Sashe 33
Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin ranta tana son kuma ta Kira shi a waya amman tana tsoron yanda zai amsheta ko kuma kada ta Kira yana tare da Ma'un tashi ta bata masa rai. Kwanaki suka dinga tafiya kowa abunda ke damunsa ransa na ci gaba da girma. Ga Ahmad da matarsa ma'u sun kwantar da hankalinsu, domin yace mata yana tsumayin takardar sallama ne, sannan zai fara nema musu gidan haya, sai ya sanar da Musa ya bashi ko Shekara daya ne ya samu inda zai koma shima. Wannan labarin ya mata dadi a zahiri, amman a badini tana damuwar irin sana'ar da mijinta kuma zai yi a nan gaba, tana tsoron kada su koma cikin matsala, musamman yanda yake taimakonta da iyayenta da 'ya'yanta, tana son ta saduda amma kuma kishi ya hana ta yin hakan. Ga Alhaji Nura Kwangila ya rasa me ya dace yayi, dukkan al'amuransa sun tsaya cak, yana son zuwa yaga yayansa da mahaifiyarsa ma amma abun ya faskara don dama duk bayan watanni shidda yake zuwa gashi lokaci yayi yana fargaba, babu Wanda ya san abun da yake ransa sai shi daya. Daga karshe dai mai dakinshi ta tare shi a daki don jin gaskiyar abun dake faruwa, bai boye mata duk yanda suka yi da Ahmad ba. Ita ma ta shiga tsananin damuwa da tsorata har ta rasa abun cewa, don ta san idan Nana taji wannan labari komai zai iya faruwa. Alhaji Nura Kwangila ya kurawa Hajiya Batula ido yana fadin "wannan shine halin da nake ciki, ban iya bin malaman tsubbu ba balle nace zan bi su dawo min da hankalin yaron nan kan Nana ba, sannan ba zan iya siyan shi da dumbin dukiyata ba, yaya zan yi yanzu? Tayi shiru tana kada kai sannan tace "shi Ahmad din bai da iyaye ne? Ya kalle ta da sauri sannan yace "abunda ban sani ba kenan, amman ina zaton iyayensa suna nan da ransu don na taba jin yana maganarsu tun lokacin da ya taba zuwa lagos sai dai ban sani ba ko suna raye yanzu" Hajiya Batula ta kada kai "ALLAH yasa suna raye, idan har suna raye su ya kamata ka samu, ka fara kallon yanda suke da irin halinsu, idan kaga za a iya siyan su da kudi a shirye muke mu mallaka musu dukkan abunda muka mallaka, idan kuma kudin bai da daraja a gurinsu kamar dai shi Ahmad din sai ka sanar da su gaskiyar komai da halin da diyarmu take ciki, na san zasu tausaya mata" Yaji dadi har ya bayyana akan fuskarsa yace "wannan tabbas shine abun yi, insha ALLAHU zamu samu nasara ta nan" Sau uku ana sanar da shi ana zuwa nemansa da wani mutum a cikin hadaddiyar mota amman bai kawo komai a ransa ba. Yau yana zaune kan tabarmar kofar gidan da yake Juma'a ce ya dawo daga aiki da wuri daga masallacin Juma'a ya taho gida. Mota hadaddiya ta tsaya a kofar gidanshi daga can nesa direba ya bude da sauri ya zagaya ya budewa Alhaji Nura Kwangila. Daga inda Malam Sulaiman yake zaune yana hangen motar yana tunanin ko gurin wa tazo cikin layin, don bai taba ganin mota mai kyan irin wannan ba. Sai dai ga mamakinsa sai yaga kai tsaye gurinsa mutumin da aka budewa kofar motar yake nufowa, har ya iso inda yake yayi masa sallama. Malam Sulaiman ya mike da sauri yana amsa masa