Sashe 39
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da maganganun Maryam sun shigi Ma'u amman KISHI ya rufe mata ido tace ita a kyaleta, sai Maryam ta roke ta Ko message ne tayi wa 'yan gidansu ta sanar da su inda take don hankalinsu ya kwanta, Sai Ma'u tace ashe ma tana fatan Ahmad ya dawo mata ma kenan. Haka suka dinga tataburza har dare yayi, sai dai wani abu da yake bawa Maryam mamaki shine, tsawon yinin wannan rana Ma'u tana kallon hoton Ahmad mijinta a wayarta da ta Sanya sabon layi, abun sai ya baiwa Maryam dariya. Wajen karfe goma na dare aka far buga kofar gidan da yake gida ne na irin na kananun nasu rifin asiri babu maigadi. Da sauri Maryam ta dauki wayarta tana cewa "yauwa ka karaso? To gani nan zuwa" ta nufi kofar sam Ma'u bata kawo komai a ranta ba. Tana kwance akan kujera ta runtse idonta har suka turo kofa suka shigo. Kamshin turaren da taji ne ya sanya ta bude idonta da sauri, turaren Ahmad daya ne tun yana talakansa har zuwa yanzu da yayi kudi, don haka ko cikin bacci ba zai bace mata ba. Yana tsaye jikin kofa idonshi yayi jajir, kamar gauta, duk yayi baki ya rame yini daya tal. Bakin ciki ya cika Ma'u ta kalli Maryam da tsananin takaici da harara. Maryam tace "kiyi hakuri Ma'u idan har na bar mijinki da iyayenki cikin damuwa bayan na san halin da kike ciki ban yi musu adalci ba, ban kuma cika masoyiyarki ta gaskiya ba" Ma'u ta mike a fusace ta nufi kofar fita, amman Ahmad ya cafkota ya matseta tsam a jikinsa, ta dinga fizge-fizge da kokarin kwacewa amman ta kasa, sai ta fashe da kuka tana fadin "me ya sanya ka biyo ni, nace bana son aurenka kaje ka zauna da 'yar uwarka jininka ka barni na tafi don ALLAH yaya! Ka tafi yaya" tana magana tana kuka amman tana rike gam a jikinsa ya ki sakinta. Sai da tayi mai isarta tayi shiru tana shesshekar kuka, Maryam tana tsaye tana kallon ikon ALLAH, soyayyar Ma'u da Ahmad na burge ta. Cikin sanyin murya Ahmad ya far magana "WALLAHI Ma'u da Maryam bata sanar da ni kina gidanta ba da babu abunda zai hana zuciyata bugawa, tun dag lokacin da na gano baki tare da ni ban huta ba, ban sha ruwa ko mukurya guda ba, ban ci abinci ko loma daya ba, ban huta ko na minti daya ba. Ma'u kece rayuwata ke nake so, ki yarda da kaddara ki amince Nana matata ce ta kaddara da zan rike kamar yadda addini yace babu zalinci, ke musulma ce Ma'u kin yi imani da ALLAH me ya sanya ba Zaki yi imani da aurena ba, me ya Sanya ba Zaki yarda ba? Na san nayi miki laifi amman bai kai ki kuntata min da guduwa ba, kin taba kokarin guduwa tun kina amarya ALLAH ya rufa min asiri, ko baki san gudun mace daga gidan mijinta masifa bane ba? Ko baki ga masifar da ta samu raliya ba? Shin kina son ke ma ta same ki Ma'u?" Yanda ya dinga maganar tasa sai ya kashe mata gwiwa, har taji da ta sani bata taho ba. Sai gashi tana bashi hakuri, lallai ta gano mijinta na tsananin sonta. Wannan abun kamar shirin fim ya zamewa Maryam, wai sai ga su sun shirya sunan fadin zasu tafi. Da mamaki Maryam tace "ina ai dare yayi, ku bari ku kwana anan mana da safe sai ku wuce" Yace "kiyi hakuri bai kamata mu kwana babu izinin mijinki ba, na riga na kama daki a hotel zamu kwana a can, na gode kwarai da gaske. ALLAH ya bar zumunci" Ya dauko bandir din kudi da bai san adadinsu ba ya bat ta amsa da zumudi yana godiya, don daman wata yayi nisa bata da kudi, kuma komai nata ya kare. Har gaban mota Maryam ta r akasu, sai da ta ga tafiyarsu sannan ta juya ta nufi gida. Bayan ta kulle gidan a ranta tana cike da sha'awar soyayyar Ma'u da mijinta Ahmad. Su dai kam ba su yi sa'ar aure ba sam. A can hotel din Ahmad ya dinga lallaba Ma'u dakyra ta yarda zata yi wanka tace amman ba zata yi tare da shi ba, dole ya kyaleta. Tana daga bandakin taji Kira ya shigo wayarshi, don bai jima da kunna wayar ba, sai ta jiyo shi yana amsawa da bacin rai "eh na ganta... Ban san sanda zamu dawo ba gaskiya... Sai da safe...! Daga yanda yayi maganar ta san da Nana yake, sai taji tausayin Nanan ya kamata tana bin namiji yana mata yanga. Shi kuma haushin Nana yake ji yanzu don yana ganin kamar ita ce ta janyo masa duk wannan matsalar ma. A bangaren Nana har sai da tayi hawayen takaici. Duk da Ahmad ya so samun wani abu a gurin Ma'unsa amma sai yaga ta hade rai ta kwanta a falo ma, dole ya kyaleta. Washe gari da safe suka wuce Kano. Nana taji dadin ganinsu tayi murna, ya hada su guri daya yayi musu nasiha da rokon arzikin su zauna lafiya. A gurin Ma'u tace ta