Sashe 24
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ahmad da kyakkyawan saurayi. Sai ta lumshe ido a cikin zuciyarta tana fadin "to wai me ya sanya ta damu da tuna shi ne ma? Bata da amsar da zata bai wa zuciyarta. A haka tana tunanin har tayi bacci, a cikin barcin nata na wannan dare sai da tayi mafarkin Ahmad. Da sassafe ta fara shirin tafiya aiki inda take yi a karkashin kamfanin mahaifinta amman zuciyarta fal da tunanin ahmad. Sai ta tsinci kanta da sanya kaya masu matukar kyau, ta san ba don ta burge ahmad ba ne, amman zata so ya ganta cikin shiga mai kyau. A haka ta wuce ofis. Karfe goma na safe ta janyo ofis dinta ta rufe ta nufi motarta ta shiga ya tasheta ta fice daga kamfanin. Kai tsaye gidan man su Ahmad ta nufa. Motar da ta hau yau ba irin ta rannan bace, don ita NANA FOUR ce don haka har ta isa inda yake bai kula da ita ce ba. Cikin sa'a kuma yau gidan man nasu babu layi. Yana tsaye har ta ISO gab da shi ta bude motarta ta fito, bai ganeta ba sai dai yaga kamar ya Santa, domin rannan da bakin gilas ta iso gurin nasu, yau kuma babu. Ya kau da kansa da sauri daga kallonta domin ba dabi'arsa bace kallon mata. Ta isa kusa DA shi ta tsaya tace "ina fatan za a zuba min man ko? Ya kalle ta DA sauri yana son tuno inda ya santa. Tayi murmushi har fararen hakoranta suka bayyana tace "sunana NANA ASMA'U" sai a lokacin ya gano ta, yayi yake saboda jin sunan, yakan girmama dukkan macen dake da wannan sunan a duniya. Yace "Hajiya barka da war haka. Na nawa za a zuba miki" Mamaki ya kara kamata don tunda take zuwa gidan man mahaifinta bata taba bayar da kudi ba, amman yau gashi ana tambayarta na nawa za a bata, koda yake ta riga ta gano waye ahmad, kaifi daya ne don haka tace "ka cika min tankin sai mu ga na nawa ne" Bai ce komai ba ya nufi tankin motarta ya fara zuba mata. Ta dinga satar kallonsa, ta jima bata ga namijin da yake burgeta kamar ahmad ba, har ya kammala cika mata tankin motar da mai ya iso inda take tsaye yace "Hajiya na dubu hudu da dari biyu ne" Bata yi musu ba ta leka motar ta dauko wata hadaddiyar jakata kirgo dubu biyar ta bashi. Ya amsa ya fara kokarin ciro mata canjin, amma tuni ta shiga motarta. Ya matsa da sauri yana fadin "Hajiya ga canjinki fa" "Ka zuba man sauran canjin a cikin babur dinka don na kula baka shan man cuta" ta bawa motarta wuta ta fice a guje. Ahmad yabi motar da kallo cike DA mamaki kwarai DA gaske. Jazuli yana kallon dukkan abinda yake faruwa ya dan matso yana fadin "ya aka yi ne dai abokina, kun shirya da mutuniyar taka kenan? Ahmad yayi murmushi kawai bai ce komai ba, amman a ranshi ya ji da ya sani bai yi mata abinda yayi mata ba a baya. Macen da take dauke da wannan suna mai daraja bata cancanci wulakanci ba. Asma'u mahaifiyarshi, diyarshi kuma matarshi abar kaunarshi. Ya kada kai ya koma ya cigaba da abinda ke gabansa. Duk ranar ALLAH sai nana tazo gidan man nan ta sha mai a gurin ahmad, tun bai sakar mata fuska har suka fara sabawa don ya gano tana da matukar kirki yanzu. Ita ma ta gano ahmad din ba miskili bane sabanin yanda take zato a da. Yau da dare suna cin abinci ita da babanta da mamanta ta kalli baban nata tace "daddy wai wannan ahmad din bai da ilimi ne, yanayinsa da mu'amalarsa sun nuna kamar yana da ilimi" Alhaji Nura kwangila yayi murmushi "ni kaina na fara tunanin wani abu a kansa, yaron nan yana da gaskiya da rikon amana, ban taba jin ance wani abu ya bata a hannunsa ba, abinda ya faru tsakaninki da shi ya kara bashi matsayi mai girma a raina, don irinsu basu hada kai da kowaye gurin cuta ko ha'inci, fatana dai ALLAH ya sanya iliminsa ya dan yi zurfi ko yaya ne" Nana tayi murmushi tace "gaskiya kam ya kamata ka gwada shi, wata kila yayi maka yanda kake bukata. Musamman yanda muke da bukatar karin ma'aikata a kamfani, irinsu muke so" Hajiya Batula tace "ba dai wai yaron nan abokin fadanta take magana a kansa ba? Nana tayi murmushi, shima Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yace "shi mana, yanzu kam sun fahimci juna, shi ne babban customer dinta" Nana ta fashe da dariya tace "ka ji daddy sai kace wani dan kasuwa" Haka suka cigaba da hirar su cikin walwala da jin dadi. Washe gari DA yamma ahmad yana tsakiyar zuzzuba mai manaja Saddam ya iso gurinshi yace "Ahmad kasan kamfanin Alhaji Nura Kwangila inda office dinsa da na diyarsa yake?" Ahmad yayi jim sannan yace "ina zaton na taba zuwa sau daya, shine na can cikin sharada phase II ko? Manaja yace "good, nan fa gobe can zaka wuce Alhaji