sallamar ya ba shi hannu suka gaisa. Alhaji Nura Kwangila yace "don ALLAH ko kai ne Malam Sulaiman mahaifin Ahmad? Cikin sauri yace "zahiri nine lafiya dai ko? Alhaji Nura Kwangila yayi murmushi yace "lafiya kalau sai alheri, mu zauna nayi maka bayani idan da hali" Suka koma suka zauna, bayan sun kara gaisawa Alhaji Nura Kwangila ya fara yi masa bayani abun dake tafe da shi tun daga farko har karshe, ya kare zancen nasa da roko kamar zai fashe da kuka. Malam Sulaiman yayi yake yace "wato yaran zamani basu da dama, ban da shiririta ko dumbin halaccin da aka yi masa ba zai kalla ba, kishin banza kuma na matarshi shi da ALLAH ya hore masa ikon auren mace hudu zai zauna yana wannan shirmen? Ka kwantar da hankalinka insha ALLAHU kamar anyi an gama wannan auren" Alhaji Nura Kwangila yaji dadin wannan maganar, wato bai nuna kudi ko wani abu don ya samu abun da yake so ba, lallai ya yarda ya samu surukai da mijin diya nagari Wanda ko bayan ranshi zasu rike dukiyar diyarshi da ita kanta da daraja don haka ya dinga godiya. Can Malam Sulaiman yayi shiru da damuwa a fuskarsa. Alhaji Nura Kwangila yace "lafiya dai ko Malam?" Malam Sulaiman ya gyara zama yace "eh to akwai wani hanzari ba dugu ba, ban sani ba ko idan kaji zaka yarda diyarka ta auri Ahmad, bana so sai abu yayi nisa irin abunda ya faru a neman aurensa na farko ya kuma faruwa, duk da ba shine ya nemi auren ba, a yanzu abunda zai biyo baya zai iya yi masa ciwo har ya fama masa mikin dake ranshi da ya jima da narkewa" Alhaji Nura Kwangila ya kalle shi da rashin fahimta, amman bai yi magana ba ganin kamar Malam Sulaiman din bai gama bayani ba. Malam yayi dan Jim, yanayinsa ya sauya zuwa damuwa gaba daya dakyar ya daure ya cigaba da magana "Kamar yadda aka fada maka nine mahaifin Ahmad haka ne, amma ba wanda ya kawo shi duniya ba" "Mahaifinsa rasuwa yayi kenan? Alhaji Nura Kwangila ya tambaya da sauri. Malam Sulaiman ya girgiza kai gami da fadin "ko daya har zuwa wannan lokaci ba a san waye mahaifin Ahmad ba" Alhaji Nura Kwangila ya waro ido cikin tashin hankali da fargaba yace "wai kana nufin shege ne bai da uba? Malam Sulaiman ya kada kai "ko daya! Har yanzu dai bamu sani ba Ahmad yana da uba ko bai da uba. Na gaya maka ne tun kan magana tayi nisa kuce an munafurceku. Shekarun baya wata mahaukaciya da take zaune akan bolar bayan gidana mai suna Asma'u ita ce ta haife shi" Malam Sulaiman ya kwashe labarin Ahmad kaf ya sanar da Alhaji Nura Kwangila tun lokacin da aka haifeshi har zuwa yau. Gumi ya soma karyowa Alhaji Nura Kwangila, shike nan murna ta koma ciki, amman sai ya kalli Malam Sulaiman yace "ko zaka iya rike shekarun da abun ya faru? Malam Sulaiman yace "gaskiya ban rike ba sai dai akwai takaddu da hoton matar na ainahi da aka dauka randa ta mutu, don danta ya amsa yaje an ciro fuskar mahaifiyar tasa yayi babban hoto dashi ya kafe a cikin dakinsa. Alhaji Nura Kwangila yace "ka dauko su, bai kamata a zauna tsawon shekaru haka ba a yi cigiya ba. Sannan kuma ni jikina yana gaya min wani abu, amma don ALLAH yi