Sashe 27
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
boye miki? WALLAHI babu wani abu tsakanina da Nana, kalle ni da kyau ban yi kama da mai karya ba" Bata ce komai ba ta fara kokarin tafiya, amman bai bata damar hakan ba, ya riko hannunta ya rike gam da karfi, tayi kokarin kwacewa amma ta kasa ko motsawa. Cikin kuka ta cigaba da magana "ka sake ni ba zan yarda da duk abinda zaka ce ba yaya" Ya janyota jikinsa ya matse ta tsam tankar zata koma cikinsa tana cigaba da kuka da cewar ya saketa, amman ya ki matsawa duk da dukan da take kai masa bai ji ko dar ba. Sai da ya tabbatar ta sare ba zata iya kwacewa ba sannan yace "ma'u ki yarda da ni, babu kowa a cikin raina bayan ke, kece zabin iyayena kece kuma abar sona" ya dinga surutai da ban hakuri" Ta fara rage kukan don yanayinsa da yanda kalamansa me fitowa ya fara kashe mata jiki, ya sanya harshe ya fara lashe hawayenta dake zuba ya sassauta rikon da yayi mata ta daddage ta ture shi tana dariya saboda cakulkuli da yake mata, ya fadi wanwar a kasa ya dafe keya ta fashe da dariya, shi kam dadi ya ji don ya kula ta fara saukowa, ta juya ta nufi cikin dakin bacci. Dukkan abunda ta ajiye masa wanda ta girka sai da ya cinye, kasancewar bai ci komai ba tunda ya fita bayan dan kunu da cincin a ofis, kasancewar Nana ba mai cin abinci bace sosai shiyasa bata damuwa ko ta wuni bata ci abinci ba. Wannan ya sanya zuciyar ta dan ji sanyi, ta kara yarda mijin nata ba shan ice cream suka fita ba. Shi kam kallonta kawai yake yi tana ta wani kwarkwasa jikinta ya kara cika da kyau kasancewar tayi yaye cikin satin, sha'awar matarsa da begenta sun cikashi. Sanda ya fito daga wanka sai ya tadda ta sanye da sabuwar shiga cikin kayan bacci wadanda ya san tayi ne don tsokana. Komai na ma'u burge shi yake yi, sai dai a ransa yana mamakin irin wayewar ma'u da yanda ta iya tsara kwalliya. Kodayake yasan tana yawan kalle-kalle da karance-karance, wata kila ta hakan take kara samun wayewa. Ganin irin kallon da take yi masa ya sanye ya nufe ta kai tsaye da dariyar mugunta, tana hango shi ta tashi ta zura da gudu tana dariya, ya rufa mata baya da yake ba ta da wani jiki ta iya gudu kamar 'yar barewa, don haka ya kasa cimmata sai da ta nufi kicin ya sanya kafa ya sharbe ta, saura kiris ta zube kasa amma ya tare ta, ta fara mai da numfashi da tsoro tana fadin "amma yaya baka da kirki da na fadi fa?" "Ba ma zaki fadi ba" ya bata amsa kafin ya fara aika mata wasu sakwanni da suka fara rikita mata lissafi. Ahmad namiji ne da ya iya mallake dukkan zuciyar mace, musamman da yake kakkarfa mai kirar zaki. Dakyar ma'u ta lallaba shi suka nufi daki don taga karatun nasa ya fara wuce saninta. Cak ya dauke ta tamkar wata 'yar tsana, sai da ya tabbatar ya wanke mata zuciya fes ta ta yarda babu wata mace a cikin ransa bayan ita. Daren wannan rana sai ya zamto musu kamar daren amarcin da ba zai gogu a cikin rayuwarsu ba. Ga Ahmad yana yin iyaka kokarinsa wajen ganin bai kara yin wani abu da ya shafi Nana a gaban ma'u ba, ko sunanta bai iya ambata balle wani abu da ya shafe ta. Yana kallon kayan da ta baiwa yaran ma'u bata taba sanya musu shi ba, ta ma ajiye su guri dabam, amma bai taba nuna damuwarsa ba don bai son rikici, sai da ita da kanta taga dacewar ta sanya musu din ta saka musu da kanta. A ranshi ya yaba da kayan, amman bai iya fitowa ba don ganin irin kallon da take masa na tuhuma, sai ya bar abin a cikin ransa ya nuna kamar bai gane kayan ba ma, hakan ya dan sassauta mata damuwarta. Hm kishi kenan kumallon mata DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Ranar wata lahadi ta farkon wata lokacin Ahmad aljihunsa akwai nauyi, ya tattara iyalanshi da matarshi don fita yin siyayya a kanti. Yaran suna cikin kwalliya gwanin sha'awa kamar 'ya'yan turawa. Yayin da mahaifiyarsu ke sanye da atamfa ta amshi jikinta riga da siket, gyalen da kayan kamar tare suka zo. Haka nan takalmi da jakar hannunta, idan baka sani ba ba zaka yi zaton ma'u uwar yaran bace, don bata yi kama DA wacce ta haihu ba sam. Sun siyo abubuwan da suke bukata, masu tsaron gurin suka rako su aka zuba a mota, suna shirin shiga mota suka jiyo muryar mace daga can bayansu yana fadin "Ahmad" gaba dayansu su daga kansu ga kinda sunan yake fitowa. Muryar nan ba bakuwa bace a gurinsu, ko bayan shekaru dari suka ji ta sai sun gane ta, mamaki ya kama su gaba daya. Ummi ce tsohuwar budurwar