Sashe 10
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ba a san asalin barbela ba sai tace daga madina take" "Oho! Ko ma dai meye ai ya fi masu yawo a kwararo an rasa mai tayi balle tayi daraja, 'ya'yan bakin uwa da uba kawai" tana fadin haka tayi waje da sauri. Amina ta kara fusata tayi kofar da sauri, lami ta yi hanzarin rikota tana tirjewa da bakin ciki, "ki sake ni don ALLAH lami, yau sai na cu uwar yarinyar nan a gaban uwar tata" "Amina kada ki jawo min bala'i ko a baya da kuke yi ma ba ki taba samun nasara ba balle yanzu da ta zama DIYAR GATA ki barta zamu rama cikin ruwan sanyi muddin kere na yawo zabo na yawo wata rana dole za a hadu" Amina ta koma ta zauna tana huci, ba don ta hakura ba sai dai ta tabbatar zata rama wata rana. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Umma da malam suna ta zolayar Ma'u da ahmad da suke ta hada kayansu, suka fice suna dariya. Shatar mota taxi suka dauka har zuwa kofar gidansu. Gidan yayi fututu cike da tsananin kura kamar an yi shekara ba a shiga cikinsa ba, don ma ma'un takan zo duk karshen wata ta gyara shi, ummanta ce ke sanyata yin hakan. Ma'u ta cire gyalenta ta sakale shi a jikin igiya ta fara karewa gidan kallo tana tunanin ta ina ya dace ta fara gyaran ne. Ahmad ya bita da kallo tunda ya dawo yake mamakin irin girma da cikar da ma'un tayi, sai kace yayi shekara rabon shi da ita kamar ha ma'unsa ba. Kamar ance ta kalli inda yake ta juya tana fadin "yaya ta ina zan fara ne...? Ta kasa karasa maganar ganin irin kallon da yake yi mata. Ta dauke kanta da sauri, domin ya zuwa yanzu ta sana ma'anar kowanne irin kallo, domin tabkaranta a littafin Nafisa Lili 'Yar Nijar ta fayyace kowanne irin nau'in kallo. Shi ma ya dan ji kunya, amma sai ya dake yace "wannan aiki ya fi karginki kr kadai Ma'u, dole sai na taimaka miki, bari ki gani" sai ya fara kokarin cire kayansa shi ma yana ajiyewa a kan igiya, ya rage daga shi sai gajeren wando da singileti. Ta kalle shi da mamaki yaushe rabon da ta ga yayan nata a haka, duk jikinsa ko ina gashi kwance lublub, gabanta ya yanke ya fadi, domin har ta gama fayyace surar mijinta, domin ta gani a littafin Lili mai suna MU SAN KANMU MAZA DA MATA kuma da alama mijinta yana daga cikin maza masu kirar zaki ne. Bai kula da yadda take kallonsa ba ya fara aikinsa. Ta sanya hannu suka ci gaba da yi tare. Sai wajen karfe hudu sannan gidan ya dawo hayyacinsa yadda suke bukata, sun yi butu-butu da kura. Shi ya fara shiga bandaki yayi wanka bayan ya fito ya sanya kayan DA ya bari a kan igiya, ya fice domin yaje ya siyo musu _Take Away_ saboda yamma tayi babu damar yin girki yanzu. Yana fita ita ma Ma'u ta fada wanka, bayan ta fito ne ta fara gyara jikinta da turare masu kamshi, domin umma wannan karon bata yi sanya gurin hada mata kayan kamshi da gyaran jiki ba. Wata kila ta fahimci har lokacin ma'un budurwa ce ita. Kafin kace meye wannan tuni gidan ya dauki wani irin kamshi dadi da tsananin sanyaya zuciya. Ta fara duba kayan DA yayan nata ya kawo mata tsaraba, dukkan su kananan kaya ne sai kuma rigunan bacci, sai kuma kayan gyaran gashi da mayuka kala-kala, komai mai kyau me ta san yayan nata Dan gayu ne. Amma bata yi tsammanin ya iya zabe kamar haka ba sai yanzu da idanunta suka gane mata. Ta ma rasa wanne kaya ya kamata ta sanya daga cikin kayan DA yayan nata ya kawo mata tsarabarsu, domin kowanne a cikinsu yana da tsananin kyau. Daga karshe dai ruwan idonta ya kare a kan wani dogon siket mai roba, da alama idan aka sanya shi zai kama mutum, zai kama jiki sosai. Rigarsa kuma mai kama jiki ce kwarai da gaske, ruwan hoda ce sai dai akwai zanen fulawoyi ruwan golden a jikinsu. Ko da ta saka kayan sun anshe ta kwarai da gaske. Kitson kanta shuku ne don haka ya dace da kwalliyarta, kasancewar tana da gashi tayi dauri da wani gyale, kitsonta ya fito ta tsakiya ya sauka a bayanta. Ta sanya wani dogon dankunne wanda shi ma yana cikin kayan da yayanta ya kawo mata a cikin tsaraba. Bayan ta gama tsantsara kwalliyarta ta koma falo ta hakimce tana kallonta, domin an kawo wutar nepa a lokacin. Sai bayan sallar magriba ahmad ya shigo gidan, domin ya biya ta gurin abokinsa Ishaq sun gaisa sannan yayi yan biye-biyensa dai. Bata damu ba bayan kallo da take yi 'yan matan unguwar su A'ilo suna ta shigowa suna gaisawa da murnar dawowarsu. Kai tsaye falonsu ya nufa domin can ya jiyo motsinta. Bai fita da babur dinsa ba Domin ya san shi ma yana bukatar gyara sai washe gari zai kai shi a duba shi tukunna. Haka ya sanya Ma'u bata san ya dawo ba sai da ya shigo da sallamarsa. Ta dago kanta da Sauri ta kalleta shi. Sai ta mike daga zaunen da take ta nufe shi tana fadin "sannu da zuwa yayana" ta amshi kayan dake hannunsa ta nufi cikin faki domin ta ajiye. Ahmad ya bita DA kallo komai a jikinta juyawa yake yi. Ya bude baki sai kace wani sauna. _Anya kuwa wannan ma'unsa ce ba sauya masa ita aka yi ba?