gaggawa ka dauko mini hoton" Da sauri Malam Sulaiman ya mike ya shige cikin gida, Alhaji Nura Kwangila ya kasa zama ya mike yana kaiwa da komowa da damuwa cikin ranshi yana ta addu'a. Can sai ga Malam Sulaiman ya fito bayan dogon lokacin da ya dauka cikin gidan to rike da wata tsohuwar bakar leda ya miko masa. "Wannan shine dukkan bayanansa har hoton mahaifiyarsa yana ciki" Da sauri Alhaji Nura Kwangila ya karbi ledar ya kwance, hoton yake fatan ya gani. Ya dauko shi da sauri ya kura masa ido, sai ya fasa salati da kabbara yana fadin "ANTI ASMA'U dama kece mahaifiyar Ahmad? Tabbas Ahmad dana ne WALLAHI dan yayana ne. Wannan matar yayana ce da ta sami tabin hankali shekaru kusan talatin da biyu baya" Malam Sulaiman ya cika da mamaki har ya kasa cewa komai, ya tsaya yana sauraron sambatun Alhaji Nura Kwangila. Can yace "bari na sanar da cikin gida, ciki zaka shigo sai mu yi maganar a nutse don na ga har yara sun fara taruwa" ya juya ya shige cikin gida. Mintuna kadan sai gashi nan ya dawo ya dauki tabarmar da butarsa yana fadin "biyo ni nan Alhaji" A cikin gidan ma Umma mamaki abun ya dinga bata. Aka ce a kirawo Ahmad din a waya. Ana kiransa ya dauka hade da yin sallama. Malam Sulaiman yace masa yazo yana son ganinshi amma ya tabbatar ya biya ya taho da iyalinsa baki daya yanzu" Hankalin Ahmad ya dan tashi amman da Malam Sulaiman yace masa kada ya damu alkhairi ne ya sanya hankalinshi ya kwanta, lokacin daman yana kan hanyar zuwa gida, don haka yana isa ya sanarwa da Ma'u sakon Malam. Ita ma ta tsorata amman ya tabbatar mata babu komai kada ta damu. Yaran su daman suna shirye cikin kwalliyar Juma'a don haka aka dunguma aka wuce gidan nasu. DA ME AKE ADO? Aunty Fauziyya D Sulaiman (Matar Bello Q for Q) Typing Dan Almajiri Whatsapp number 08163840712 Alherin ALLAH ya kai miki Fauzanmu. Malam Sulaiman da Alhaji Nura Kwangila suna zaunne suna tattaunawa Ahmad da Ma'u da yara suka shigo suna sallama. Mamaki da tsoro ya dan kama Ahmad ganin Alhaji Nura Kwangila zaune a tsakiyar gidansu, amman dai ya dake ya karaso ciki. Alhaji Nura Kwangila ya kura masa ido yana kallo, sai yake gani kamar yayansa yake kallo. Ya jima yana jin Ahmad da kaunarsa ashe jininsa ne. Duk sanda ya ga Ahmad sai ya dinga jin kamar ya san shi ashe jinin dan uwansa yake kallo. Suka karaso suna gaida su, abun da ya dan fadar musu da gaba bai wuce kallo su da suka ga kowa yana yi ba. Ita dai ma'u bata san ko waye Alhaji Nura Kwangila ba, shi ya sanya damuwarta bata da yawa. Suka zauna bayan an gaisa Malam Sulaiman ne ya fara yin magana "Ahmad ka san wannan?" Ya nuna Alhaji Nura Kwangila. Da sauri Ahmad yace "na san shi maigidana ne Alhaji Nura Kwangila" "Daga yau kada ka kara kallonsa a mai gida sai uba kuma mahaifi" Malam Sulaiman ya bashi amsa. Abunda ya fara fadar da gaban Ahmad da Ma'u kenan suka kalli juna da mamaki. Malam Sulaiman ya cigaba da magana. "Ya zo da wata bukata sai kuma bukatar ta sauya zuwa wani abu daban. A yau mun gano Alhaji Nura Kwangila kanin mahaifinka ne da ya haife ka uwa daya