Ahmad, bata cikin kazamar shiga amma babu alamun jin dadi a tattare da ita, kayan dake jikinta sun nuna haka. Ta karasa kusa da su da farin ciki tana fadin "Ahmad kayi mamakin ganina ko?" Yayi saurin wayancewa tana kallon ma'u don ta hade rai nan da nan yace "ban yi zaton ganinki ba ma, ya kike?" Da sauri tace "lafiya lau Ahmad, shikenan sai ka buya' Ta kalli yaran dake gabansa tace "Woo! Wadannan kyawawan yaran fa?" Cikin sauri yace "yarana ne" Mamaki ya kama ta tace "yaranka fa kace? Yanzu har kayi aure ka haifi wadannan yaran lallai ka cika mai sa'a" Ta kalli ma'u tana kokarin tunota. "Wai wannan ba ma'u ba ce ba?" Ma'u ta dan yi yake amman ta kasa magana Ahmad ne yace "ita ce mahaifiyar wadannan yaran da kika gani" Ummi ta dan ja da baya da fargaba da mamaki tana fadin "wai kana nufin ma'u ka aura Ahmad? Ma'u kece matar Ahmad?" Ma'u tayi murmushi "WALLAHI kuwa, haka ALLAH ya kaddara. Yaya mu wuce ko?" Tana kallonshi take magana, don ganin irin yanda fuskarsa take. Bai ko kalli inda Ummin take ba yace "OK sai an jima Ummi." Ya suri malam suka nufi motarsu, Ummi ta bisu da kallo da tsananin mamaki ta kasa furta komai. Ahmad ne ya zama haka? Wani irin sonshi da sha'awarshi suka bijiro mata. Da tuni itace mai wadannan kyawawan yaran. Gaskiya mahaifanta sun cuce ta. Sai hawaye ya fara biyo kuncinta. Tana tsaye tana kallonsu har suka ta da mortar suka yi nisa. Sai ta ji ta fasa siyan hodar da ta zo siya, ta juya da sauri tana tsai da adaidaita sahu, daman ta zo siyan hoda da kuma rage yamma ne kamar yanda 'yan mata da zawarawa keyi. Ga ma'u kam hade rai tayi katamau zuciyarta kawai ke tafasa. Irin kallon da Ummi ta rinka yiwa Ahmad ne ke bijiro mata. Wai Ummi tana da aure ne ma ko bata da shi? Ko tana da aure ko bata da shi ba damuwarta bane, damuwarta daya kallon da Ummi ke yiwa mijinta kamar zata lashe shi danye. Ma'u tana tsananin kishin mijinta, bata son kowacce mace ta ko kalle shi ma. Ahmad ya kula da halin da ma'u ta shiga, ko kadan baya ganin laifinta akan kishin da take yi, sai ma jin dadi da hakan ke sanya shi, don burinshi a duniya bai wuce ace matarshi na matukar kaunarshi ba, irin abunda ya so samu kenan ga Ummi kasancewar tana tsananin son shi, ashe ba ita ce matarshi ba. Ya sanya hannu ya zunguro ma'u daidai inda ke sanyata dariya, ta noke amma taki dariya sai ma cewa tayi "don ALLAH yaya ka bari" Yace "na ki na bari sai kin bani labarin da kika ce zaki bani na Amina" Ma'u ta dan yi yake tana fadin "Yanzu kuma na fasa sai wani lokacin, bana jin dadi" Dariya taso kwace masa amman ya dake yace "yarinya waye ko yake jin dadi a wannan lokacin?" Haka ya dinga janta da Hira tana basarwa har suka isa gida, shi kuma bai nuna mata ya damu ba sam. Sai da aka yi kwanaki biyu babu wata magana ko wani abu da ya shafi Ummi da ya fito daga bakin mijinta sannan hankalin ma'u ya kwanta, ta tabbatar lallai mijinta ya manta da rayuwar Ummi gaba daya. Ga Ahmad ba haka abun yake ba, tunda yaga Ummi yake tunanin rayuwarsu ta baya, idan yace baya son Ummi a zahiri yayi karya. Yau yana zaune a ofis ayyuka sun sha gabansa, wayarsa tayi kara. Ya duba yaga bakuwar lamba ce kamar bai zai dauka ba, haka ya daure dai ya dauka. Yana dagawa yaji an ce "Ahmad" sai yayi saroro da mamaki saboda jin muryar Ummi da duk rintsi duk tsawon shekaru ba zata bace masa ba. Da mamaki yace "Ummi ina kika samu lambar wayata?" Ummi tayi yake tace "Ai mai son dan tsuntsu shi yake binsa da jifa. To kafin komai dai ya kake ya aiki ya yaranaka?" Ya jingina da kujera yace "duk suna lafiya. Hajiya da sayyada suna school, malam kuma yana tare da ummansa a gida". Tayi doguwar ajiyar zuciya tana yake kamar tana gabansa tace "Ahmad da ma'u 'yan gata, domin kowa ya samu sa'a da iyaye irin naku ya more" Ya bata fuska don ya soma gano inda ta dosa yace "haka ne ko?. Tace "babu tantama, ba zan ja ka da nisa ba Ahmad na jiyo dukkan abunda ya faru da rayuwarka bayan rabuwarmu da kai, da yake har gobe kaine zabina, sai dai na jima ina tunanin yanda muka rabu kamar daman ka gaji da nine abinda nayi maka ina cikin fushi da bacin rai ne Amman kaima ka biye min. Tabbas a wannan lokacin daga ni har iyayena muna cikin fushi na zuga da korafi da ake yi maka sanda muka huce kuma muka tabbatar ka guje min kamar daman ba sona kake yi ba, tunda ka tafi baka taba waigowa ba, me ya sanya Ahmad?" Ta fama masa wani tsohon ciwo da ya jima yana cin