Sashe 26
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wayar ba a lokacin don haka ya tura mata sakon lallashi. Sai da nana ta bata kusan awanni biyu sannan ta iso, dama ya gaji da jiranta, amma dai ba zai iya tafiya ya barta ba ta shigo da sauri tana fadin "tuba nake yi na yi zaton ma ka tafi" Ya mike DA sauri yana fadin "ni na isa na tafi na bar hajiya" "Na gaya maka ka daina ce min hajiya ko Ahmad? Bari dai na dinga ce maka Alhaji kaima, hajiya sai kace wata tsohuwa" Yayi murmushi 'ni ban je ko airport ba ya sunan Alhaji zai hau kaina? Wuce mu je" ya nuna hanyar fita daga ofis din DA dan yatsansa. Ta wuce suka fice har suka isa gurin motar tashi. Wannan shine karo na farko da nana ta taba shiga motar ahmad, ko lekawa ma bata taba yi ba sai yau. Sai da suka yi 'yar rigima kafin ya yarda ya zauna a kusa da shi, cewa yayi dole sai dai ta koma baya, ita kuma tace bata yarda ba ai shi ba direbanta bane. Hankalinta ya kai kan wani hoto dake sakale a jikin madubin dake cikin motar yana dan lilo, bayan sun shiga. Dan karami ne hoton an sanya shi cikin wata 'yar kwalba tana lilo. 'Ya'yansa ne a jiki sun yi kyau dukkansu a tsaye suke. Rike da kugu Sayyada kenan, an raba mata gashinta gida biyu, hajiya tana gefe ita ma taci kwalliya ga malam a tsakiyarsu shi ma cikin kananun kaya har da hular sojoji akan sa, yaran sun yi matukar kyau a hoton. Nana ta kalle shi DA sauri sanda ya tada motar suka nufi fita daga kamfanin tace "wadannan yaran fa ahmad?" Ya kalli hoton yayi murmushi, daidai lokacin DA suka fita daga cikin kamfanin yace "yarana ne" Yaranka? Nana ta tambaya da mamaki. Iyakacin ganin da take wa ahmad da saninsa bata taba zaton yana da aure ba ma balle har da yara uku. Mamakinta ya kasa boyuwa har ya gane yace "sun yi kadan ko? Da sauri tace "yara ukun ne sun yi kadan? Ban taba zaton kana da aure ba ma balle yara, don baka yi kama da mai aure ba sam" Yayi dariya da jin dadi yace "akwai wani da yake nuna mutum yana da aure ko bai da shi daman? Ta kwanta jikin kujerar motar jikinta yayi dan sanyi tace "no, ba haka ba ne. Amma wani lokacin zaka ga masu aure kamar suna cikin damuwa DA matsala ne, amman kai ban tana ganin ko daya tattare da kai ba" Ya sha kwana yana murmushi yace "dukkan mai halin da kika ganshi cikin irin halin da kika bayyana to ya jahilci auren ko sam bai yi sa'a da mace ya gari ba, ni kam ina alfahari da matata, duk da kasancewar Ma'u yarinya ce amma bata rage ni da komai ba, ina samun dukkan abun DA nake bukata daga gurinta, bani da damuwa ko matsala sam cikin aurena" Tayi shiru tana tunani har sai da ya kalle ta yace "yaya dai hajiya, ban san inda muka dosa ba fa" tayi ajiyar zuciya "kana so dai muyi rigima da kai in dai baka daina ce min hajiyar nan ba, ka Kai ni shoprite ina so zan yi siyayya" duk da hankalinsa yana gun zuwa gida amma ba zai ki yin abun da nana ta sanya shi ba, ya juya kan motarshi suka wuce can. Suna tafiya suna yin hira jefi-jefi tana tambayarshi yaran nasa. Abin da yafi komai yi mada dadi kenan don haka ya saki jiki suka dinga hirarsu har suka isa shoprite din. Irin siyayyar da nana ta dinga yi ta baiwa ahmad mamaki kwarai, yarinyar bata jin kudi, hankalinsa bai tashi ba sai da aka je biyan kudi ya gama rikicewa, siyayyar ba wata mai yawa bace amma sai makudan kudi, babu wani ko dar ta fito da ATM card dinta ta mika aka sanya cikin P.O.S. aka fara diban kudin har aka gama aka ciro mata ATM card dinta aka mika mata. Ta kalli Ahmad tace "Ina ta rokomka ka dauku wani Abu ka ki ko? Ina fatan zaka amshi agogon da na siya maka?" Yayi murmushi bai ce komai ba suka nufi hanyar fita, masu daukar kaya na biye da su da manyan jakankuna. Bai gama tsinkewa da lamarin alhaji nura kwangila da iyalansa ba sai da ya isa gidansa. Ya san alhaji nura kwangila yana da kudi, amma bai yi tsammanin ya mallaki gida kamar wannan cikin GRA unguwar masu kudi haka ba. Sai da suka yi doguwar tafiya sannan suka iso ainahin gidan. Motarsa tana tsayuwa ma'aikata kamar guda uku suka fito daga cikin gidan mata don Nana tayi musu waya dama. Ahmad ya bude motar da sauri ya fice ya bude bayan motar ya fara fito da kayan. Nana tace"tsaya ai ba duka ne kayana ba" Ta dauki leda guda uku ta mikawa masu aikin sannan ledojin wajen guda hudu cikin motar suka rage a cikin but din motar. Ahmad ya kalleta da sauri cikin mamaki yace"wadannan kuma fa?" Tayi murmushi "na yarana ne, leda biyu na takwarata