Sashe 12
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
magriba, yau ma haka ya shigo gidan. Tunda soro ta taro shi ta amshi jakar da yake goyowa a bayansa ta uniform da takalminsa irin nasu na ma'aikatan gidan man. Ya karaso tsakar gidan ya kafe babur dinsa sannan ya janyo ya jikinsa ya matse. Tayi dariya tana fadin "gaggawar ta meye bayan taka ce ni jai kadai, babu mai gutsirar maka? "To meye don na taba kayana kuma za a damu? "Bar maganar haka je ka cire kaya kayi wanka tukunna" Bai yi musu ba ya sumbaci wuyanta sannan ya wuce domin yana dawowa wanka yake fara yi kafin komai, domin an yini cikin rana. Har sai da ya ci abinci ya koshi, suna falo suna kallo sannan ma'u ta bijiro masa da abinda ke ranta. A lokacin kanta yana kan cibyarsa yana wasa da gashinta suna cikin nishadi. Ta dan dago ido ta kalle shi tace "yaya akwai wani Abu dake damun zuciyata, ina son gaya maka kullum amman ban san ya zaka dauki abun ba" Ya lakace mata hanci yana murmushi "yaushe muka fara 'yar haka da ke ma'una, ki boye abu a ranki ya sanya miki ciwon zucuya, idan na rasa ki me kike tunanin zai sami rayuwarta? Tayi murmushi "sai ka sake wata matar 'yar gayu..." Tayi kara saboda mintsininta da yayi ya bata rai. Wacce mace ce zata auri mutum irina? Ai idan na rasa ki ni ma na rasa kaina, bayan su Abba babu Wanda zai kara ba ni matar aure har abada... Ta mike zaune da sauri tatoshe bakinsa. "Ya isa haka, ba zan mutu ba sai ka riga ni mutuwa da shekara ashirin da daya" Ya kuma mintsininta yana dariya, ta sanya ihu ta Zame tana fadin "kai yaya Wallahi ka iya mugunta" mugunta ko gaskiya? Yaya za a yi ba yarda na mutu na bar ki har tsawon Shekaru ashirin da daya? Wato wani ya aure mini ke ko? Na ki wayon, rana daya za mu mutu ni da safe ke da yamma" Yanda yake maganar babu dariya ya sanya ta fashe da dariya tana fadin "ka ji yaya kamar ka leka littafin kaddararmu ka san komai, ni dai ba zan mutu da wuri ba gaskiya." An ji an bar miki gadin duniyar, amman gaya min abinda kike boyewa yanzu ko na samu kwanciyar hankali, don har Kin daga min hankali yanzu" Ta yi ajiyar zuciya da fargaba, don bata san yanda zai dauki maganar ba. Ta tsare da idanuwanta sannan tace "yaya ina son ci gaba da karatu ne" gaba daya annurin fuskarsa ya dauke kamar ha shi ne mai dariya ba yanzu. Hakan ya kara haifar mata da faduwar gaba amman sai ta ji yace "karatu kuma kamar yaya? Tana kallonshi har lokacin tace "karatuna na boko mana har da na islamiyya ma, don kaga abokan karatuna har sun yi candy, ni kuwa ina ya zaman banza." Wannan kalmar ta karshe ta shige shi har ya kalleta da sauri yana kuma maimaita maganar. "Zaman banza fa kika ce ma'u, zaman auren ne ya kasance abin banza? Ta wayance da faduwar gaba tace "ba haka nake nufi ba yaya, ina nufin wai ina zaune haka babu komai ga abokan karatuna har sun yi candy" Yayi shiru yana sauraronta kamar ha zai yi magana ba, da ya ji tayi shiru ta sunkuyar da kanta kasa ganin yadda yake kara daure fuska duk sakwan daya yaci gaba da magana. Ya kamata ki gane aure shi ne gaba da komai a rayuwar 'ya mace, sannan ina da halin da zan iya rike ki kiyi karatu amman a yanzu lokaci ya kure, ba zan iya kallon ki kina fita kullum da sunan karatu ba wasu na gane min mata, don haka ki cire maganar karatu cikin kundin burikanki" Yana gama fadin hakan ya mike tsam da nufin ficewa daga cikin dakin, amman maganarta ta hana shi fitan. "Haba yaya kada ka zamto irin mazan nan masu daukar mace tamkar baiwa. Kai ma kana yin abin da ka so, ya kamata ka ba ni dama ni ma ko sau daya ne a rayuwata, gaskiya ba ni da burin da ya wuce ganin na yi karatu" Ya waigo baki bude jin kalaman da suke fitowa daga bakin ma'unsa kamar wanda ta rubuta a cikin littafi take karantowa. Amman sai ya ga ba haka ba ne shi din take kallo kyar! Kuma tana ci gaba DA zakulo abin dake ranta. Ya so ya kyaleta ta cigaba da maganarta amman sai ya kula bata cikin nutsuwarta don haka da sauri ya daka mata tsawa yana fadin "ki kame bakinki ma'u, in har ni ne mijinki kuma sai da izinina zaki yi karatu, na gaya miki ba zaki yi ba har abada. Don haka ki sanya wannan a ranki. Ina kuma gargadinki akan kada ki Kara yi min irin wannan zancen daga yau" ya nufi kofa da sauri yana huci. Wani malolon takaici ya taso ya tokare zuciyar ma'u. Wanne irin miji ne Allah ya bata mai kishin tsiya da son kanshi? Ban da son kai kullum shi yana waje amman ita ko unguwa zata sai ta kau ruwa rana da shi, yanzu kuma ya sani sarai karatun nan akwai alfanu a ciki amman ya rufe idonshi ya hana ta don kawai yana takamar yafi kowa kishi. Sai ta fashe da kukan takaici da bakin ciki, cikinta ya hautsine, kirjinta ya kama zafi don bakin ciki, ta rike cikin tana murkususu tana kuka. Shi kam ya riga ya fice bai ma san abin dake faruwa da ita ba. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Can ya ji amai ya taso mata, ta yunkura ta mike da gudu ta nufi tsakar gidan, kafin ta isa ga rariya tuni aman ya cimmata, ta tsuguna a nan ta fara kelashi tana dafe ciki da kirji kamar zai biyo hanjinta ya fito waje take ji. Ya shigo dauke da maganin sauro da ya je siyowa ya hangota durkushe tana amai, ya kidime ya nufe ta da sauri yana tambayarta abin da ya faru. "Yaya aka ma'u? Me ya same ki, lafiya?" Duk ya rikice ya rude. Bata iya ce masa komai ba saboda aman da take yi, ya mike ya nufi rubar ruwa ya debo ruwa cikin buta ya nufeta ya fara zuba mata a kanta, don ta jigata da aman tana ta kakari babu komai a cikinta domin ta amayar da dukkan wani abu da ta ci wanda bai narke ba. Ya dinga wanke mata fuska da jikinta har sai DA ya tabbatar ta koma cikin hayyacinta ya kama rigar jikinta ya cire domin duk ta baci sannan ya tallafe ta suka nufi daki ya zaunar da ita gefen gado ya cire mata sauran kayan jikinta ya dauko wata doguwar riga ta bacci mara nauyi ya sanya mata sannan ya kama ta ya kwantar akan filo yana fadin "sannu ma'u meye yake miki ciwo kuma yanzu? Ta kada kai muryarta a dashe tana fadin "babu komai sai dai tashin zuciya kadan-kadan" "Zai daina shima, garin yaya kika fara aman ne? Ta rintse ido "ban sani ba ni ma" yayi shiru yana kallonta DA tausayawa sai ya mike tsaye. "Bari na samo miki magani a chemist din sister Deeja" ya fice da sauri. Ita kuma yana fita taji wani sanyi na shigarta, ta janyo bargon dake gefe ta kudundune. Ya dawo dauke da magunguna ya ajiye ya dauko ruwa ya bude abinda ta lulluba fashi ya tallafo kanta yana fadin "ma'u tashi ki sha magani" Bata yi musu ba ta amsa ya fara sha har ta shanye duka ya maidata ya kwantar ya mike ya fara fita da kayan ita kuwa ta kara kudundunewa domin har lokacin akwai zazzabi a jikinta. Yana can yana kokarin dauraye kayan da ta bata ya kuma jiyo kakarin amanta, ya bazamo dakin da gudu ya sameta tana durkushe a gaban gado ta amayar fa dukkan magungunan da ta sha. Ya dafe kai da damuwa kamar zai fasa ihu, ya isa dai ya gyara gurin ya dauko kaya ya jibga akan wadancan na wajen ya dawo ya dauko dan ruwa yana bawa matar tashi, ya fasa wanke kayan ma ya rungume ta a kirjinshi yana shafa kanta da lallashi, duk ya dauki laifin wannan cutar ya dorawa kansa, domin da bai yi mata masifar nan ba da ba zata yi aman har haka ba, da zai iya ma da ya janye dukkan maganganun da ya gaya mata, amman ba zai iyu ba saboda magana zarar bunu ce, in ta fito bata komawa. Haka nan suka kwana tana ta aman, tayi ya kai sau hudu cikin dare, don haka tun da asuba ya fara shirin kai ta asibiti. Karfe bakwai sun fice. Ya so kaita na kudi amman kuma babu kudi a hannunsa domin wata ya fara nisa, don haka na Murtala Muhammad ya kaita. Da yake sun fita da wuri sun yi sa'ar ganin likita da wuri, aka rubuta musu magunguna har da karin ruwa da kuma gwajin fitsari. Har wajen karfe uku suna asibitin sai da ruwan ya kare tas. Sai dai har a sannan Ahamd bai san abindake damun matar sa ba, don haka da za su tafi ya sami wata ma'aikaciyar jinya ya mika mata korafi yana fadin "sister don ALLAH meke damunta ne, dazu ina rude ban tambayi likita ba, ga shi ya tashi yanzu" Ma'aikaciyar jinya tayi kamar ha zata amsa ba, da tayi ido hudu da ahmad sai ta gaza yin musu, domin shi mutum ne mai kwarjini da haiba, da wuya ka kalli tsakiyar idonsa kayi masa musu. Bayan ta gama karanta abindake rubuce a jikin katin ta kalli ma'u tana rariya tana fadin "ina taya ki murna kin kusa zama mama" Sam ma'u bata fahimci komai ba. Ahmad ya dan fahimta, amma duk da haka sai ya sake kallon ma'aikaciyar jinyar da sauri "sister kina nufin wai ciki ne da ita"? Ma'aikaciyar jinyar tayi murmushi tace "ka cire kalmar wai" ta mika masa katin tana murmushi. Tace "ALLAH ya raba lafiya" Ma'u kam kunya duk ta kama ta kamar ta nutse a gurin, ta kau da kanta gefe daya tana