← Book details Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 40

Sashe 5

Da Me Ake Ado 3 & 4 Complete Hausa Novel · about 1 min read

wannan iskanci ne, turawa ne suke yi a cikin fim, kuma umma da baba ma idan ana yi ko a talabijin kashewa suke yi, haka ma a gidan yaya auwal idan ana yi fada yake yi, kai me ya sanya kayi min yaya? Ya dafe kai da damuwa, wai wacce irin yarinya ce ma'u, ga ta haihuwar birni kuma 'yar makaranta wadda ya kamata ace ta san komai amma babu abinda ta sani. Ya gyara murya yana shirin sake lallaba ta, amma tuni ta fice daga cikin dakin tana ci gana da kuka. Ya bita DA kallo ya ma rasa me zai yi. Washe gari da sassafe ya shirya ya fice gurin aikinsa ya bar mata rubutu a takarda ganin bata tashi daga bacci ba. Yau basu kwana daki daya ba ma shi can falo ya kwana don ganin duk ya firgita da shi yau, zuciyarshi fal da tunani ya fice.
Chapter 5 · 0% Book details