baiwa Nana kwananta na wata guda, Ahmad bai ji dadin hakan ba, amman babu yanda ya iya tunda lallabata yake yi. Ita kuwa Nana dadi ne ya kama ta har farin ciki ya bayyana a kan fuskarta. Cikin wannan watan Ahmad ya shig tsananin damuwa da tashin hankali, yayin da Nana ta more amarcinta yanda ya so, mijinta ya debe mata dukkan damuwa da kewa. Ita kuwa Ma'u da wannan damar tayi amfani gurin neman NAFISA LILI 'YAR NIJAR ta harhada mata magungunan gyaran jiki MAI DA TSOHUWA YARINYA ta dinga sha da tsarki da na turare. Cikin wannan lokacin da kanta ta san ta sauya, don haka Ahmad idan ya ganta kamar ya cinyeta, don akwai sanda ya gaza hakuri ya matseta a daki suka dinga rikici yace WALLAHI ta dauki alkawarin ba zata ci amanar Nana ba sai dai yaje gabanta ya gaya Mata shine yace sai ta karya alkawarin ta, abun da ta san ba zai iya ba. Haka dole ya hakura ya kyaleta don ba zai iya yin raping din matarsa ba, don yana matse kwarai da gaske, dole ga Nana ya kai bukatarsa. Wannan yayi wa Nana dadi, wannan abu da Ma'u tayi mata ya sanya take girmama ta kwarai da gaske, sannan ta riketa kamar 'yar uwarta, za a yi wasa ayi dariya daidai gwargwado. Amman ranar da Ahmad zai koma dakin Ma'u Nana ta raina kanta ganin yanda yake ta zumudi da rawar kafa har taji KISHI ya rufe ta a ranta tace sai kace ba gurin tsohuwa zai je ba. Tun daga irin rigar baccin da Ma'u ta Sanya ta tsokano shi ya dinga wani irin kallon da tana wani kwarkwasa da yanga har dai ya gaji ya janyota yana fadin "yarinya WALLAHI baki isa ki haukata ni ba" Ya fashe da dariya don ta gano ya shig tarkonta. Ranar kam sai da ta raina kanta don a daren nan sai da ya fanshe watanshi guda, musamman da yaji ta kamar ba Ma'unshi ba ta koma masa wata 'yar budurwa kamar daren amarcinsu. Wannan daren kam sun karar da shi gurin nunawa juna yanda suka yi rashin juna. Ahmad ya gama gano yanayin matansa, don haka ya ci maganin Zama da kowacce daidai da halinta. Ita dai Nana tana da tsananin bukata, don haka kafin girkinta ya fita sai ta ishe shi. Ita kuma Ma'u shine yake da tsananin bukatarta saboda gyara da kuma yanayin halittarta, don haka har Nana ta gano shi ran girkin Ma'u doki yake yi da zumudi, ita ma Ma'u ta gano hakan, sai dai yana iya kokarin sa gurin ganin cewa ya kamanta gaskiya da adalci a tsakaninsu, sai dai bai isa ya boye soyayyar Ma'u ba, duk da ita ma Nana yana bata wani matsayin na ita ce jininsa 'yar uwarshi da yake sun fahimci juna sai suka zauna lafiya. Cikin shekarar ne duk ALLAH ya albarkace su da samun juna biyu, Nana ce ta far haihuwar katon namiji yaci sunan Alhaji Abdullahi (Mujahid) yaron yaga soyayya da gata gurin dangin 'yan leman. Sai kuma Ma'u da ta kara haifo mace. Ita ma ta samu gata. Ahmad dai shine mutumin da ya karya alkadarin camfin danginsu na haihuwar da daya ko biyu, sai gashi da biyar cur! Wannan ya Sanya iyayensa jin dadi. Adalcin da Ahmad yayi a gidansa da ya kwantarwa da Ma'u hankali shine hana Nana yin aiki yace shi ya dace ya nemo, duk da Nana ta damu da farko, rigima har gaban babanta amma bata samu goyon baya gurin iyayen ta ba dole ta hakura, don babanta yace ita kanta mahaifiyarta digiri biyu gareta kuma saboda kwarewarta a makaranta suka hadu suka yi aure, amman bata aiki saboda family dinsu suna da tsananin KISHI, wanda tayi a baya ma ALLAH ya amfana. Hakan ya sanyayar mata da gwiwa. Ahmad ne yayi kokarin kulla auren mahaifinsa da Hajiya Amina don mijinta shekaru biyu kenan da rasuwarshi. Hakan yayiwa kowa dadi musamman kakarshi da ta damu yayi aure. Ita dai Nana tun daga haihuwa daya shiru babu kari da yake itama jinin iyalin ne suke tabata. Game da Ummi kam yanzu ta yarda Ahmad yafi karfinta ta gano matsayinshi dole ta samarwa kanta lafiya, amma iyayenta sun yi da sun sani da takaici, musamman da mahaifinta ya gano mahaifin Ahmad tsohon ubangidansa ne, shike bashi kaya kafin kaninsa ya cigaba da bashi. Wata rana kafin tayi aure ta hadu da shi a super market ta gaya masa shi kadai take so amma ta hakura da shi zata auri wani, ta bashi tausayi kwarai da gaske, sai dai ya san bai isa ya karawa Ma'u kishiya ba, sai ya amshi lambar account dinta ya tura mata kudi masu yawa wanda da su ne tayi komai na aurenta. Wata rana sun je gidansu da yamma ana ta hira suka jiyo kuka a harabar kofar gidan, suka fito da sauri da su Umma da su Ma'un da yaya Auwal da sauran da yake duk ranar Lahadi da yamma anan ake haduwa ayi ta hira. Lami suka gani da wata