_ Bata san yana yi ba har ya isa ya zauna duk jikinsa yayi sanyi, abinda yake ji game da ita ya dinga dawo masa, ko a can legas yayi fama da irin wannan matsalar, sai dai ya dinga dagewa da yawan addu'a don kada shaidan yayi galaba a kansa. Komai na ma'u ya sauya cikin dan wannan lokaci. Koda yake tun kafin ya tafi ya fara fuskantar wasu 'yan sauye-sauye a tare da ita, amman ba su kai na yanzun ba. Ta mike ta nufi kicin ya dauko babban faranti ta juye musu abincin da yayo musu take away dinsa ta kawo gabanshi ta ajiye. "Yaya sauko mu ci abinci, ni fa yunwa nake ji" ya sauko yana fadin "nima haka, amman dai a baki zaki bari ni ko 'yar matata? Tayi dariya ta kau da kai, kunya ta rufe ta a zuciyarta cewa tayi "me zai hana na baka na gwada yanda Alhaji Bashir ya yiwa Fauziyya akanka ta cikin littafin SAWUN GIWA" Amma a fili ba zata iya ba, yayi murmushi ya fara cin abincinsa ya dinga janta da hira yana ba ta labarin abincin ikko, ita ma tana bashi labarin abubuwan da suka faru, wani yayi dariya wani ya bata fuska, a hakahar suka kammala cin abincin. Dukkan hankalin ahmad yana kan Ma'u a yau dai yake jin fauriyarsa zata kare, idan bai isa ga matarsa ba komai zai iya faruwa a gare shi. Ita kanta ma'un tana jin wani abu yana yawo akanta duk lokacin. Da ta kalli mijin nata. Domin ta cika tayi dankam babu wata damuwa ko ta kwabo a ranta, amman kowa ya rasa yanda zai iya tunkarar dan uwansa. Ma'un ce ta fara duguwa dakin baccinsu ta sanya kayanta, don akwai rigunan bacci kala-kala don haka a ciki ta zabe wata mai kyau ta sanya, duk da dukkan rigunan ana hango komai na mutum idan ya sanya, ita kuma ba zata iya yarda yayanta ya ganta a haka ba, don haka ta haye gado ta kudundune cikin bargo. Shi ma bai wani jima a falon ba ya biyo bayanta, sai ya tadda ta a gado a kudundune, ya isa kusa da ita ya zauna a gefen gadon yana fadin "Ma'u sanyi kike ji ne haka? Kin ga bude na gayanda rigar tayi miki kyau, duk kayan da basu yi miki kyau ba sauya su za a yi" Ta kunshe kai tace "tayi min kyau ma yaya" "A'a sai na gani da idona, bari na gani" ya fara kokarin janye bargon tana rikewa da 'yar kissa, amman sai da ya cire ya zubawa halittar matarsa ido. _wai da gaske daman haka ma'unsa take?_ Ta kara kudundunewa zuciyarta na cigaba da bugawa. Tabbas yau zai abibda take karantawa a cikin littafi zai faru a kanta, duk da bata san a wanne haki yake ba shi mijin nata. Jikinta ya bata cewa ya kura mata ido ne, don haka ta kara matse jikinta gabanta yana ci gaba DA faduwa. Yayi wata doguwar ajiyar zuciya ya mike tsaye yace "taso Ma'u" Tayi shiru bata yi magana ba kuma bata motsa ba, har ya dan juya ya fara tafiya amman sai ya sake waigowa yace "Ma'u kina jina fa, daure tashi kiyo alwala, zan gaya miki abinda zaki yi idan kinyo alwalar" Ta yunkura kamar kifanya har lokacin jikinta yana nannade ta rike zanin gadon, yana kallonta kada kai yayi murmushi ya fice. Tayi ajiyar zuciya bayan ta hango inuwarsa ya gama ficewa ta dafe kunci, ta kara mai da hannunta ga kirjinta da yake ta bugawa, tayi dan murmushi sannan ta mike ta fito. Yana tsakar gidan kusa da bandaki yana daura alwala. Ta rakube tana jiran ya kammala, yayi kamar bai ganta ba yana ganawa sai ya shige falo, sai ta nufi bandakin ta shiga. Ta jima a tsakar gidan bayan ta kammala alwalar gabanta yana faduwa ya kasa shiga dakin. Ta jima tana sakawa da kwancewa. Kukan wata mage da ta zo wucewa ne ya bata tsoro sai ta shige dakin da sauri Yana zaune a kan sallaya ya tankwashe kafafunsa yayi shiru, amma bakinsa yana dan motsi alamar lazimi yake yi. Ta isa kusa DA shi ta tsaya daga bayansa, yaji alamun shigowarta don haka ya mike da kansa ya dauko hijabin sallarta ya mika mata ba tare da ya kalle ta ba yace "sallah zamu yi raka'a biyu Ma'u" ya shige ba yana kokarin tayar da sallar, ta bi shi a baya ta tayar. Bai ja dogayen surori ba yayi sallama ya juyo ya