Sayyada, daya na malam daya na Hajiya."kafin yayi magana ta fito da agogo cikin jakarta tace "wannan kuma na baban yaran ne" Ya kura mata ido da mamaki, domin ya ga yawan kudin da ta sayi agogon. Ya kada kai yace "Nana wannan bai dace da ni ba, yafi dacewa da mutane masu kudi, ki barshi na gode zan kaiwa yaran naki..." Ta bata fuska kwarai da gaske. "Bana son nayiwa mutum kyauta ya ki karba, shine abinda yafi bata min rai. Kafi karfin komai a gurina Ahmad, kuma ba rokona kayi ba." Ya mika hannu ya amsa ganin yadda ranta ya baci yace "na gode ALLAH ya saka da alheri, bari na wuce naga magariba ta kawo jiki" Ya juya ya nufi motarsa. Ita kuma ta wuce cikin gidan da sauri tana murmushi, duk da akwai faduwar gaba a tattare da ita. Ahmad yana isa unguwarsu aka fara kiran sallar magriba, don haka ya tsaya a wani masallaci yayi sallah sannan ya karasa gida. Ma'u tana falo tayi wanka tayi kwalliya cikin wata atamfa da tayiwa dinkin doguwar riga amman ya kama jikinta daurin ma ya kama jikinta. Ma'u ba tayi ilimi mai zurfi ba sannan bata yi mu'amala da mutane ba, amman yawan karance-karance da kallo ya sanya ta waye da yawa, babu irin littafin da bata karantawa daga Hausa har zuwa novels na turanci. Sannan tana kokarin tafiya da zamani, musamman yanzu da mijinta ya samu rufin asiri, shima da yake ma'abocin siyo mata dukkan wani abu na bukata da zai amshi jikinta ko ya burge shi ne. Ya shigo da sallama dauke da kaya a hannunsa, ta dora kafa daya kan daya ta amsa ba tare da ta kalle shi ba. Ya isa gabanta ya ajiye kayan sannan ya kama Kunnuwansa irin yanda yara suke yi idan sun yi laifi. Ta kalle shi dariya ta kubce mata ta sanya hannu ta tureshi ya fadi da bayansa ya kwanta, amman sai da ya janyota da hannunsa ta fada kansa ta fara kokarin kwacewa. "Ka sake ni ka iya yiwa mutum laifi sannan ka komo kana yi masa wayo. Yanzu ka tafi ofis tun safe sai Yanzu ka dawo bayan ranar da ya dace ka zauna tare da nice." "Kin san ba zan yi dukkan abunda zai bata miki rai da gangan ba ma'u, aiki ne ya rike ni kiyi hakuri, kin hakura?" Ta kwanta kawai a kirjinsa tace "Ina son na hakura amman bana son baka damar maimaita irin hakan nan gaba" "Na zan kara ba, kin yarda? Ta daga kai alamar eh, har lokacin tana kwance a jikinsa. "Wai me ka siyo ne? Ta zame daga jikinsa ta mike ta nufi ledojin, gabansa ya fara faduwa ya mike zaune da sauri, don bai san me zai biyo bayan ganin da zatayi ba, sai dai ya kudurce a ransa zai yi mata karya yau sau daya, don neman zaman lafiya a gidansa. Ta fara duba kayan, da farko ta dan fara murna, sai da ta nutsa cikin kallon kayan mamaki ya fara bayyana akan fuskarta, domin kowanne akwai kudinshi a jikinshi, a ranta tana lissafin kudaden sai ta fara sakin baki. "Yaya ina ka samu kudin siyan wadannan kaya masu yawa haka?" Gabansa ya kara faduwa ya isa gabanta da sauri yana yake yace "Wai kina nufin bani da kudin da zan iya siyan wadannan kayan?" Ta kalle shi da mamaki tace "Yaya an sauya ma albashi ne ko kuma wata sana'ar ka samu, don a yanda naga kudin nan na jikin rigunan nan sun fi karfin albashinka na wata uku ma" Yayi yake yace "Nana ce ta siya musu fa..." Bai san sanda bakinsa ya furta wannan kalmat ba. Ma'u ta kalle shi da tarin fargaba, daidai lokacin da ta janye hannunta daga kan kayan bakinta na rawa, wani irin tashin hankali ya dinga shigarta. Ya kula da yanayin da ta shiga, amma ya dake yana son basar da bacin ran nata yace "ni kaina nayi mamakin siyayyar da ta bada, daga ganin hotunan yara jikin mota suka bata sha'awa sai ga siyayya wai tasu ce' Ma'u ta mike tsam daga gurin kayan bata kuma cewa komai ba nufi hanyar dakin baccinta. Ya bita da kallo da mamaki kafin ya fara kiran sunanta. "Ma'u! Ma'u!! Meye haka, meke faruwa ne?" Ya isa da sauri ya sha gabanta da tsananin mamaki yana fadin "wai meye haka ne ma'u, kayan ne ya bata miki rai? To kin ga dakata bana son damuwarki sai na dauki kayanta na mai da mata faqat!" Ta ja ta tsaya. "Aikin banza kenan, kuma ta baya ta rago! Meye kuma matsayinta a gurinka ka jima kana raina min hankali akan wannan matar yaya, yau dai ALLAH ya toni asirinka, ko baka san naji lokacin da tayi ma waya tunda safe bane, ka fita gurinta kuka yi ta yawo har wannan lokacin sannan ka dawo ka gaya min maganar banza... Na gaji da wannan yaudarar taka, na gaji..." Ta fashe da kuka, hankalin Ahmad ya tashi ransa ya baci, ya kalleta da muzurai yana fadin "ni nake yaudarar ki ma'u me zan