarwa irinna masu rufin asiri, an ci ansha daidai Misali. Wannan abu ya kuma komawa lami rai. Raliya kam har kuka tayi, ta kunshe cikin daki ta kasa ko lekowa waje, da tuni itace zata haifi wannan diyar ta halak, ta yiwa kanta, tabbas ta shiga tsananin da ta sani, wacce Hausawa ke cewa keya ce. A daren ranar suna ciwo ya kuma raliya cikin daki, tun tana abin ita daya har ta fara kiran mahaifiyqrta. Lami ta shigo cikin dakin suka ci gaba amma shiru babu haihuwa sai azaba. Tun lami tana ganin abin kamar wasa ne har ta fara tsorata. Shi kam malam jibril tunda ya fuskanci abun dake faruwa ya shige cikin daki ya rufo kofa. Lami taga haza taje ta buga masa tana kuka. Ya bude kofar ransa a bace yana fadin "yaya aka yi lafiya dai ko? Cikin kuka tace "raliya zata mutu jibril ka taimaka min" ya galla mata harara "rayuwar raliya da mutuwarta duka daya ne a gurin lami, don gwara ma ta mutu ko na huta da abin gori" ya juya ya shige cikin dakinsa ya ja kofa. Lami ta fashe DA kuka gami da juyawa dakin da gudu saboda jiyo ihun diyar tata da take yi, suka ci gaba da fama amma har tsakiyar dare shiru. Shi kansa malam jibril sai da ya karaya ya leka dakin, halin da yaga diyar tashi ya daga masa hankali kwarai da gaske, ya gogice yana tambayar yaya za su yi? Lami tana kuka tace "asibiti za a kai ta kawai" ya dan waro ido waje. "Asibiti kuma! Gashi ban da ko kwandala, shi kuma asibiti sai da kudi kin sani" "Kaje gurin yayanka mana ai ba zai hana ka ba ka sani, ka taimaka don ALLAH jibril" Ya juya a kidime ya nufi gidan yayan nasa, ya jima yana buga kofar da zata sada shi da gidan yayan nasa, can jimawa malam Sulaiman ya ISO yana tambayar waye? Malam jibril yace "nine jibril" malam Sulaiman ya bude kofar