yana son ganinka, amma idan zaka wuce ka tafi da takardunka na makaranta domin ina jin interview za a yi na daukar ma'aikata a kamfanin nasa, wata kila kana da rabo a ciki" Ahmad ya bude baki da mamaki don abinda ya jima yana nema ke nan sai gashi Yau ya same shi a ruwan sanyi. Manaja Saddam ya dafa kafadarsa yana bugawa "kana cikin mutane masu sa'a, har naji a jikina kana da rabo a wannan kamfanin" Ahmad ya kada kai yace "na gode ranka ya dade" Tun dare ya sanar da Ma'u abinda ke faruwa, don haka bata kwanta bacci ba sai da ta goge masa kayan da zai fita da su sannan cikin dare ta tashi tayi sallah ta dinga rikon ALLAH da yi masa magiya akan samun aikin mijinta irin wanda ya jima yana nema. Da sassafe ta kammala shirya masa dukkan abinda yake bukata, ya riga su fita tana zolayarshi da cewa "mijina ka hadu fa, kada ka yarda kowacce mace ya kwace min kai kaji ko?" Ya kada kai yace "nima ba zan kallesu ba" suka rabu da farin ciki. Sanda ya isa kofar kamfanin mamaki ya cika shi ganin ganin gurin cike da mutane kowa da doguwar anbulan alamar sun zo interview ne suma. Ya dinga kallon mutanen dake kan layi yana tunanin sanda layi zai zo kansa har ya shiga. Yana nan tsaye wata hadaddiyar mota ta iso gurin ya nufi kofar shiga kai tsaye tana horn yabi motar da kallo, motar ta iso bakin kofar ta tsaya tayi horn sannan sai bakin glass din gaba ya fara sauka a hankali. Mamaki ya cika shi da ya hango nana, cikin murmushi nana ta yafito shi da hannu, ya nufe ta DA sauri yana fadin "Hajiya barka da zuwa" Ta amsa gami da cewar "bude motar mu shiga mana don naga akwai layi ko na interview ka zo ba? Da sauri yace "Eh ita na zo, na gode Hajiya" ya zagaya ya bude ya shiga suka shige ciki. Gurin da ake saukar baki ta zaunar da shi, akwai mutane DA yawa a gurin wadanda suka zo interview din, shi ma ya zauna yana ta addu'a a cikin ranshi. Bayan fitowar mutum biyu aka kira sunanshi, ya mike da sauri da addu'a a bakinsa ya shiga. Abin mamaki Nana ce da wasu mutane su shidda suke yin interview din. Bata nuna masa wata alama ta sanayya ba don haka shima bai nuna ya santa ba yayi dukkan abinda ya dace, suka amshi takardunsa suna dubawa suka yi masa tambayoyi. Nana ce mai rubutu bisa laptop, sanda takardun Ahmad suka shiga hannunta ta cika da matukar mamaki, don ganin har digiri yayi, kuma j ami'a mai tsada kamar B.U.K. sannan ya karanta karatu mai kyau. Ta kalle shi ta kada kai kawai, yayi irin wannan karatu haka mai zurfi da nasara ai bai kamata ya kare a gidan mai a matsayin mai dura mai ba, yafi dacewa da aikin ofis fiye da dura mai a mota. Har aka kammala komai ya koma, kwanaki biyu yana zuwa gidan manshi yana sane da interview din da yayi, amman bai sanya rai ba don yadda nana ta sha kunu ya dan damu yana zaton ko zata rama abinda ya taba yi mata ne. Gashi tun daga ranar bata kara shigowa gidan man nasu ba sam. Wannan ya sanya gwiwarsa tayi dan sanyi, sai dai a rana ta uku yaji sako ya shigo cikin wayarshi, bai damu da dubawa ba don lokacin yana tsaka da aiki, sai da ya gama komai ya koma gida ya kwanta ma sannan ya dauko wayarshi ya fara dan duddubawa, sai yaga sakon daukarshi aiki, kuma yaga daukarshi din ta fara aiki nan take. Yayi wata doguwar kabbara da ta tashi Ma'u daga bacci ta kalle shi da mamaki tace "lafiya kuwa yaya? Ya janyo ya jikinsa ya kankame sai ta kama dariya domin tasan haka mijin nata ke nuna murnarsa ta kuma san abinda yake jira bai wuce samun aikin da yayi interview ba. Kusan kwana suka yi murna, ranar ma da sassafe ta shiryashi ya fice. *** SABUWAR RAYUWA Ga mamakinsa sai yaji wai nana ce D.G ta kamfanin gaba daya, shi kuma ya sami mukamin mataimakin manaja, wato daga ita sai wani sai shi da kuma albashi mai matukar tsoka da katon office shi daya. Bai taba mafarkin wannnan ba cikin rayuwarsa. Manaja ne ya dinga yawo da shi yana nuna masa komai da ko ina. Cikin bayanin nasa yake gaya masa cewa wannan shine kamfanin Alhaji Nura Kwangila na farko wanda ya fara yin man gyada da kayan abinci, kowanne bangare akwai shugabansa, wanda bunkasarsa ce sanadiyyar arzukun Alhaji Nura Kwangila har ya kakkafa gidajen mai DA sauran abubuwan da yake yi na neman kudi da juyasu. Bayan ahmad ya dawo office dinsa yayi shiru yana karewa office din kallo, wai yau shine a nan a matsayin mafi kololuwar dukkan shugabannin sashen mai da kayan abinci da sauransu da kuma ma'aikata kusan dari a karkashinsa suke, wacce irin godiya zai yiwa UBANGIJINSA NE? Aka turo kofar office din aka shigo, nana ce